page171to175&176to180

563 21 0
                                    

[1/3, 7:24 AM] Obama: 💔💔💔❣❣❣💔💔💔❣❣❣










*SANADIN HOTO*










*HASSANA D'AN LARABAWA*✍✍✍









*page 171 to 175*







*DAD'INA DA GOBE SAURIN ZUWA ,ABIN YAZO KAINA KENAN ,ANSAMU MASU SAIDA MIN DA NOVEL D'INA SANADIN HOTO ,ALHALI NI FREE NE ,TO MASU SAIDAWA KUSANI ALLAH YANA KALLONKU KUMA BAZAI BAR HAK'K'INA BA ,TUNDA BADA YARDATA KUKE SAIDA MINBA ,NIMA BASON KUD'IN NE BANAYI BA ,AMMA SABODA KYAUTATTAWA NAKE YIN FREE ,TO KUSANI KUDA ALLAH YANA KALLON DUK ABINDA KUKEYI*




DEDICATED TO

*ZAINAB MAHMUD*

(sister Zainab)

*ina yinki over wallahi*






***A waje kamal yayi parking ,baishiga da motar ciki ba saboda yana saurin isa gun aiki ,sarai yaga su uncle tsaye suna magana shi da ya Abbas ,amma duk da haka kamo hannuna yayi kafin in fita daga motar ,yayi k'asa da idanunsa yana min wani kallo a hankali ya bud'e bakinsa yacemin .


"Yanzu kike son inshiga inga babyn ko inbari sainazo d'aukarki ??

" nima na dubeshi ina shagwab'e fuska nace "nifa kwana zanyi yau a gida ,karma kazo d'auka na ,gara dai kashiga yanzu kaga babyn ko ???


Wani miskilin murmushi yayi yana k'ura min ido yace " kwana kuma ?a ina zaki kwana ?keda kwanan gidan Abba kuma ai har abada !don bazan iya ki kwana wani gurin ni ina wani gurin ba ,gara ko ba a d'akin ki nakeba ya zamto muna guri guda ni dake !Dan haka kibarma wannan zancen .......!



"Kallonsa nayi yana rik'eda hannuna sai murzawa yake ,nad'an kwab'e fuska nace "amma ita Maman hisham da tace zata kwana a gidan hajiya rannan ka barta ?amma ni zakace bazan kwana gidanmu ba ??


"Hannuna yasaki ya tallabo fuskata da hannayensa ya rik'e yana jifana da wani kallo yace" jamila daban !Aysha daban !sai dai duk d'aya kuke a wajena ,ragowar maganar na barwa zuciya ta ,dan wani zubin b'oye magana yafi bayyana ta alkairi ,idan nabar jamila ta kwana wani gun kisani kedai bazan iya barin kiba ,idan bawani babban dalili da yasha kainaba ".



***Ya saki fuskata ya juyamin bayansa ,cikin wata irin murya yace "ga uncle d'in ki can da yayanki Abbas ,kisani a yanzu ke matar aure ce ,sai ki San cewa nauyi ya hau kanki na tsare mutuncin ki da mutuncina ,Dan Allah kar kiyi wani Abu Wanda zanji zafinsa a raina, da ,da yanzu ba d'aya bane, kuma inason incigaba da ganin mutuncin Abbas da girmamashi ,amma fa saida temakawarki na nuna ni mijinki ne .....!


"Yana kammala maganarsa yafara k'ok'arin bud'e k'ofar motar Dan yafita .




" da sauri nakamoshi ina k'ok'arin dawo dashi mazauninsa ,zuciya ta tayi k'una akan maganarsa ,to me yake nufi ??yana nufin zargina yake kenan ??bai San nadad'e da cire ya Abbas a raina ba !na d'au k'addara ta ,gashima har munzama Abu guda ni dashi !ya Abbas d'in da yake shirin auren Y'ar uwata nan da sati d'aya ,ai yanzu babu wata alak'a tsakanina dashi saita zumunci kuma ".


"Juyowa yayi yana kallona idonsa cikin nawa ,har idanuna sunfara kawo hawaye,yayi sauri ya kauda kansa daga fuskata saboda bayason ganin hawaye na ,shidai yasani ,Allah yasani yanada zuciya a k'irjinsa ba zai iya jure abinda ya jure da ba ,yayi hak'uri iya hak'uri ,kuma harga Allah baitab'a k'ullatar Abbas a ransa ba ,saboda yasan Abbas abin tausayi ne kuma yayi jarumta ,sai dai gaskiya a yanzu yanajin kishin safah fiyeda k'ima a zuciyarsa ,ko da d'inma ya sassauta kishin ne saboda yayiwa Abbas halacci ,bawai Dan bayajin kishi a k'irjin saba ".




SANADIN HOTOWhere stories live. Discover now