38

881 44 1
                                    

_______________________
    
    _*MINENE MATSAYINA...*_

© _Hafssatu Musa_
      *Indon K'auye*

_*NO...38*_

Umma tamkar taga wani Abin tsoro "Abdul kanajin Abinda kafada kuwa?" Sakin hannun Abdul tayi zata fita cin karo tayi da Abba fad'awa tayi jikinsa Abban Abdul wai Abdul baisanin ba baisan kuma kowane Abdul nake nufi ba" Ki kwantar da hankalinki Ummun Amal bari nakira Likita" Office d'in Likita Abba ya nufa yakirashi..Bayan dan wani lokaci doctor ya duba Abdul  juyuwa yayi   ''Am sorry Alhaji Aliyu dama nafada muku cikin biyu saidai d'aya ko yayi loosing d'in Memory sa ko kuma ya tabu da tabin hankali to bisa tambayoyin sa daga nayi yanadaga cikin gwaje gwajen mu kuma kaga yadda ya nuna hakan bazai nuna bazai taba warkewa ba Aa yana iya d'aukar kwanaki weeks  wattani shekaru, wani kuma  har karshen rayuwar sa..."..Doctor zamu iya fita dashi k'asar waje?'' Doctor Murmushi yayi tare da Kallon Umma..Hajiya kiyi hakuri duk k'asar da zakuje bazasu iya warkar da shi ba sai lokacin da Allah ya nufa zai warware  saidai akwai maganin da zai taimaka mishi gurin dawo da tunanin sa" A hakan  Doctor ya dinga kwantar ma Umma da Abba hankali..

       ~*One week later*~

Jikin Abdul yayi sauqi  babu inda ke mashi ciwo,Amal kuwa kullum cikin kuka take ganin yadda Abdul kemata kamar bai san taba sai Umma ta tilas mata sannan take cin Abinci kwata kwata takoma suku suku kamar ba Amal ba gwago ba shiri tadawo daga  yola tashiga tashin hankali sosai itama ganin halin da Abdul yake ciki Amal yar gatan gwago tasha rankwanshi gun gwago jin sanadiyar ta Abdul ya had'u da wannan lalura d'in   gwaggo takara jinjina wannan kauna da Abdul kema Amal tare..

*After some Months*

Amal sunyi Exam din fita daga jinour section saboda rashin maida hankalin da batayi tana cikin damuwar rashin lafiyar yayanta tafadi dole sai ta maimaita wata shekarar Amal bata damu ba  Add'uar ta da burin ta Allah yaba yayanta lafiya  yadawo yana tarairaiyarta kamar da  yana kula da ita kamar da,

''Umma yaushe ya Abdul zaidinga ceman Amal Baby kidaina Kuka ''Amal mekikeso  baby zaki sha chocolate zakisha Apple Baby zona goyaki zona miki Girki Umma yaushe yaushe?""""

Umma goge hawayen Fuskar ta tayi ''Amal kicigaba dayima yayanki Add'ua zaiji sauqi insha Allah kinji ko kidaina damuwa." Amal mik'ewa tayi ta nufi d'akin Abdul kwance ta iske shi ''Ya Abdul nice    fa Amal dinka Don Allah ka tuna ni kaga nafadi Exam nadaina kokari a school dole sai nayi repeat."
K'ura mata ido yayi kokarin tuno wani Abu yake Amma yakasa maido idon shi yayi ya rufe Kuka Amal tasaka tare tashi tabar d'akin Abdul jin kuka yake Amma yarasa ta yadda zai rarrashe ta tashi yayi dafe da kanshi yayi  ya fito kusada Umma yazauna Apalour umma jawoshi tayi ta d'ora A kafada ''Yaro na Allah ubangji ya baka lapiya cikin gaugawa...

____________________
Abba ne cikin Mota shida Umma da Amal da Abdul sunfito zagaye gari ko sun d'ebe kewa go slow ne yayi yawa bisa hanyar Idon Abdul ne  bisa titi yana kallon kanshi namishi masifar ciwo go slow din ne yafara ragewa wani makaho ne da yar jagora suka tafo zasu ketara titi wata mota ce data fito daga go slow din tatafo dagudu inda tayi sama da makahon da yar jagora din Duk kan idon Abdul wata k'ara yasaki tare dafe kanshi ya sume..Rikece Abba suka nufi Asibiti....

*AFTER FOUR HOUR'S*

Bud'a idon sa yake A hankali ya kalli d'akin sunan Amal yafara Ambata da karfi mik'ewa yayi da karfi su Umma ne tsaye kanshi ''Umma Ina Amal  "Umma karkice min wani Abu ya sami Amal don Allah Umma  Amal dake bayan umma ta labe tuni ta fito ''Ya Abdul  ka tuna ni yanzu kasani  Umma ya Abdul ya tuna ni yanzu da gudu tafada jikin Abdul.Murnar da family d'in nan suka shiga bata mistulawa dawowar Abdul cikin hayyacin sa inda suka shirya hadadiyar waleema tadawo hayyacin sa suna ma Allah Godiya..

   
      *AFTER 4 YEAR'S*

Wata kyakyawar budurwa bazata wuce 17 year's ba Amma zaka iya cewa tayi 19 year's  kuka take rike da cikin ta duk ta yaye Blanket d'in datake sama gashin kuwa duk ya barbazu bisa pillow d'in datake kwance bisa wani kyakyawan handsome guy ne ya turo kofar d'akin ya shigo guy d'in ya hadu inda bazai wuce 23 year's kwala ma Amal kira yake Amma yaji shiru nishin yakeji A hankali dasauri ya kalli inda yakejin numfashin cikin tsananin firgici yanufi gun har yana tuntunbe....

Follow me on wattpad
@hafssatu
#vote
#comment....

MENENE MATSAYINA...Where stories live. Discover now