page 36 to 40 & 41 to 45

521 22 0
                                    

[1/3, 7:24 AM] Obama: 💔💔💔❣❣❣💔💔💔❣❣❣.    

*SANADIN HOTO*  

*TARE DA ALQALAMIN HASSANA D'AN LARABAWA*✍✍✍.  

Page 41 to 45

                                                      

....A tun sanda kawu Sani yagama korawa mamy da ya Abbas yadda sukayi da Abba   qirjin mamy ke dukan Tara Tara ,kallon inda ya Abbas yake tayi inda yake zaune a qasa kan carpet d'in d'akin ,yayinda itada kawu Sani suke kan kujera zaune ,tunda kawu Sani yafara magana har yagama ya Abbas bai motsaba kansa na sunkuye ,mamy CE takula da cewa kamar  baya motsima ,hakan yasa takira sunanasa tace " Abbas " ,amma taji shiru bai amsaba ,asanyaye ta tashi tanufi inda yake ta durqusa gabansa tad'ago kansa tana kiran sunansa "my son" sai gani tayi yayi talau yafad'o jikinta alamun a sume yake ,arud'e ta d'ago fuskarsa tana kallo saitaga jini na fitowa ta bakinsa amma kuma ko motsi bayayi ,wani mugun tashin hankali ne ya kamata atake tahau girgizashi tana kiran sunansa cikin kuka ,amma INA baima San tanayi ba duk inda tajuyashi Binta yakeyi ,kawu Sani ne yataso a rud'e shima yana tambayarta meya faru ,sai ganin Abbas yayi kwance jikinta ba alamun numfashi taredashi ,ga jini har ya b'ata gaban rigarsa .                             "innalillahi wainna ilaihirrajiun""!!!!!!!!!             " Abinda kawu ya furta kenan ,yaci gaba da cewa "hajiya a man jini yakefa ,kuma baya numfashi ,tashi ki d'auko mayafi asibiti zamu kaishi karwani Abu yafaru dashi "" ya sunkuya ya d'auki ya Abbas a hannu kamar wani baby ,daman ya Abbas dayake siriri gashi wannan lamarin yaqara ramar dashi yazama fiyat dashi .      "da gudu kawu yayi waje dashi ,mamy tashige d'aki ta rarumo hijab tasaka tabisu da sauri sai faman kuka take ,bayan mota tashige ta zauna kawu Sani ya shimfid'e mata Abbas akan cinyarta shikuma yashige gaban motar yatada ita yafigeta aguje suka fita yad'auki hanyar asibiti..............".          

******************* 

""Ganin yadda safah ta sandare a tsaye yasa mama isa inda take ,takamota ta rungumeta a jikinta ko taji sanyi sanyi ,sannan tad'agota tana kallonta ,safah sai wuri wuri take da ido alamun bata cikin hayyacinta ,mama ta girgizata tana cewa "" ke safah kiyi magana mana ,wani lokacinma yin magana inkayi sanyi kakeji a zuciya ,ko kukanne kiyi zakiji sanyi a zuciyarki kinji "" safah tabi mama da ido galala tana kallonta ,ba alamun yin magana banda zare ido da kalle kalle ba abinda takeyi ,hankalin mama ya tashi tajuyo a fusace ta kalli Abba dake zaune kan kujera tace "haba ABBANSU "kana ganin halinda yarinyar nan ke ciki kayi banza damu !! So kake ta hauka cene ?!! Wani irin zuciya CE dakai ne ?? Yara sunyi laifi sunyi nadama anbaka haquri kaqi haqura ,ya kakeso ayi dakai ne ??gaskiya inaji INA gani bazan tsaya 'yata ta cutu ba ,nagaji ,nagaji ,nagaji ,abinnan ya isheni  ,wallahi idan baka sassautaba zan sanarda hajiya abinda  ke faruwa ,inbakaji maganar kowa ba ita dole kaji tata ,tunda mahaifiyarkace      " wani mugun kallo Abba ya watsawa mama sannan ya miqe tsaye ya nuna mama da yatsansa yace "kina tambayata wace irin zuciya CE dani ko ,?tuntuni bakisan irin zuciyata ba tsawon zaman danayi dake ?
lallai tabbas kinzama BILHU ,to kisani in ma baki saniba !zuciyata cike takeda kishin iyalina da 'YA'YANA ,abinda safah ta aikata mummunan abune agareni yadda ta b'atamin nima saina b'ata mata wallahi ,sanda zata aikata abinta batayi shawara daniba ,danhaka nima Baku is a inyi shawara dakuba ,muddin INA Raye na fad'a na nanata ba aure tsakanin Abbas da safah ,zancen zaki gayawa hajiya bismillah ga hanyanan kije !ki had'ani da mahaifiyata !!amma kisani wallahi kika aikata haka to ABAKIN AURENKI !!!!!".   

"Gaban mama yayi mugun fad'uwa ,wannan wace irin masifa CE ?shekara da shekaru basu tab'a sa'insa da mijintaba sai yanzu ?hard a ambatar SAKI "innalillahi wainna ilaihirrajiun "        lallai ta tabbatar qila da gaske dai rabuwar safah da Abbas tazo !!qaddararsu CE tazo a haka ,lallai wannan shine ake kira SANADIN HOTO KO KUMA K'ADDARA "" .juyowa mama yayi da nufin yiwa Abba magana saitaga wayam Ashe yana gama magana yabar gurin ,jikin mama yayi sanyi azuciyarta tafara juyayin taya safah baqin cikin rabuwa da babban masoyi !!ta juya ta kalli safah cikin tausayi saitaga tanata zubarda hawaye fuskarta sharkaf alamun taji duk maganganun Abbanta saidai ba bakin magana ,tausayi yasa mama yin hawayen itama ,ta janyo safah jikinta taqara rungumeta qaqam ,hawayen safah nazuba a qirjin mama har said a gaban rigar mama yajiqe saboda hawayen safah masu zafi dasuke zuba banda ajiyar zuciya babu abinda takeyi ,haka mama tasa hannunta taita shafa bayan safah alamun rarrashi ,ta dinga karanta mata add'ua cikin kunnenta ,hartaji shiru alamun tayi baccin wahala............."".       

SANADIN HOTOWhere stories live. Discover now