page86to90&91to95

416 17 1
                                    

[1/3, 7:24 AM] Obama: 💔💔💔❣❣❣💔💔💔❣❣❣





*SANADIN HOTO*






*TARE DA ALQALAMIN HASSANA D'AN LARABAWA*✍✍✍






*page 86 to 90*






*DEDICATED TO*

*FAUZIYYA SANI JIBRIL*😍😍sharhinki yana burgeni aunty Fauziyya ,INA matuqar ji dake a raina, Allah ya raya iyali yabar zumunci🤝🤝🤝

*GAREKU FAN'S*

*Ku dinga haquri zuwa lokacin da marubuciya zata kammala rubutun ta ,qorafi ba naku bane ,duk Wanda yafara karanta SANADIN HOTO daga farko zuwa inda na tsaya ko ban kai qarshe ba zai fahimci inda na dosa ,masu cewa INA sasu kuka da zubarda hawaye suyi haquri labarin ne yazo a haka ,nima wani zubin idan INA typing nakanyi hawayen,INA godiya ga wad'anda suka fahimci labarina har suke ganin matuqar qoqarina duk da nid'in sabuwar marubuciya CE ,masu ganin banyiwa Abbas adalci ba su Sani cewa ba komai kakeso kake samuba ,kuma ba komai ke zame maka alkairi ba ,zakaso Abu kamar ka mutu amma yazamo sharri a gareka ,idan kayi haquri ka miqawa Allah lamarinka ka karb'i qaddarar ka sai kaga kasamu rabo agurin Allah ,labarina yana tafiya da abunda yake faruwa a rayuwar mu ,sannan labarina yana d'auke da salon da ya sha bam bam da sauran litattafai,Dan haka masu qorafi kuyi haquri kucigaba da karatu ,idan yanzu bakuji dad'iba qila a gaba kuji ,duk da ba munayin rubutu Dan aji dad'i ayi nishad'i kawai ba ,akwai jigo wato fad'akarwa ,ilimantarwa ,da tunasarwa,ngd fan's INA ji daku tamkar yadda kuke sona da rubutu na Allah yabar zumuncin mu*❤❤❤





,,,,,,,,,,,,,Haka taron ya tashi ba tare da kammalawa ba ,nidai ranar babu Wanda ma ya dosheni da sunan lallashi ,anbarni nayi kukana na more ,qawaye na sukayi jugum jugum ,wasu na tayani kukan,,a zuciya ta fad'i nake Abba sai dai kayi haquri ,alqawarin da nayi maka akan indena kuka ba zai yiwuba ,ya Abbas yakuma dawomin da miki sabo ,,,,,,,,!!




,,,,,,,,Washe gari asabar za'ayi dinner ,kowa ka gani gurin dinner d'in yad'au wanka samari da y'ammata kamar ba za'a mutuba saboda d'aukar gayu .


Qawaye na sunyi anko cikin material blue me adon pink ,sai head pink takalmi da jaka da sarqa duk kalar kayansu sunyi matuqar kyau ,,,,,,,!!


Abokan ango ma sunyi shigar blue d'in shadda anyi aiki da pink d'in zare sai hula pink ,suma nabarku Ku hangi kyawun da sukayi ,,,,,,,!!


"Nida kamal kuwa shigar coffee da milk mukayi ,kyawu naban mamaki mukayi ,duk da zuciya ta ba dad'i nayi qoqarin sakin fuskata ,,INA ta yaqe musamman da muke wajan zaman mu mutane NATA zuwa gaishemu da bamu kyaututtuka ,hotu na kuwa da aka dinga d'aukarmu kamar inyi ihu nakeji ,ba'abinda na tsana a rayuwata irin hoto yanzu ko ganin camera banason yi ,,,,,,,!!



Idona yayi qwal qwal zanyi kuka ,sai mutsu mutsu nakeyi INA hararar masu hoto ,kamal ne ya lura dani hankalinsa gaba d'aya yadawo gareni ,ya matso jikina yana kallona bakinsa saitin kunnena kamar me rad'a yace min"menene uhuummm ,me kikeso gayamin,karkiyi kuka zaki b'ata kwalliyarki ,"

Na d'ago kaina na juyo INA kallonsa ,fuskata dab da tasa kamar mu had'e ,d'aga idanuwa da nayi in kalleshi shiyabawa hawayen idona damar zubowa nace cikin shagwab'a irin wadda nakewa ya Abbas "kace su daina ,banaso sunayi "


Kamal ya rud'e da ganin shagwab'ata ,jikinsa ya kama rawa ,abinda baisaba ganiba ,jamila bata iya shagwab'a ba ita in banda masifa babu abinda ta iya ,hannunsa na rawa ya kama kafad'ata ya riqe cikin rawar baki yace "menene ba kyaso ??su waye ??me sukeyi ??fad'amin kinji baby na !!.


"Wani haushinsa ya kamani !wai baby !!ga haushin hoto ,ga kuma wani haushin ya qaramin ,,,,,!!

Na zunb'uro baki naqara shagwab'ewa nace " hoto mana!nidai banaso !kace su dena !ka koresu anan banaso kaji !!ni gaula ban San cewa shagwab'ar da nakeyi qara afkashi cikin shauqi nakeyi ba,,,,,,,!!



SANADIN HOTOWhere stories live. Discover now