[11/13, 6:10 PM] Hassana D'an Larabawa🥰: 💔💔💔❣❣❣💔💔💔❣❣❣ *SANADIN HOTO*

745 30 0
                                    

[11/13, 6:10 PM] Hassana D'an Larabawa🥰: 💔💔💔❣❣❣💔💔💔❣❣❣

*SANADIN HOTO*

*TAREDA ALKALAMIN HASSANA DANLARABWA*✍✍✍

*page 5*

Awannan tsukin munata shirye shiryen tafiyarmu, ya abbas dai bayason rabuwa dani dandai bashida yadda xaiyi ne, kuma sannan ibada zanjeyi, nice nazama me lallabashi ina kwantar masa da hankali.

Ana saura kwana biyu mutafi, na tambayi maman mu akan zanje gidan su amira kawata muyi sallama, mama ta barni amma tace kada nadade, saboda abbanmu bayason yawo.

nashirya cikin atamfata me kyau *abc ghana* dinkin riga da siket kasancewar ni macece me diri sai kayan sukaimin cif siket din yazauna a quguna dam, kirjina kuwa masha Allah kamarsu tsone idanun mutum, gaskiyar magana Allah yayini da dukiyar fulani mayalwata masu tsari wanda sukaimin cif cif kamar nina dasawa kirjina su, kafin suzama haka kuwa lokacin danafara qirgen dangi kunya nakeji, musaman in ya abbas yazo muna hira ko karatu yakan tsuramin idanunsa, nikuwa innaga yana kallona saina kama mayafin jikina in cukuikuye shi a kirjina inta boye boye inyaga nai haka saidai yayi dariya ya girgiza kai kawai.

Bayan nashirya na dauko hijab dina nasaka naleqa dakin mama inmata sallama na tarar tashiga wanka, aikuwa sai nai maza nakoma na cire hijabin na dauki yalolon mayafi nasaka, shedan namin zuga akan kici wannan kwalliyar amma kisa hijabi aigara kisa gyale kwalliyar tafi fitowa, aikuwa dayake ance abunda ba kyau kyaune dashi tuni naganni nayi rangadadau kamar asureni a gudu,.

Nafito barandar gidanmu ina 'yan wake wakena, dai dai lokacin danaji anturo get din gidan mu anshigo, haba saiji nayi mun zabga karo, nayi taga taga zanfadi yai saurin rikoni nafada jikinsa, gabana ya yanke yafadi kirjina yahau bugawa, wani masifaffen kamshi yadaki hancina, jikina yahau rawa Kar kar nadago agigice ina kallonsa, bansan nashagala da kallonsaba saidanaji ya huremin ido yace""

"wannan kallonfa "

"cikin kyarmar murya nace, "sorry ya abbas bankula bane "saboda wannan ne karo na farko da jikina ya taba nasa, iyakata dashi yarikemin yatsu ko yajamin habata, shima yana tsananin taka tsan tsan akan hakan,.

Da murmushinsa me tsada yadubeni, saikuma naga ya gintse fuskarsa, "ke!!!! Inazaki da wannan shigar badai fita zakiyi ahaka ba? "

Na dubi jikina sosai sannan na kalleshi na rausayar da kai waini naga sahibi na zanyi iyayi "ya abbas gidansu amira zani zanmata sallama kasan kwana biyu yarage tafiyarmu "

Aikuwa ya dallamin wata shegiyar harara dabai tabamin irintaba, afusace yace, "ahakan zaki gidansu amiran?

Kinada hankali kuwa "?

Wane irin shashanci ne haka "?

"dalla malama koma kisaka hijab kirufe jikinki koki fasa fitar wallahi"

Ko angaya miki a garin mahaukata ake"?dazaa barki kifita haka "?na tabbata mama batasan kinfito hakaba, dan haka maza koma kisa hijaab, keni kicire kayanma duka ban yarda kifita dasu ba, karki kuma sawa ki ajiye inmunyi aure kyasamin ingani, amma bazan lamunci kidinga fita da irin wadannan dinkunanba.

Safah dai ta tsaya tsam ganin ikon rabbi, tun tana mamakin abbas hartadena, soyayyar dayake mata me girmace, amma baya hanashi motsa kwanjinsa akanta matukar tayi ba daidai ba.

Cikin shagwaba da kwabe baki tace "

"yanxu ya abbas me ye laifin shigata "?

Au!!! Tambaya ma kike "?lallaima yarinyar nan, Allah inbaki wuceba ranki zaiyi matukar baci, kinason fita duk mazan waje su kalleminke ne "?su cuceni, kalli kirjinki duk awaje.

SANADIN HOTOTempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang