[11/13/2019, 6:10 PM] Hassana D'an Larabawa🥰: 💔💔💔❣❣❣💔💔💔❣❣❣
*SANADIN HOTO*
*TAREDA ALKALAMIN HASSANA DANLARABAWA*✍✍✍
*page 16 to 20*
Hoto ne Abba "yafada murya na kyarma, bayan yadawo daga gigitar marin da yasha, dan tabbas ya maru iya maruwa, kankace me har kumatunsa ya dan kumbura.
Abba yace a harzuqe "eh naga hoto ne, abinda nakeson sani shine dagaske abinda idona yake gani gaskiya ne!!!!! """?da gaske safa nake gani a cikin hotonnan!!!! ""???da gaske amanata yaronnan yaci!!!! "???da gaske ne abubuwannan kokuma mafarki nake!!!! """????amsamin nace ""yaqara dakawa uncle muguwar tsawa!!!! "".......
"itace Abba, amma wallah........!!!!!!!! Kan ya qarasa Abba yadaga masa hannu........ Jeka Kai sallah, "kar kuma kayiwa wani magana tsakanin safah da Abbas din, Kai ban yarda kayi maganar nan da kowa bama, tunda har ka tabbatar min itace a hotonnan rungume jikin wani namiji wanda ba mijinta ba, lallai safah taban mamaki, kuma nima zan shayar da ita mamaki fiye da wanda ta shayar dani!!!!!!! """"
Yana fadin haka yasa Kai ya fice daga dakin, cikin sauri kamar ya kifa.
Uncle Zubewa yayi akan katifa cikin dukan zuciya, hawaye na kwaranyo masa, tausayin Friend dinsa da safa na nuqurqusar zuciyarsa, tabbas yasan yayansa yanada masifar zafi matuqa in aka taboshi, amma baitaba ganin yayi fushi irin hakaba a tsawon rayuwarsa, wannan wane irin bala 'ine ya tunkarosu haka!!!!.......
Ya dade cikin wannan yanayi da debe qauna, kafin yamiqe yashige toilet yadaura alwala, ya fito, anan dakinsa yayi sallarsa tunda masallaci duk Sun idar, yadade zaune cikin hawaye yana adduar Allah ya taqaita wannan abu, duk abinda zaifaru da safa da Abbas Allah ya taqaita musu yabasu wuyan dauka.....!!!!!!!!!!.Abba dakinsa yashige ya kulle kansa, bakin ciki nacin zuciyarsa, shekara da shekaru yana qoqarin bawa 'yarsa tarbiyya, amma tashi daya wani yanason ruguza masa!!!!!!!! Wace irin masifa ce wannan!!!!!!! Wane irin zamani ne wannan!!!!!! Idan akace masa ko a mafarki safah zata aikata Haka to tabbas idan yatashi daga wannan mafarki saiyayi sadaka!!!!!!!!!! Yarinya simi simi da ita, shi kansa Abbas din kallon kamilin yaro yake masa, baitaba tunanin haka daga gareshiba, ashe lumbu lumbu ne wutar qaiqayi!!!!!!!!! Tsabar tsaurin ido ya daukar masa 'ya yaje ya qwaqumeta ya tattabeta ayi musu hoto!!!!!???? Bada saninsa ba!!!!!! Bada yardarsaba!!!!!!! Tashin hankalinsa daya Allah dai yasa bawani abu daya shiga tsakaninsu, gabansa yayi matuqar faduwa yakuma kallon hoton dake hannunsa, wanda suke kallon junansu kallo irinna soyayya, Abba yaji fargaba takuma rufeshi,!!!!!!! Wannan kallon dasukewa juna kamar na mata da miji acikin hoto kenan!!!!! To inaga Sun kebe??????wayasan abinda suke aikatawa???? """""""ya ubangiji ka taqaitamin jin kunya kar yarinyar nan ta zubar Min da mutunci """.
Mun shigo kwanar gidanmu kenan, mukaga adaidaita sahu ta ajiye mama qofar gida, hannuna riqe da na ikram muka qarasa gunta, harta sallami me mota ya juya, mama ta juyo ta dubemu tana "yanxu kuka dawo kenan, munyi dai dai "nace ""sannu da zuwa Maman mu, ya jikin saleem din ""nafada ina daukan saleem, Allah sarki yaron harya rame wallahi, mama tace da sauki muntsaya Sun sa masa drip ne saboda aman da yayi!!!!!! Ya jikin ameera????? Na kwantar da saleem a kafadata mukayi cikin gida ina cewa ""da sauki itama, sai dai fa taji jiki duk ta yanqwane itama,!!!!!! Mama tace ""haka aketa fama wallah, ke kinga asibiti a cike yake anata kawo mutane, Allah dai yabamu wucewa lafiya """!!!!!!!!!!!
Dai dai lokacin muka shiga barandar gidan mu, saimukaga motar Abba, ikram tace "lah mama Abba yadawo "na kalli motar a raina inacewa Allah yasoni tareda mama zamu shiga, nasan idanni kadaice sainasha fada, haka zece yawo natafi!!!!!!!mama ce tace ""eh kin manta yau Sunday ikram aida wuri yake dawowa, yanxu kinga karfe uku tayi kiyi sauri mushiga kici abinci kisa uniform kitafi islamiyya, yau Kim makara!!!!! Da gudu ikram tayi gaba tanacewa to mama!!!! (ni daman munyi sauka a islamiyya, yanxu hadda mukeyi, kuma a sati so uku muke zuwa, litinin, talata, laraba,).
YOU ARE READING
SANADIN HOTO
Historical Fictionlabari ne da aka ginashi akan tsabtatacciyar soyayya ,wadda tafara tun daga yarinta ,dab da burin masoyan zai cika k'addara ta afka musu dalilin sanadin hoto ,kubiyoni Dan sanin shin k'addarar tana kaisu ga auren juna ko kuwa ........!?