46

1K 53 1
                                    

_*MNNM*..._
_*NO..46*_

Abinda Amal ta furta yasashi tsayuwa cak! ...."kada ka kuskura  yah Abdul ka matso inda nake kana matsowa wlh Zan caka maka kaina wuka sannan na kunna fetir duka gidan ya k'one"..

""Aaahh Amal don girman Allah kada kihakan banason ki mutu kafira ki mutu ubangji yana tsananin fushi dake sannan kisaka su Abba cikin tsananin tashin hankali..mekikeso nayi miki?''   "Inason yanzu yanzu kace ka sakeni don bazan tab'a sonka ba  yah Abdul.." "Amal bakya tunanin halin da Abba zasu shiga duka yau fa wata d'aya da Auren mu don Allah Amal kiyi hakuri kiyi biyaya kinji inasonki ina kaunar ki kaunar bayan umma da Abba duk duniyar nan Amal babu wadda yafi kaunar ki fiye dani Amal yayan Abdul d'inki ne.." Abdul durkuwasa yayi k'asa "Amal yau gani durkushe gabanki  ina rokon ki yarda dani nazama zab'i ranki..."
Amal kauda fuska tayi wani tausayin Abdul taji zai shige ta itama durkusawa tayi Amma bata Aje fetir d'in da Ashana da wukar hannun ta had'a hannun tayi waje guda ''yah Abdul indai soyayar gaskiya kakimin kana kuma son farin cikina ka sadaukar ma Hasheem dani inkanaso kacigaba da ganin dariya ta da murmushi na kuma kanason farin ya wadatu gareni kabarni naje na auri zabin raina kai kuma Zan maka Add'uar Allah yabaka wadda tafini komai wallahi inban kashe kaina yanzu ba wata rana Zan iya samana poison duka muci mu mutu.... "Innalillahi wa inna illaihin raj'un.."Amal tabbas ni masoyin kine kuma inason ki kasance cikin farin ciki na har Abada xan cika miki burinki Amal yanzu Allah yasan hakan yafi Alkhairi." Abdul kuka ya fashe dashi  Astagafurallah Astagfurallah "Amal furta wannan kalamar gareni tamkar inajin zuciya ta kamar ta fashe min Amma tabbas yazamin wajibi na furta "Amal na s..ake ki *SAKI DAYA*.."
Amal wani dum taji tarasa wane  yanayi take ciki Farin ciki ko baki cika kuka tafashe dashi shima Abdul kuka yasa tare da dafe kansa mik'ewa yayi yana layi hannunshi dafe da kirjin sa wani duhu ya dinga gani duniyar gabaki d'aya ta dinga juya mishi   luf daganan bai sake sanin a ina yake ba Amal kwallah k'ara tayi tare da  nufo inda yake...

*******

Ahankali ya bud'a idon sa tare da bin d'akin dayake ciki da kallo tabbas! A asibiiti yake meyakawoshi Asibiti tuno Abinda yafaru yayi runtse idon sa yayi wasu hawaye masu rad'ad'i suka dinga zubo mishi turo k'ofar akayi aka shigo tamkar wata munafuka  dasauri ya maida idon shi ya rufe...

*Flash back*

Lokacin da Abdul ya fad'i ya suma  Amal ta kwala k'ara da gudu ta fito kanta ko kallabi babu ta nufi neighbors d'insu tanemi taimakon su akan suzo su taimaka musu da taimakon maigidan da maigadin gidan  Aka saka Abdul mota zuwa Asibiti mafi Kusa dasu..

****
Zaryar ta takai 3 bai farka ba tana tsoron kuma kiran su Abba tafada musu suzo kuma yah Abdul yafada musu duk wani tsoro ya baibaiyeta..can Anjima Abdul yaji sauki samakon wata Allura da ya rubuta akaje pharmacy aka sawo ta akayi mishi dama yanada kudin ajikinsa..Amal nazaune barandar cikin Asibiti taga fitowar Abdul  mik'ewa tayi  tabi bayansa kawai napep ya tsaida ya shiga..itama napep ta saida ta shiga..Abdul yana shiga gidan bisa doguwar kujerar Palour d'in ya kwanta Amal d'aki ta shiga ta d'auko Mai nepep kud'in sa   inda tadawo tafara lodar kayan ta cikin akwati, Abdul yana kwance yaji k'arar jan Akwati  A hankali ya bud'a idon sa Amal ce har takai bakin k'ofa A hankali ya kirata cak! ta tsaya tasowar shi taji runtse idon tayi tana jiran saukar duka...muryar shi taji cikin sanyi jiki _''Amal koba aure ni d'an uwanki ko bahakan ba Addinin mu ya horar damu idan munyi saki mubar matan mu suyi iddar su A d'akin su   har sai tak'are sai dai insun zo da Alfasha  wadda take bayyaniyya,  mu zaunar dasu  kada mu cucesu  ko kuma takura musu  idan suna da ciki  mu ciyar dasu har sai sun haihu  idan  kuma su zasu shayar dasu mu basu ladar shayarwa  kuyi yarjejeniya da Abin sanin  shar'ia   idan baku daidai ta ba, to shi uban sai ya samo wata mai shayarwa Dabam_

(Allah  ne mafi sani ni daliba ce mai neman sani)

"Don haka ki mayar da kayanki d'aki har ki k'are iddar ki Indai nine yau zan barmiki gidan Amma kisani kiji tsoron Allah  kitsare mutunchinki ki kauracewa kowa harki kamallah iddar Alfarma biyu nake nema inhar akwai ajiyata tare dake ki kulamin dashi kinji ko..  Alfarma ta biyu kada ki sanar dasu umma har sai ranan da kika kamallah iddar ki ina miki fatan Alkhairi farin ciki ya cigaba da bibiyarki har k'arshen rayuwarki  inason ganin Murmushi ki kodayaushe k'anwa ta.. ".. Abdul d'aukar akwatin Amal yayi ya maida mata shi ciki sannan yafita bada jimawa ba yadawo kud'i yamikata kimanin 500k "gashinan inkina buk'atar sayen wani Abun nasan zasu isheki yanzu zan aiko miki da kayan abinci da kuma wasu Abubuwan  buk'ata..juyawa Abdul yayi zai fita Amal kiranshi tayi "Ya Abdul tsayawa yayi batare da ya juyo "Kayi hakuri nayi bakin ciki saka soyayarka cikin zuciyar ta. " Abdul juyowa yayi ya kalli Amal Fuskar shi cikeda hawaye "karki damu k'anwata." ...Ina miki fatan Alkhairi juyawa yayi dasauri ya fita.. Amal fad'awa tayi bisa gado tare da fashewa da kukan data rasa ko namenene...

MENENE MATSAYINA...Where stories live. Discover now