page 46 to 50 & 51 to 55

633 30 5
                                    

[1/3, 7:24 AM] Obama: 💔💔💔❣❣❣💔💔💔❣❣❣


*SANADIN HOTO*


*TARE DA ALQALAMIN HASSANA D'AN LARABAWA*✍✍✍

*page 46 to 50*


"Ringin d'in wayar ta ne ya tayar da ita daga baccin da takeyi ,a tsorace ta dubi wayar tana tunanin wake kiranta a dai dai wannan lokacin ,ta d'aga kai tadubi agogon d'akin qarfe biyu harda minti ashirin da bakwai NA dare ,ta juya ta kalli safah da ke gefenta da tunanin zata ganta tana bacci ,saita ganta zaune dangwargwar akan gadon da alamun baccin ya gagari idonta kanta Asama ta fad'a zuzzurfan tunani ,mama ta qara juyawa ta dubi wayarta saitaga baquwar Numba CE ake kiranta da 'ita ,har wayar tagama ringin ta katse bata d'agaba ,saida ta katse aka kuma kira sannan ta miqa hannu ta d'aga cikin far gaba tace ,,,,

" Assalamu alaikum "",

" daga can mamy dake kuwa ta amsa sallamar mama ,sannan ta cigaba da magana cikin rawar murya "Maman sameer nice mamyn Abbas "

Mamyn Abbas kuma ?? ,, Abinda mama tace kenan cikin mamaki da tsoro sannan tacire wayar daga kunnenta ta dubi number da aka kirata d'in .

Safah cikin tunani take ,amma jin mama ta ambaci sunan Abbas a maganarta batasan lokacin da ta hantsilo gaban mama ba tana zare idanu ........,,,

Mayar da wayar kunnenta tayi ,sannan tace "mamyn Abbas lfy kuwa naji muryarki haka ??gashi kin kirani a irin wannan lokacin dare ya tsala ,Allah yasa dai lafiya kuke ,INA Abbas d'in yake ??.

Cikin kuka mamy tace " muna asibiti Abbas bashida lafiya ,sai aman jini yakeyi ,doctor yace jininsa ya hau kuma zuciyarsa tana shirin kamuwa da ciwo koma ta buga ,gashi baya cikin hayyacinsa amma sai kiran safah yakeyi ,doctor kuma yace akawo safah asibiti kafin qarfe sha biyu na ranar gobe ,anmasa allurar bacci anaso ya farka yafa cin karo da ita ,Dan girman Allah Maman sameer kitemakeni safah tazo da safe wallahi rayuwar Abbas na cikin garari ,bakiga yadda yadawo ba ,kinsani shi kad'ai ke gareni banason in rasashi ,kiyiwa Allah ki roqi Abba yabari safah tazo Dan ta ceci rayuwar musulmi ,,,ta qarasa da fashewa da kuka .......




Duk maganar da mamy keyi safah najin komai domin a hands free mama tasaka wayar ,kan kace me safah har tafara kuka ,qirjinta ya quntata numfashinta nakai kawo ,ta tabbatar itama da za'a auna jininta qila yafi na ya Abbas hawa ,ta tabbatar itama zuciyarta na gab da bugawa ,daman haka zafin rabuwa da masoyi yake ??masoyin da bata tab'a tunanin akwai qaddarar da zatazo ta shata layi tsakaninta dashiba ,masoyi na haqiqa Wanda yake sonta fiye da kansa ,so Mara algus !!!ba'abinda takeso dagani irin ya Abbas a halin yanzu !!!wallahi da zata ganshi har rungumarsa saitayi saboda tsananin shauqin sonsa daya
qaru a zuciyarta Kodak kuwa agaban ABBA NE 😳😳sai dai ABBA YA GIDIDDIBATA ,,,,,,,.

Idanun mama na kan safah tana girgiza mata kai alamun tabar kuka ,tafara magana cikin muryar tausayawa .....

"Hasbunallahu waniimal wakil "" yanzu abin harya kai Abbas ga asibiti ??Allah sarki Abbas Allah yabashi lafiya ,karki damu hajiya insha Allahu zan kawomiki safah da kaina asibiti da safe ,nasan dai Abban su bazai bariba amma zan San yadda zan b'ullomasa ,kiyi haquri kidena kuka zaisamu sauqi da yardar Allah ,ai cuta ba mutuwa bace ,,,wannan tashin hankali dai Allah yakawo mana qarshensa ,wallahi ba irin fafatawar da bamuyi da Abban akan zancen ba amma ya kafe yaqi saurarata ,har barazanar SAKI yayimin akan maganar nan ,amma karki damu inyafi qarfinmu ai baifi qarfin ALLAH ba ,zamu qara kai kukanmu zuwa gareshi ,insha Allah zai amsa mana ""!!!!!!!!!.........



SAKI kuma ??abinda mamy tace kenan cikin tsananin far gaba da rud'u ,lallai wannan Abban jidalin sa yayi yawa ,nan da nan taqara sarewa da lamarin har taji zuciyarta tafara tsanar Abban bisa kafiyarsa da qin tausaya yara masu raunin zuciya .......

SANADIN HOTOWhere stories live. Discover now