13&14

1.1K 51 0
                                    

______________

_*MENENE MATSAYINA.........*_

© _Hafssatu Musa_
      *Indon Kauye*
Not Edited❌
*13/14*
''Ummi sannu da zuwa Anzo lpy."..wani kallo tayi Mata kawai "Mekike cikin d'akin ne inata sallama baki Amsa min ne?"
''Kiyi hakuri Ummi banjiki bane wallahi'' tab'e baki tayi ''Ina Hasheem d'in?"..
Amal sani halin dayake ciki tattaro wata natsuwa tayi tare da Furta Mata yana ciki yana bacci."
''Muje b'angare na kigyara mani."..nufar b'angaren ta sukay,key tafito daga cikin wata jikka dake hannun ta ta bud'e d'akin Amal ta shiga tafara gyara  d'akin da duk yayi k'ura  ''Ummi nagama"..
Gyara laffayar dake jikin ta tayi "Muje nagani." D'akin suka nufa ''Inda d'akin uwar ki ne kibar sa da wannan dirty labulen da Blanket d'in?"...

"Kiyi hakuri Ummi."
Amal cire labulen tayi tare da yaye Blanket d'in tafara wanke su hannun ta har saida yayi jawur ga   kugunta da yayi masifar rik'ewa Kukan Basma taji dasauri taje ta dauko ta ta aje ta nan kusa da ita ta cigaba da wankin har wajen magariba sannan ta idar d'akin Ummi ta nufa ta iske tana waya Basma suna shiga ta k'ara lafewa jikin uwar ta Ummi saida tagama wayar ta juyo ta kalli Amal ''Ummi nagama."
''Basma yaki nan"..Kuka ta saka tare da  kara maqalqale Ummar ta
''Bilkisu k'iyayar tawa zaki nuna jikar tawa..".. aaa Umme" Gashi kuwa taki yarda dani tun tashin ta dama kike nuna mata kiyayar tawa wataqila ba jini na bace A kwararo Kika samo ta ko?" kirjin Amal yabada wani dam.."wallahi Ummi Basma jininki ce bantaba Aikata zina ba tunda nike A rayuwata jikar ki ce  Ummi."..

''Ke rufemin baki kitashi Maza Maxa kimin girki yanzu inajiranki,"
''Ummi bamu da Abinci A gidanan"... Ina kike Kai Abincin yau fa banfi sati biyu da barin gidanan ba nabar Abincin tule a gida sannan kice min babu Abinci tashi  Muje gun Hasheem d'in part d'in su suka nufa lokacin hasheem ya fito yana ma karuwar tashi bankwana suna tsaye..ihu yayi kamar wani arne yayi hugging din Ummi ''Ummi na yaushe kikadawo ne?''

''Yau nadawo.''
Idon ta tamaida ga budurwar dasuke tsaye cikin harshen fulatanci tayi ma Hasheem magana ''wacece wannan"

''Ummi Abokiya nace tazo ganinan''
Kallo buduwar yayi cikin harshen Larbci  ''Nadiya ki gayar da ita Ummi na," Nadiya matsowa tayi kusada Ummi tayi Hugging d'in ta tare da sumbatar ta  Gaisawa sukayi sannan Hasheem yaraka Nadiya  duk Amal tana tsaye 

''Hasheem ina wannan yarinyar kikai Abinci gidan har da zance tayimin girki tacemin Babu Abinci a gida nan?"..

''Ummi na bansan inda take Kai Abincin ba nafada Mata ba kud'in banza gareni ba kamar b'arawon uban ta."..

''Hasheem zaman uban mi take a gidanan Amfani metake maka tunda Abinda kake nema bata Amfana maka ba meyasa bazaka sawaake mata ba ne tunda ba Auren zobe kukayi ba,''

''Ummi kijira saura lokaci kad'an."..Amal dake tsaye cikin wani tsananin Fushi ta nufi Hasheem...

_*Manage pls*..🙏🏻_

*Insha Allah komai yadaidaita zakudinga jina akai Akai Nagode😘*

*Comments*
     *&*
*Share*

MENENE MATSAYINA...Where stories live. Discover now