[1/3, 7:24 AM] Obama: 💔💔💔❣❣❣💔💔💔❣❣❣
*SANADIN HOTO*
*TARE DA ALK'ALAMIN HASSANA D'AN LARABAWA*✍✍✍
*page 181 to 185*
*k'awata ,aminiyata ,wato Aysha Abdullahi bagudo ina tayaki murnar kammala littafinki me suna y'an cinki ,Allah yabaki ladan fad'akarwa da nishad'antarwa,inda kikayi kuskure Allah ya yafe miki ,sai mun jiki a sabon novel d'inki me suna MUWADDAT*
🥰😘😍🤝💃🏻
DEDICATED TO
*KADIJAT (khady pinky)**Maman eemaan*
***Anyi taro lafiya ,angama lafiya ,ansha hotuna iri iri amma ni da ya Abbas bamu yarda anyi hoto ko d'aya damu ba ,saboda dalilin tsanar da mukaiwa hoto.
"Hafsat bataji dad'in yadda angonta yak'iyin hoto da ita ba ,tanaji tana gani sauran angwayen da amaren sunata hotuna amma nata mijin yayi mirsisi yak'iyi ,babu yadda su uncle basuyi dashi ba amma yak'i ,da suka dameshi ma hawaye ya farai musu tilas suka k'yaleshi,Dan ya Abbas yazama a lallab'a.
Komai yacigaba da wakana agun dinner , muna zaune GU d'aya nida kamal ,nan nake cewa kamal ban bawa ya Abbas gudummawar saba ,saboda tunda aka fara bikin bangan shiba sai yau ,amma su ragowar duk naba su.
"Kamal yamin umarnin idan har natawo dasu yakamata inbashi yanzu ,kafin atashi daga gun dinner.
"Kiyi kiransa kibashi babu damuwa ".......abinda yace dani kenan .
***Na kalli inda su ya Abbas d'in suke naga mutane sun yanyame su anata gaisawa dasu ,amma shi wayarsa na hannunsa ,sai dannawa yake ,ko me yake oho .
"Zaro wayata nayi a jaka na daddanna numbobin ya Abbas da na haddacesu a kaina tamkar karatu ,har tafara ringin wata zuciyar tace ai text yakamata kitura masa ,ba kiransa zakiyi ba .
"Da sauri na katse kiran ,na rubuta text kamar haka ,na tura masa .
*ya Abbas idan ba damuwa inason magana da kai yanzu ,muhad'u a bakin hall d'innan pls*
*k'anwarka safah*
K'arar shigar sak'on ita tasashi dubawa ,aikuwa yana karantawa ya kallo inda nake ,nayi masa murmushi tareda jinjina masa kaina ,shima murmushin yayi na yak'e amma ,sannan ya taso a hankali mutane na tareshi Dan gaisawa amma haka ya yakicesu yasamu nasarar ficewa daga hall d'in.
"Fitarsa tabawa kamal damar rik'o hannuna ,na kalleshi sai ya d'agamin gira yana murmushi yace "kije gashican yafita kugama ,amma karki dad'e pls 🙏,kuma karki yadda naga hawaye a fuskarki Dan banaso kinsani ,Wanda kikayi yanzu ma a bayaninki ya isa haka .
"Na gyad'a masa kai ina murmushi nace " bazanyi kuka ba ay insha Allah mijina "
"Yawwa matata Allah yai miki albarka ,abinda yace kenan yana matsamin Dan na wuce .
***Ina taku d'ai d'ai nafita ,kamal yabini da kallo yana kuma jin sona a ransa da k'aunata da wani irin tausayi na .
"Can gefen hall d'in na tadda ya Abbas ,gurin babu mutane sosai ,yana tsaye yana abinda yasaba wato danna waya.
"Ina zuwa nace "kai ya Abbas wai me kakeji a danna waya ne ???kullum tana hannunka kana faman dannawa ???.......da walwala a fuskata na fad'a .
YOU ARE READING
SANADIN HOTO
Historical Fictionlabari ne da aka ginashi akan tsabtatacciyar soyayya ,wadda tafara tun daga yarinta ,dab da burin masoyan zai cika k'addara ta afka musu dalilin sanadin hoto ,kubiyoni Dan sanin shin k'addarar tana kaisu ga auren juna ko kuwa ........!?