💧💧
_*MENENE MATSAYINA..*_
💦💦💦_*HAFSATTU💫*_
_Dasunan Allah mai rahama Mai jinkai...._
*1&2*
"Don ubanki wanki dana barmiki kimin shine kika kiyimin Kika zauna kika rungume wannan shegiyar d'iyar taki wallahi koki aje ta ko kuma yanzu jikin ki ya gayamiki nafada miki banza..."
Fuskar jike da hawaye ta d'ago ta kalleshi cikin kyarmar murya tafara Magana Haba! Noor...marin dataji a fuskar ta ne yasa bata Ida fadar Abinda ke bakin ta ''shegiya tun yaushe na haneki da furta wannan sunan gareni wallahi duk ranan danaji kin kara Ambata ta da wannan sunan na lahira sai yafi jikin dadi jaka kawai ball..yayi da ita daga ita har d'iyar dake hannun ta goshin ta ya bugu da bango d'iyar dake hannunn ta tsayanra kuka tare da Ambatar Umme...
''Kafin nadawo gidanan ki tabbatar da kimin wanki sannan kingyara min dakina nafada Miki..""
Juyawa yafita yabarta rushewa tayi dawani matsanancin kuka mai tattare da tausayi hannu taji da fuskar ana share mata hawaye "Ummee kidaina kuka kitaci mutafi gun Umman ki ko Uncle Abdul..." Rungume ta tayi.."zamuje Basmah Amma inaje gunsu *MENENE MATSAYINA..?*"
Rungumo ta tayi jikin ta "Ya Abdul kayafemin nasan hakki ka ne ke bibiyana Umma, Abba kuyafemin Abinda na aikata gareku nakasance mai butulci A rayuwa yau gashi hak'k'in ku da sakayyar ku yana bibiya yana wadda nazaba a matsayin Abokin rayuwata Basan *MENENE MATSAYINA*.. gunshi ba ya maidani cikakiyar baiwa marar yanci.." tad'au tsawon lokaci tana kuka Basma taga takoma bacci inda itama Basma tasha kukan ta domin taga ummin ta tanayi..wani yagalgalen zane ne ta dauko ta shimfid'e ta..d'akin sa ta nufa ta dauko uban wanki dake tule yana jiran ta tafito dashi bokitai tadauka tare yafa mayafinta tafita tafara jiddo ruwan wanki dazatayi sai data cika wani katon Abu da ruwa sannan tafara wanki sai yamma likis tagama inda tayi masifar gajiya bayan ta ya masifar rikewa haka ta daure ta nufi d'akin sa tana d'angyashi tafara gyarawa jawo wasu kaya tayi zata linke Abinda yafad'o ne tabi da kallo.. Brexiya ce da pant kundudene pant d'in duk sperm ne ya bushe jikin sa Hawaye taji yana bin fuskar ta zuciyar taji tana wani bugawa kamar zata fasa kirjin ta tafito jagwab ta koma bisa kujera tazauna tare da dafe kanta tashi tayi ta ida gyara d'akin a galabaice tafita.. ta iske Basma har tatashi k'ak'aro murmushin k'arfin halin tayi Basmar Ummi har kin farka?"...
''Ummi cunwa najeji.."
Gabanta ne yafad'i tuno da ko kwaran shinkafa babu cikin gida nan. ita ma kanta yunwar ke kwakwalar mata yan hanjita...Kukan Basma ne yadawo da ita daga d'angajeren tunanin data tafi dasauri ta nufi inda take ''Yi hakuri Basma kinji bari nasamo miki Abinda zakici waje tafita ta d'ebo ruwa a cup ta kwankwand'a ma Basma har tasamu tayi shiru wani bacci ya d'auke ta...rungume Basma tayi jikin ta tare da jinginar dakanta da bangon d'akin tana wani tunanin..Muryar shi ta razanata daga ita har basma data taji firgice......ta miqe....
_*HAFSSATU MUSA💫*_
YOU ARE READING
MENENE MATSAYINA...
Mystery / Thriller"Don ubanki wanki dana barmiki kimin shine kika kiyimin Kika zauna kika rungume wannan shegiyar d'iyar taki wallahi koki aje ta ko kuma yanzu jikin ki ya gayamiki nafada miki banza..." Fuskar jike da hawaye ta d'ago ta kalleshi cikin kyarmar murya t...