[11/13, 6:10 PM] Hassana D'an Larabawa🥰: 💔💔💔❣❣❣💔💔💔❣❣❣
*SANADIN HOTO*
*TAREDA ALKALAMIN HASSANA DANLARABAWA*✍✍✍
*page 1*
Bismillahirrahmanirrahim
Zaune nake akan katuwar dadduma nida ya abbas ,a farfajiyar gidammu karatu yake koyamin ,littafin math ne agabana gaba daya kaina adaure yake saboda ba fahimta nake ba .kowa yasan yarda math bashida farin jini agun mutane da dama, tonima hakan take aguna, yayinda ya abbas yadage akan saina koya shiyasa yakemin bitarsa agida idan munsamu tym, munyi zaman kusan minti 30 amma bangane ba har yagaji yadago dara daran idanunsa masu matukar kyau da daukar hankali yadubeni ,"yace My safah cikin kayatacciyar muryarsa Me dadin sauraro ,nadago kaina na kallesa kallon danaga yanaminne yasani saurin sunkuyarda kaina ban shiryaba, yatsun hannuna naji yakama yamatsamun su nankuwa naji danzafi hakan yasa nadanyi kara tareda shagwabe fuskata nadubeshi nace" ya abbas akwai zafifa shan kunu yayi yace aidama sonake kiji zafin tundazu muke abu daya kinki maida hankali kigane sai wahala muke menene hakane My safah,? nace to aini banason math dinne dama ka kyaleni, pls ,Cikin xaro ido 😳yace" impossible antaba kyale karatu damn? Malama inzaki maida hankali kikoya tom inbahakaba kuma Allah zamu bata dake zandena zama dake ina siya miki Sweet da ice cream ""ai safah najin haka tuni ido yai kwalkwal hawaye yazuraro akan kyakkyawar Baby face nata cikin shagwaba nace "sorry ya abbas dina nadena ,ganin hawayen fuskarta nandanan sai jikinsa yai sanyi aduniyar nan ba abinda ya tsana irin bacin ran safah dinsa, hannu yakai yagoge mata hawayen yace" yawuce amma kimaida hnkl kan karatu shine gatanki agaba inason ganin nangaba kinzama wata babbar Mace me kima kinji my safah .cikin murna na jinjina kaina nace insha Allah zanyi karatu yayana harsaikace ya isa haka "yayi min wani sumammen murmushi har kyawawan hakransa suka bayyana yace good girl ina alfahari dake "yafada yaname jamin haba ta sannan yamike yanacewa bari inje gida mami na jirana zata aikeni gun aunty safiyya, nace lah" inkaje kagaidamin my teema kace tatawomin da abunnan school gobe yace wane abune? Nace ""um um sirri ne yamin wani kallo yace sirriko?aishikenan tunda bazaa gayaminba ngd my safah ,nayi murmushi nace zangayama amma ba yauba kaji nafada ina kallonsa, ya jinjina kai yana fadin shikenan intayi tsami naji ainasan baabinda kike boyemin bari naje nace ok" kagaidamin mami kafin nashigo yace tom haryajuya yafara tafiya nace ya abbas yajuyo asukwane nace," bakagayamin kalmar karsheba zaka tafi koka mantane?. Kuramin ido yayi yanamin kallon sama da kasa cikin kasalalliyar murya yacemin" kalmar tanamiki dadine? Cikin kunya na sunkui dakai ina murmushi nace yes yayi murmushi, harnajiyo sautinsa yace *ilove you my safah* wani masifaffen dadi yakamani, cikin farinciki nadago kaina na kalleshi na juya idanuna nace "*mee to ya abbas*najuya nashige gida "da guduna .......🏃🏻♀🏃🏻♀🏃🏻♀
*hassana danlarabawa*✍✍✍
[11/13, 6:10 PM] Hassana D'an Larabawa🥰: 💔💔💔❣❣❣💔💔💔❣❣❣*SANADIN HOTO*
*TAREDA ALKALAMIN HASSANA DANLARABAWA*✍✍✍
*page 2*
Maman mu na tsaye a tsakar gidanmu tanabawa zainabu me aikinmu umarnin tabude fridge ta dauko kaji ta gyara nafado gidan aguje ina haki tajuyo afirgice tanaceawa lfy safah?nadubeta nace bakomai mama nida ya abbas ne tayi tsaki tace kudai shirmenku baya karewa kuna girma kunacin kasa to yanzu kunyi karatun kokuwa? Munyi mamanmu nafada ina duban zainabu nace Baba Zainabu yau mezaki dafamana ne? Tayi murmushi tace diyar abbanta farfesu zammiki yau nadaka tsalle inacewa lallai zamuci dadi yau pls baba zainabu nida abbana kawai zakiwa sai ya abbas kosu sameer karkisa dasu kinji kanna rufe baki mama ta katseni dacewa to 'yar gidan abba da abbas dayake su su sameer din sukika raina ko? To sai ansa dasu din nasuma saiyafi naki yawa me bakin kwadayi kawai nakwabe fuska zanyi abinda nasaba wato shagwaba nanda nan baba zainabu tajawoni jikinta tana fadin rabuda ita diyar abba zanmiki me dadi amma kibari a sanwa su sameer suma kadan ko? Na jinjina Kai nace to baba mamanmu tayi murmushi tace ku kuka sani dai aranta kuwa dadin yadda baba zainabu take sona take nace bari inje in ajiye daddumar da Books dina mamanmu har yanzu aunty hameeda bata tashi bane?eh bata tashiba amma duba dakinku kigani kitasheta ma laasar tayi kuyi sallah banason baccin yamma domin yanasa ciwon kai me tsanani nace toh mamanmu nayi gaba ina fadin baba zainabu bari inyi sallah inzo intayaki aikin a kitchen kinji tace to yarinyar kirki saikin Fito.
❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤
Ya dade atsaye yana kallon kofar kamar ba gobe dadi na dibarsa kamar me kyawawan idanunsa suncika da kwallar farin ciki besan sanda yadaga hannunsa yadubi gabas ba yace "Allah kaine Allah ina rokonka kacikamin burina kabani safah amatsayin matar aurena" Allah kasa tazama alkairi agareni ya rabby "ya shafa yana me goge hawayen sa shidai yasan yana son safah, so me tsanani yana jinta fiye da tunanin me tunani yanasonta fiye da kansa, kullum yana wayar gari da sabon sonta a ransa yatashi da sonta ne amma bazai iya fadar takamaimai sanda yafara sontaba "a baya yayi tunanin zumunci da amincin dake tsakanin iyayen sune yajanyo domin mahaifin abbas kan yarasu aminin mahaifin safah ne ",sai yanzu yagane sone daga Allah, kaunace daga indallahi ,bazai misalta yadda yake jinta aransa ba "yasauke ajiyar zuciya yadawo daga tunanin dayatafi na sakan kuna badan yasoba haka yakada kai yafice ya nufi gidansu dake bayan gidan su safah, dan basuda nisa.
Safah nashiga dakinsu taji karar ruwa a toilet ,alamun aunty hameeda na ciki ta ajiye daddumar da littattafanta tacire hijabinta, yayi dai dai da fitowar hameeda ragowar ruwan hannunta ta yarfawa safah tana fadinľ kungama karatun ko soyayyar kukayi ,😉"na kyalkyale da dariya ina fadin" kai aunty soyayya kuma? Tace eh aiko makaho dabaya gani inya ganku yasan soyayya kuke ,kallonda Abbas kadai yake miki abin tambayane inyasaki gaba kamar ya hadiyeki fa,gashi baisan bacin ranki ko kadan tunkuna yara balle yanxu dakuka girma kuka kusa isa aure" nazaro ido aure kuma aunty? 😳kema baaimiki aure ba ballemu yara ,aunty ta tuntsure da dariya, kune yaran? Ah ah motsin gado ne ku karewar yarinta 😆.
Karki mantafa shekararki 15 ko yanxu aka kaiki dakin miji zama daram zakiyi ,balle abbas dayake da shekara 25" nace um um aunty ba yanxuba sainaga karshen biro da takarda, haiiiiiiiii casssss "aunty tafada tana dariya Tace "kizama mangwafak ma safah karewar karatu kenan ni kauce inyi sallah muntsaya surutu tym zaiwuce" safah tayi dariya tareda bude kofar toilet tayi addua kafin tashiga
*(allahumma inni auzu bika minal kubsi wal kabaisi waminash shaidanirrajim)*
Sannan tashiga da kafar hagu ,bayan tayi kyakkyawan tsarki da alwala tafito da kafar dama tareda fadar"
*(gufranaka allahumma azhaba annal aza waafani)*.Fitowarta yayi daidai da hameeda ta kammala sallar laasar, batadubi auntyn tataba ta shimfida abun sallah ta tada sallarta bayan ta idar tadade tana addu'a sannan tamiqe tacire hijaab ta ninke ta ninke daddumar ma ,sannan tajuyo tadubi hameeda dake gyaran kaya a sib tace" aunty ni nayi kitchen zantaya Baba zainabu aiki hameeda tace to kanwata ayi mana medadi nasanki fannin girki ba dama ceke "tafada tana murmushi dadi yakama safah dan kuwa ita mutumce meson ayaba mata, insha Allah aunty sai kunnenki yayi motsi dan dadi tafada tana me ficewa daga dakin tanufi kitchen din.
Hameeda ta girgiza kai" tanajin kanwarta aranta sosai ko cikin kannenta safah ta davan ce. 😘🥰*hassana danlarabawa*✍✍✍
CZYTASZ
SANADIN HOTO
Historycznelabari ne da aka ginashi akan tsabtatacciyar soyayya ,wadda tafara tun daga yarinta ,dab da burin masoyan zai cika k'addara ta afka musu dalilin sanadin hoto ,kubiyoni Dan sanin shin k'addarar tana kaisu ga auren juna ko kuwa ........!?