page161to165&166to170

644 22 0
                                    

[1/3, 7:24 AM] Obama: 💔💔💔❣❣❣💔💔💔❣❣❣








*SANADIN HOTO*










*TARE DA ALK'ALAMIN HASSANA D'AN LARABAWA*✍✍✍










*page 161 to 165*








*don Allah masu tambayar sanadin hoto daga farko Ku dinga tambaya a groups bazaku rasa Wanda zai Baku ba ,wallahi abubuwa suna yimin yawa kuma kuyita bina PC kunacewa inbaku daga farko !gashi inajin kunyarku bazan iya hanawa ba ,sai dai wallahi ina takura ,kuyimin uzuri pls ,ga typing ,ga karatu,ga ayyukan gida da kula da yara ,sannan kuma inzo ina binku d'aya bayan d'aya ina turamuku tundaga farko ?to don Allah kuyimin hak'uri da uzuri nagode*







DEDICATED TO

*HASSAN TANKO (ATK)*
*muna godiya gareka wajan yimana posting d'in litattafanmu group group ,Allah yasaka da alkairi*













***mun jima cikin wannan yanayin daga ni har kamal ,yadda jikinsa yad'auki zazzab'i haka nawa ya d'auka ma ,yana kwance a k'irjina ya k'ank'ameni sai rawar sanyi yakeyi ,nikuwa azaba ta isheni tun ina kuka da hawaye har hawayen ya k'afe sai ajiyar zuciya ,kamal yakasa tashi ya temaki kansa balle ya taimakamin.



"Saida aka fara kiraye kirayen sallah na farko a masallatai sannan kamal ya iya mik'ewa daga jikina ,Wanda zuwa lokacin ko hannuna bana iya d'agawa saboda balai'n ciwon jiki ,da yadda k'asana ke rad'ad'i tamkar an bad'amin yaji a wajen".


"Babu k'arfi a jikinsa sosai saboda zazzab'in da ya rufeshi ,amma haka a daddafe ya sauka daga gadon yanata aikin kallona shi kad'ai yasan me yake ji a zuciyarsa game dani ,nikuwa idona a runtse yake bana iya ko bud'esu ma dalilin zafin da sukemin saboda hawaye me yawa da ya Fita a cikinsu ""



"Yana jin jiri kansa na sarawa haka ya isa toilet d'in ya had'a ruwan wanka ,saida yafara yin cikakken wanka da soso da sabulu sannan yayi wankan tsarki .......!


"Ya had'amin nawa ruwan sannan yafito daga toilet d'in ,zuwa yayi ya tsaya a kaina yarasa taya zai tasheni ,shi yayi tunanin bacci nake gashi bayason katsemin baccina musamman ganin yadda na jigata ,yasan yana tashina da kuka zan farka ,to amma bayason mu rasa sallar asubahi dole haka zai daure ya tasheni ".


"Bargon jikina ya yaye ,jikina babu wani sauran kaya ko fant babu ,runtse ido yayi saboda yadda yakuma ganin surata saida jikinsa yayi mugun harbawa ,yaji sabuwar sha'awata takuma bijiro masa tamkar ya lasheni yake ji ,wani so da k'auna da girmamawa   da kusanci me k'arfi yake ji yana huda ransa ,yasan sun zama Abu guda shi da safah ,ya karb'i Abu mai muhimmanci atare da ita wato budurci ,duk da cewa jamila ma shine ya bud'eta a ledarta ,to amma yau yaji abinda baitab'a jiba ,yau yaje duniyar da baitab'a zuwaba ,inama idan anje dawwama akeyi ba'a dawowa ,ba zai kwatanta safah da kowace mace ba ,lallai ya yadda y'a mace kowacce da kalar ni'imarta !kuma kowacce da kalar dad'inta da baiwarta......!


"Bai yanke abin yiba ,kawai sai yasa hannu ya sungumeni ya had'ani da k'irjinsa ,zazzafar ajiyar zuciya ya sauke saboda jin tudun k'irjina a nasa suna zungurinsa ,yayinda nasaki wata Y'ar k'ara saboda motsawar jikina, idonsa a kan fuskata yake nufar band'aki yana huramin iskar bakinsa akan idanuna dake lumshe fad'i yake "kiyi hak'uri Aysha ,banida bakin magana agareki yanzu ,kibani zuwa anjima lokacin da zakiji garau ,akwai zantuka daga zuciya ta zuwa bakina wanda zasu iso zuwa gareki ,kimin alfarma inbaki kulawa a yanzu Dan girman Allah matata ".


"Yana dasa aya a maganarsa muna shiga toilet d'in ,banida bakin magana sai dai inajin maganarsa ,ruwan da ya had'a me zafi aciki ya sakani a hankali ,na kwala uban ihu saboda azabar da naji a k'asana ,nayi zumbur zan mik'e amma nakasa saboda jikina babu k'wari ,shi yarik'eni yanata lallashina tamkar zai kuka ,haka na zauna tun inajin zafin ruwan harnafara jin dad'in ratsani da ruwan yake ,duk abinda ake nakasa bud'e idona in kalleshi saboda azabar kunyarsa da nakeji  tayaya zan iya had'a ido da kamal yagama sanin sirrina kaf ?nima kuma nagama ganin nasa sirrin Wanda ya kid'imani ya gigitani .........?!


SANADIN HOTOWhere stories live. Discover now