_______________________
*MINENE MATSAYINA.......*
© _Hafssatu Musa_
_*Indon kauye*_*Page 24*
_NOT EDITED❌_*BIKI BUDIRI*
Kowane b'angare sunata hidimar su inda yau yau saura kwana d'aya bikin Ayau gidan su salma Mammy ta shirya k'asaitaciyar waleema inda Malama Maryam tayi wa'azi mai ratsa jiki ga ma'aurata da rayuwar Auren su inda take cewa
_"Ki kasance mai hakuri a cikin rayuwar auren ki domin shi Aure Ibada ne ki kasance Mai biyayya da bin umurnin Mijinki domin Aljannar ki tana karkashin k'afar mijinki karki zamo marar biyaya tare b'ata Aljannar ki kizamo tamkar baiwa a wajen mijinki wata rana shi zaima kamar_ _bawanki har_ _wasu kiji suna cewa ''Ai ta Asirce shi ne ta_ _mallake shi boka ya mallake Mata shi" yar uwa babu Abinda zaija miki face hakurin nan naki da biyayar ki da_ _tausayi da tausasa harshe da hakuri da mijinki tare yi mishi Add'ua a kodayaushe inhar ya nuna bayason Abu ki nuna mishi kinfi shi tsanar Abun A ranki inko yanason Abu ki_ _nuna mishi kinfi shi son Abun tare da kaunar Abu karki nuna kinajin zafin Abinda yake ma uwar shi da dangin sa domin_ _tunkafin ki san shi kika ganshi da dangin sa_ _karkiyi kishi da uwar mijinki ina nace miki Kalmar uwa ko banfada kinsan muhimmacin ta gareki don haka Mata ku gyara rayuwar Auren ku rayuwa ba tabbas karki sake da damar ki ta wuce ki rayuwanan k'alilin ce_ *MUTUM DA DUNIYAR SA*
*(AUNTY BILLYN ABDUL*)
_yakamata ya gyara_⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡
Fitowa yayi tsakar gidan inda itakuma take k'okarin d'ora sanwa Ummi tana gefe can wajen k'ofar d'akin ta Amal d'agowa tayi kawai ta kalle shi tamaida k'an ta ga Abinda take ''ke."
Shiru tayi kawai ta kyale shi wani hauri ya kaimata inda kanta ya bugu da bango Amal k'ara ta saki tare dafe kanta hasheem baijira komai ba ya rufe ta duka
''Naga wani rashin kunya ke damunki ne da kwanan kikemin rashin kunya narantse da Allah kad'an kenan daga hukuncin dazan miki inhar kikazama mai k'etare maganata da umurni na." Wani tsoron Hasheem Yakama Amal cikin kyarma murya tafara bashi haquri "kije kulsum na kiranki cikin sauri ta miqe tanufi d'akin Kulsum tana kinshid'e bisa wani tuntu sallama tayi kulsum kuro ma Amal kallo tayi Amal wani tsoron Kulsum yakamata "A..aunty gani."..kulsum murmushi tayi ma Amal tare da bud'a bakin ta,nuna ma Amal tayi ta zauna Amal zama tayi gefen ta kulsum riko hannun Amal tayi tafara murza Amal ganin zata wuce gona da iri hannun ta yana neman shiga cikin rigarta dasauri ta fizge hannun ta tare da mikewa dagudu bangaje hasheem tayi dake niyyar shigowa, Kulsum kwafa tayi tare Ayyana azabar da Amal zata d'and'ana wajen ta har sai taci buri Akanta domin tunganin ta da ita nafarko ta kwad'aitu da ita jan hannun Hasheem tayi suka shige d'aki domin tuni taji wani feeling tunda tafara tab'a jikin Amal,💫💫💫💫💫💫💫💫
Ayau dubun mutane suka shaida d'aurin Auren Salma zayyan da Abdullahi Bilal akan sadaki 100k kunsan Abin ku ga bikin manya.baka gane a kowane yanayi yake farin ciki ko Akasin hakan gashi nan dai,
Salma tanajin Andaura Auren toilet tashiga ta d'auro Alwallah tazo tayi sujadda ga Allah da ya nuna Mata wannan ranan Abdul yazama mallakin ta tana rokon Allah yasa Alkhairi a rayuwar Auren su,
⚡⚡⚡⚡⚡⚡
"Abdul nasan har yanzu akwai soyayar Amal A cikin xuciyar ka rokon da nike ka rike Salma da muhimmaci nasan zakayi Alfahari da ita fiye da Amal kada ka cutar da ita Abdul." Abdul jiyayi muryar Abba na rawa Umma kuwa tuni ta fashe da kuka tuno wani lokaci can baya Abdul dasauri yanufo Abba tare da Umma,....
*Manage please*🙏🏻
#TEAM AMAL
#TEAM ABDUL
#TEAM HASHEEM
#TEAM SALMA
YOU ARE READING
MENENE MATSAYINA...
Mystery / Thriller"Don ubanki wanki dana barmiki kimin shine kika kiyimin Kika zauna kika rungume wannan shegiyar d'iyar taki wallahi koki aje ta ko kuma yanzu jikin ki ya gayamiki nafada miki banza..." Fuskar jike da hawaye ta d'ago ta kalleshi cikin kyarmar murya t...