page131to135&136to140

578 21 0
                                    

[1/3, 7:24 AM] Obama: 💔💔💔❣❣❣💔💔💔❣❣❣







*SANADIN HOTO*






*TARE DA ALK'ALAMIN HASSANA D'AN LARABAWA*✍✍✍






*page 131 to 135*








*TEAM KAMAL*🤞🤞

Zee musty
Maman khairat
Minono
Anayya
Maryam Hassan
Ramlat Abra
Ummin Khadija
Aeesha yusra
Maman Jidda
Momyn khady
Saudat
Zee gurbi

*KAMAL NA MIK'O GAISUWARSA GAREKU SABODA K'AUNAR DA KUKE MASA*🥰🥰🥰😍😍😍😘😘😘.




*TEAM YA ABBAS*🤞🤞

Maman sadiq
Maman twins
Sadiya datti wudulawa
Zainab yawale
Maman hanan
Surayya
Maryam alqali
Ruky bilyamin
Hafeeza ningi
Ummu na'im
Miss husna
Shatu

*YA ABBAS YANA GAISHEKU SABODA SON DA KUKE MASA*😍😍😍😘😘😘🥰🥰🥰.



*SADAUKARWA GA DUK ME BIBIYAR SANADIN HOTO TUN DAGA FARKO HAR ZUWA YAU ,DAFATAN ZAKU CIGABA DA BINA ZUWA K'ARSHEN LABARIN*





,,,,,,,,,,,,,,Hafsat ta d'ago kai ta kalli Abba ta amsa ,sannan takuma duk'ar da kanta k'asa .

"Abba yace "hafsat na kiraki ne domin in tambayeki ,shin kin fitar da mijin aure ne ?

"Gaban hafsat ya fad'i tayi shiru batace komaiba ,saida Abba yak'ara mai maita tambayar sannan tayi magana a hankali tace.

" ah ah Abba "tunda jabeer ya rasu har yanzu nakasa tsayarda wani shiyasa ,saboda duk yawanci mazan yanzu ba don Allah suke zuwaba ,saidon wata buk'ata tasu ,(jabeer shine saurayin da sukayi soyayya da hafsat ,shitaso ta tsaida amatsayin mijin aure ,saiyayi ciwon cikin dare d'aya ya rasu ,shine har yanzu hafsat bata tsayawa da samari ,saboda kewar jabeer ).

"Abba yayi murmushi yace " to d'iyata tunda har yanzu baki tsaidaba ,ni nasamo miki miji d'aya tamkar da dubu ,me hankali ,me kamala ,me biyayya ,me kyautatawa ,Wanda idan kika aureshi kin dace duniya da lahira insha Allah ,ya kika gani ?kin yarda da zab'ina ko kuwa ?


"Wani tashin hankali da bata tab'a riska ba ya sameta ,ta jik'e da gumi sharkaf tamkar ba fanka d'akin ,idanuwanta suka Tara hawaye ,cikin rawar murya hafsat tafara magana .


"Abba Aini d'iyarkace ,me Neman albarka agareka ,kuma daman a matsayina na budurwa kune a hak'k'u Ku zab'amin abokin rayuwa ,tunda ina k'ark'ashin ikon kune Abba ,jabeer ne zab'ina kuma narasashi daman ,banida wani zab'i yanzu Abba ,duk Wanda kukabani zanyi biyayya Abba ,magana take amma hawaye na kwarara a idanunta ".

"Abba yaji dad'in maganar hafsat matuk'a yanajin dad'in yadda yaransu sukeda tarbiyya da biyayya ,murmushi bai bar fuskarsa ba yace " naji dad'in  maganarki y'ata ,Allah yayi miki albarka ,sai dai naji kinyi saurin amincewa ,amma baki tambayi wanene mijin ba ?.

"Hafsat t ayi wani murmushi tasa hannu ta share hawayenta sannan ta girgiza kanta tace "Abba ai ba sai nasaniba ,kowaye kuka bani zan aura ,ko yaro ko tsoho ,ko me lafiya ko nakasasshe Abba ,wallahi zanyi maraba dashi Abba, domin inyi muku biyayya ,tunda banida tamkarku a rayuwata ".


Abba yace " hafsat Wanda zamu baki zakiyi alfaharin kasancewarki mata agareshi ,domin yayi tako'ina ,bashida nakasa ko wani aibu atare dashi ,sai tarin kyawawan halaye nagartattu ,da ilimi da wadata ,da kyau da kyautatawa ,wad'annan kad'an ne daga cikin halayensa ,kuma yanada kyau kisan ko wanene !bawani bane face" Abbas" .


SANADIN HOTOWhere stories live. Discover now