[1/3, 7:24 AM] Obama: 💔💔💔❣❣❣💔💔💔❣❣❣
*SANADIN HOTO*
*TARE DA ALQALAMIN HASSANA D'AN LARABAWA*✍✍✍
*page 56 to 60*
,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,✍A wannan daren bayan Abba yashigo gida yaci abinci ya huta ,yasa mama ta kirawoni ,na shiga da sallama falonsa yana zaune a kujera yana kallon tashar saudiyya ,ya amsamin tare da rage volume ,nasamu gefensa a sanyaye na zauna a qasa kaina a sunkuye nace Abba gani ,,,,,
Abba ya dubeni ya qaremin kallo ,saiyaga kamar baniba ,nayi wata irin rama Mara misali ,kamar abusheni infad'i duk nazama wata silent kamar baniba ,sai lokacin yaji tausayina ya tsarga masa ,a hankali ya kalli mama da ke gefe a zaune tazuba tagumi tana sauraren jin yau kuma dame yazo ,sannan yajuyo ya kuma kallon safah dake sunkuye ya fara magana cikin sauqaqa murya ........
,,,,,,,,,safah abinda yasa nace mamanku ta kirawo minke inason muyi magana ne ni da ke ,kibud'e kunnuwanki ki saurareni ,yanzu tambayarki zanyi kibani amsa,,"NI WAYE A GAREKI ,MENENE MATSAYINA ??.
"" MAHAIFINA NE KAI '" Safah tace cikin dukan zuciya da rawar murya ,,,,,
Alhamdulillah !!!!tunda har da bakinki kikace min ni mahaifinkine ,kinsan kuwa mahaifi bazaiso ya ga y'arsa cikin damuwa ko cutuwa ba ,safah nasan cewa ke da mutane da yawa kallon azzalumi kukemin ,kuna ganin nazama me raba soyayya a tsakanin masoya ,wallahi ,wallahi ,wallahi safah ba haka bane ,SANADIN HOTO da kukayi kuna ganin kamar shine yasani kafewa akan magana ta ko??to kisani bashi bane !!!nasan dai shine SILA !!!amma jigon shine ,tunda HOTON da kukayi ya fito nake istikhara akan lamarinki ke da Abbas bantab'a ganin haske a lamarinba ,bani kad'aiba hatta malamaina NASA anyi amma duk bakinsu d'aya AURENKU BABU ALKAIRI KEDA ABBAS!!!inason kisani bantab'a qin Abbas ba domin kuwa D'AN amininane kuma nasan Abbas yaro ne mai hankali ,amma tabbas d'aukarki kuje kuyi hoto abin ya b'ata min rai girmansa kashi hamsin cikin d'ari ya zube a idona ,,amma na yafe masa ,saidai bazan iya bashi auren kiba .......
Inaso daga yau kije kifara addu'a da istikhara ,,zakiga abinda nake gaya miki ,so da yawa abinda kakeso baya zama alkairi agareka ,,kai dai ka nemi zab'in Allah ......
A sanda mukaje saudiyya ,da bakinki kike tambayata inane guri mafi kusanci da Allah Wanda inkikayi addu'a Allah zai amsa ,nafad'amiki *multazam* shine gurin ,kunje gurin kuma INA bayanku a sanda kike addu'ar Allah yabaki miji nagari ke bakisan afili kike addu'ar ba ,to safah INA farin cikin shaida miki Allah yakawo miki ZAB'INSA INA fatan zaki karb'eshi hannu bibiyu ,,inason in shaida miki ,,,,,
*NA BAWA KAMAL AURENKI*
"A gigice na d'ago ido INA kallon Abba na zuciyata kamar tafad'o daga qirjina ,daman tunda yafara magana kuka nakeyi ,shikenan dai ta tabbata narasa ya Abbas ,wayyo Allah na wayyo rayuwata ,wayyo ya Abbas d'ina 😭😭😭....zuciyata ta quntace atake kuma ta qeqashe naji duk duniya nazama marar rabo naji inama ba'a haifeniba ,a lokacin ji nake ko kuturu ko makaho ko nakasasshe Abba yabani zan karb'a tunda rayuwata batada amfani ,zanje inqarasa rayuwata cikin qunci har nakoma ga mahaliccina ,nasan tabbas anrabani da farin cikin zuciyata ,,,Allah sarki ya Abbas ko ya rayuwarsa zata kasance ???.
Ni kuma haka Allah yad'oramin tawa qaddarar !!!ga rashin masoyi na ga kuma AUREN ME MATA 😭ni mace CE me kishi banason kishiya ko kad'an ,amma Allah ya qaddara min zan zauna da ita duk da dai shi kansa kamal d'in bai d'ad'ani da qasa ba ........har alokacin ban fitar da ran zan auri ya Abbas ba ,,nifa idan ba gani nayi and'aura aurena da waniba bazan cire ya Abbas daga zuciya naba ...........,,,
Ina sunkuye gaban Abba nayi kuka nayi kuka har kamar hawayena zasu qare ,ita kanta mama da ke gefe zaune said a tashare hawayen tausayina ,ita kuma safah haka tata qaddarar take auren me mata ,matar ma wadda duniya ta shaida batada kirki shi kansa kamal d'in zaman haquri yake da ita!!!! Dalilin mahaifiyarsa ,saboda 'yar gaban goshin tace ,,,,
YOU ARE READING
SANADIN HOTO
Historical Fictionlabari ne da aka ginashi akan tsabtatacciyar soyayya ,wadda tafara tun daga yarinta ,dab da burin masoyan zai cika k'addara ta afka musu dalilin sanadin hoto ,kubiyoni Dan sanin shin k'addarar tana kaisu ga auren juna ko kuwa ........!?