[1/3, 7:24 AM] Obama: 💔💔💔❣❣❣💔💔💔❣❣❣
*SANADIN HOTO*
*TARE DA ALQALAMIN HASSANA D'AN LARABAWA*✍✍✍
*page 81 to 85*
*INA MIQO GAISUWA DA FATAN ALKAIRI GARE KI YAYATA TA KAINA*
*SADIYA L D'AN LARABAWA*🥰
*QANWATA TA KAINA INA MIKI JINJINA*
*AMINA D'AN LARABAWA*🥰
*NA BAKI KYAUTAR PAGE D'INNAN QAWA TUN TA YARINTA ,KUMA TUN HANCINKI DA MAJINA ,QANWA GA MASOYI NA*
*SA'ADATU TIJJANI D'AHEER (MAMAN HAMDIYYA )ALLAH YARABA LAFIYA*😄😄
*ABBA YA FARA MAGANA KAMAR HAKA*
,,,,,,,,,,,,,,,,,Safah na kirawoki ne domin muyi wata magana ,abinda ke faruwa kusan sati uku ko biyu da suka shige nayi wani mafarki da ya sakani acikin tunani ,abinda nagani a cikin mafarkin shine ,keda Abbas kuna cikin tafiya riqe da hannun juna kun tunkari wata wuta da take ci baba baba ,idanuwanku sun rufe qiris ya rage Ku afka wannan wuta ,saiga wasu mutane su biyu mace da namiji ,sun tawo da gudun su sun kamoku sun janye Ku sun kuma rungume Ku a jikinsu ,ke namijin ne ya janyeki ,yayinda macen ta janye Abbas ,ba wani bane ya janyeki face kamal ,na duba domin inga wace CE ta janye Abbas ,Sai naga ba wata bace face HAFSAT ,kamal ya riqeki GAM yafara tafiya dake ,haka itama hafsat ta riqe Abbas tafara tafiya dashi ,kuna kuka kuna d'agawa juna hannu,,,,,,,A nan na farka jiqe sharkaf da gumi.......!!
,,,,,wannan mafarki yayi matuqar bani mamaki ,ba mamakin komaiba illah hafsat da nagani a ciki, nasaba yin mafarkinku Ku uku ke da kamal da Abbas ,kuma a kullum kamal keyin nasara akan Abbas acikin mafarkin ,,saina fara tunanin ko Allah ya turo hafsat tsakanin Ku ne Dan ta raba gardama ,bazan b'oyemiki ba wallahi safah ban tab'a tsanar Abbas ba nasoki da yaron nan ,matuqa gaya ,to amma SANADIN HOTO komai ya bayyana duhu ya yaye haske ya bayyana,akwai da yawa abinda zakaso Wanda ba alkairiba ,ka soshi ka qaunace shi ,amma daga qarshe yazamo sharri a gareka ,so da yawa mutane munayin kuskure bamayin bincike a aure kafin ayi ,domin akwai binciken da akeyi kafin aure kuma ana gane cewa auren zaiyi albarka ko akasin haka ,akwai da yawa da suke yin binciken kuma su gano akwai matsala amma suqi haqura dole Sai sunyi auren ,Sai ayi aure baza'a dad'eba afara samun manyan matsaloli da tashin hankali iri iri da talauci da rashin zama lfy ,,safah a TUN farkon faruwar matsalarku ta hoto zuciyata taso tayi muku afuwa saboda yadda naga kun damu ,to amma Sai na bijirewa hakan nashiga bincike da yawaita istikhara akan lamarin ,wallahi abinda naji a raina shine kwata kwata aurenku yaqara fita a raina ,sannan bincike ya nuna ko da kunyi auren akwai tarin matsaloli da zaku fuskanta a gaba, Wanda Ku kanku Sai kunce inama Baku auri juna ba ,,,,,,,,,,!!
Inason kisani sau da yawa zakiga auren da akayi soyayya me tsananin yawa da zurfi bai cika d'orewa d zama lfy ba ,amma bance duka ba ,sannan so da yawa auren da akayi shi Dan biyayya ba don zuciya na soba yanayin qarko ,ko babu komai za'aga mutuncin juna kuma za'a samu zaman lafiya da arziki me yawa ,Allah yana dafawa irin wannan auren ,kiyi haquri y'ata ,inason ki qara Sani yawanci irin soyayyar da take farowa TUN daga yarinta itama ba'acika yin aure akantaba ,a irin rayuwar mu da nahiyoyin mu kafin kisamu wad'anda soyayyar yarinta ta kaisu ga aure guda biyu ,wallahi babu kaffara Sai kin samu wad'anda saurayinsu na qarshe ma suka aura sunfi su hamsin ko d'ari ,,,,,,,,,!!
TUN fara alaqarki da kamal ban gushe ba INA bincike akan lamarin da istikhara ,wallahi kullum abin qara shiga zuciyata yake ,sannan kuma akwai tarin Alkhari a ciki ,koda zaki fuskanci qalubale to alkairin dake ciki ya ninkashi da yawa ,Dan haka kiyi haquri ki karb'i kamal a matsayin miji, ki masa biyayya ,Allah yabaki miji tamkar da miliyan ,wallahi safah duk wata soyayya ,jin dad'i ,kulawa tarairaya ,farin ciki ,da annashuwa ,zaki samesu a gun kamal fiye da yadda zaki samu gun Abbas ,ni mahaifinki ne INA sonki ,inason Abbas, bazanso Ku fad'a halakar da nan gaba zai dame kuba gara a haqura ,maganin kada ayi ,to kada a fara ,,,,,,,,,,,!!
YOU ARE READING
SANADIN HOTO
Historical Fictionlabari ne da aka ginashi akan tsabtatacciyar soyayya ,wadda tafara tun daga yarinta ,dab da burin masoyan zai cika k'addara ta afka musu dalilin sanadin hoto ,kubiyoni Dan sanin shin k'addarar tana kaisu ga auren juna ko kuwa ........!?