32

913 71 0
                                    

_______________________
    
    _*MINENE MATSAYINA...*_

© _Hafssatu Musa_
      *Indon K'auye*

*NO.... 32*

__________
*AFTER 3 MONTHS....*

Suna zaman su cikin kwanciyar hankali babu Abinda kedamunsu sai soyayaya sabuwa datake k'aruwa kodayaushe tsakanin su Aliyu tuni ya watsar da zance gwagwo ganin har wata 3 bata k'ara tadamishi maganar itada tabashi wata 2 gashi har Anyi wata 3 kwance take bisa cinyar shi ''Ya Aliyu inason zuwa Egypt kwana biyu nan ina yawan mafarkin Aunty jamila tana d'ago min hannu fa" shafo kanta yayi ''Fatyma bakiyi wata da dawowa ba fa kuma  kuna waya ba"(Lokacin ba wayar hannu sai telephone ko Akwaita sai manya masu kudi da sarakuna  gidan wane da wane To Aliyu yanada ga cikin wadda suke da wayar)

''Allah yah Aliyu inason ganin Aunty jamila da Boy na Abdul." Kedai jininki ya had'u da Abdul kodai nace Aunty jamila tabamushi ne?" Wani mik'ewa tayi Amma danaji matukar dadi Habibi Amma da wuya Abbie Anwar yabamushi domin bayasan yaranshi suyi nesa dashi kodako da kwana d'aya ne inada yazo Nigeria".."kiyi Add'uar Allah yabamu namu muma"..

Sallamar Gwagoo sukaji dasauri ta mik'e daga jikin Aliyu tare d'auko mayafin ta ta d'ora bisa
"Sannu da zuwa gwagwo" hannun ta rike da wata da fuskar ta ke lullube  gwagwo zama tayi itama matar ta zauna kusada gwagwo Fatyma k'asa ta sakko tana gaida gwagooo ba yabo ba fallasa gwagwo ta Amsa,juyo fuskar ta tayi wajen Aliyu wadda tun shigowar ta gaban shi ke fad'uwa  "to Aliyu ta dai faru ta kare yau Alk'awarin Allah ya cika yau And'aura Auren ka da zuwairah ga matar ka nan wallahi Aliyu ka cuci  Zuwairah kaida matar ka Allah ya isa nono da kasha..." Fatyma tunda gwagoo tafara maganar taji kanta yana juya mata Add'ua tafara jerawa   sannan taji sanyi  ka kaita d'akin ka ta kwanta kafin gobe da safe na turo su Asabe su shara waccen b'angaren dazata zauna".. Gwagoo juyowa tayi wajen Zuwairah wadda tuni ta d'age mayafin tana binsu da kallo cingum take tauna kasa kasa ''zuwaraih ko meyayi miki shida wannan juyar matar tashi kizo kifadamin kinji ko"

"Insha Allah gwagoo."
Gwagoo mik'ewa tayi zuwairah tabiyo ta domin yimata rakiya sannan ta dawo kallon Aliyu tayi da Fatima cikin kwarkwasa inda tuni ta cire Mayafin ta nufo wajen Aliyu ''Haidar kasha kuruminka ga  wadda zata haifan maka yara nan cike da gida tazo..."

Aliyu tsaki yaja tare da jan hannun Fatima sukabar wajen Zuwairah dariya tayi tare hayewa bisa kujera ta d'ora kafa d'aya bisa d'aya ''saini zuwairah d'iyar ladingo Ku iyayen kauna sai na tarwatsa wannann k'aunar nazama ragamar komai tadawo k'ark'shina"...wata dariya tayi.."


*Manage pls*...

*Tabdi😳karku manta kuma ku shiga rudu muna cikin labarin Amal*

Yan wattapad nakusa daina muku post tunda bakwa voted dina kuma kuna gani..

MENENE MATSAYINA...Where stories live. Discover now