page 26to 30&31to 35

484 25 0
                                    

[1/3, 7:24 AM] Obama: 💔💔💔❣❣❣💔💔💔❣❣❣.         

     *SANADIN HOTO*

                     *TARE DA*AL'QALAMIN HASSANA D'AN LARABAWA*✍✍✍

   
*page 26 to 30*

                               *kuyi manage da yanayin typing din kan agyara wayar*    

        ...."ranar munyi kwanan baqin ciki a gidannan ,domin kuwa mama da baba zainabu kwana sukayi a kaina sunamin addu'a ,saboda wani irin Abu da nakeyi har da surutai.
mama abun ya tsaya mata arai ganin hotonnan ba qaramin firgita tayi ba ,ta dai share ne kawai saboda halin da taga safah a ciki ,amma kam tayi matsanancin mamakin yadda Abbas da safah suka aikata hakan"" !!!!!!!!   
    Jira takeyi safah tasamu d'an sauqin yanayin jikinta sannan ta tuhumeta akan zancen yadda akayi hoton itama ,Dan tabbas dole Abba yayi fushi ,kuma dole ya yanke wannan hukuncin .

duk uba nagari bazaiso yaga 'yarsa a wannan yanayin ba matuqar ba tare da mijinta na aure ba "amma meyasa sukayi haka su kuwa ???

Tambayar da batada amsarta matuqar ba safah CE ta warware mata wannan qullin ba,Dan tasan ko giyar wake tasha bata isa ta doshi Abba da wannan maganarba!!!!!!
domin kuwa laifin su safah yashafeta itama ,Dan tun fitarsa baidawo gidanba sai sha biyun dare ,kuma bai nemeta ba yashige d'akinsa ya kulle ko abinci bai nemaba ,tafd'ijam rigiji gafji lallai Abba ya shaqa da yawa........           

   *********                  

  yadda gidansu safah aka kwana cikin tararrabi da tashin hankali ,hakama gidansu Abbas aka kwana fiye ma da gidansu safah ,Dan kuwa atun lokacin da uncle basheer yakai ya Abbas gida har zuwa wayewar gari hawaye bai bar zuba a idanun Abbas ba ,mamy dai tarasa kan zance tunda uncle ajuye ya bata labarin abinda ke faruwa ,tunda shima ba sanin mafarin abun yayiba ,"" ya dai cemata Abbas da safah sunje sunyi photo shine Abba yaga hoton ,ransa ya b'aci yaketa fad'a harma yace anfasa yin aurensu !!!! Wannan kalma tafi razana mamy ,saboda tasan raba Abbas da safah tamkar rabashi da numfashin sane ,tunani take a ranta wane irin photo sukayi harda Abba zai d'auki wannan tsattsauran matakin ????

Har uncle yayi mata sallama ya tafi cikin rud'ani take !!!! Ga Abbas kwance shab'e shab'e a falo banda hawaye da juya kai ba abinda yakeyi ,k'irjinsa suya yake masa ,in yayi kuyi have "" wayyo mamy zan mutu ,ki dannemin qirjina zai fashe "" hankalin mamy inyayi miliyan ya tashi ,haka ta dinga mai addu'a tana shafe masa a qirjinsa .....da kansa da ke masa ciwo kamar ya tsage ,.....a wannan dare ba'a maganar abinci ,sallah ma azaune yayita da taimakawar mama ,saboda inya miqe jiri ke kwasarsa,qafarsa taita rawa ,tsoro Yakama mamy !!!!karfa yaronta ya nakasa ,gashi tayi tayi suje asibiti yaqi ,intayi magana ya FASA mata kuka yana kiran safah ,tayi lallashin duniya amma yakasa daina kukan...  

Kwance take kan cinyarta tana shafa kansa!!!!! Cikin lallashi tace "son ka gayamin meya farune ??nakasa gane abinda ke faruwa ,wane irin photo ne kukayi ??
"meye dalilin baban safah ya Yankees muku wannan hukuncin???"".                

         " da kyar yake magana ,cikin qaramar murya wadda bata fita sosai saboda tsananin kuka da ciwon da zuciyarsa me masa yabude baki yabawa mamy labarin abinda yafaru tun daga farko har k'arshe ,ya qarasa da matsanancin kuka yana fad'in "" mamy kitemaka min !!!!kiji qaina!!!ki tausayamin !!!!Allah zan iya mutuwa mamy in aka rabani da safah ,itace jina!!! Ganin !!!!! Maganata !!!!!!numfashina !!!rayuwata !!!!farin cikina!!!!!!walwalata!!!!!!idan ba it's babu wad'annan abubuwan da na lissafa a rayuwata .....  Zan zama mutum Mara amfani Wanda baici ribar soyayya ba ,zanzama mahaukaci a soyayya ,zan zama mutum marar rabo mamy........  Kije kisamu Abba kibashi haquri ,nasan zaiga girmanki ya gafartamin laifin danayi masa........

SANADIN HOTOWhere stories live. Discover now