44

937 47 2
                                    

_*MNNM*..._
_*NO..44*_

"Hello My Amal"
"Na'am  My hasheem."
"Ganinan a k'ofar gidanku." Zabure ta mik'e daga kwance da take.
''Dagaske Dear?''
"Zan miki wasa ne Amal baxan iya jure rashin ki ba, bazan iya rayuwa babu ke ba kifito naganki don Allah kozan rage radadin da nakeji kinji Babyna"
''Kwantar da hankalinka My hasheem  ganinan zuwa yanzu." Yauwa Baby na.".. Amal tashi tayi dasauri  wata doguwar riga ta d'auka baka tasaka tare yaye k'anta da mayafin rigar fuskar nan ta ta tayi fayau saboda kukan da take zira wasu flate shoes tayi A hankali tafara sand'a tafito har ta fito  harabar gidansu  maigadi tayima magana wata k'awarta zata tafo da ita fita tayi ta k'aramar k'ofa  tunda daga nesa hasheem ya k'ura ma Amal ido itama idonta yana  kanshi bud'e mata murfin motar yayi tana shiga ya maida ya rufe tare da tada motar wani  park suka nufa..hasheem k'ura ma Amal ido Ajiyar zuciya yayi ''Amal mene aibuna da iyayenki bazasu Amince su bani ke ba  Amal Ina Sonki rabani dake tamkar Anrabani da numfashi na ne Zan kula dake har karshen rayuwa ta... Hasheem tasowa yayi daga zaunen da yake durkusawa yayi gwiwar sa k'asa tare da had'a hannuwan sa waje d'aya "Amal munyi shak'uwa soyayar junan mu ta riga tashiga jinin jikinmu zuciyoyin mu sun zama d'aya tabbas kikabarni zakiji labarin mutuwa ta.."...Amal tasowa tayi ta tsugunna ''Hasheem zuciya ta tamkar kwalba ce sonka kuma tamkar ruwa ne da yashiga ciki ya daskare inhar za'a cire sonka daga zuciya ta sai Anfasa kwalbar..hasheem har kana tunanin za'a iya fidda sonka zuciyata tabbas inhar za'a iya dole sai anciro zuciyata an tatse jinin dake gudana cikin ta"..Murmushi hasheem yayi  ILove u so much.."   Iove you too."..

   ~After two days~

Kwana biyun nan sai Amal ta saci k'afa tafita gun hasheem sunje sunsha soyayar su  sun k'ara ma junansu Alqawari kala kala..

    Abdul kuwa jikin sa yad'anyi sauqi yana d'an boye damuwar sa saboda umma da Abba gwago batasan Abinda ke faruwa ba   kuma Abba ya hana A sanar da ita Komai...Amal ce zaune cikin motar Hasheem After isha'i ta sato jiki ne tafito  Abdul ne ke gangaro motar shi yaje gun Anwar idon shi ne ya hasko mishi kamar Amal zaune cikin mota d'in wani  wani Azababen kishi ne ya taso mishi dalle su yayi da fitilar mota tabbas Amal ce ko kashe motar baiyi ba ya fito ya nufi motar  hasheem   murfin motar  ya bud'e  Hasheem ji yayi An cakomoshi Abdul baiyi wata wata ba yafara kaima naushi ta ko ina ''Kaine dama ke hure mata kunne ko Amal tafi karfin ka kaduba yanayinka ka dube ta kasan baku dace da juna  waigowa Abdul yayi b'angaren Amal data rud'e har tafara kuka ganin yadda yafiddo ma hasheem d'in ta jini...
"Akan wannan d'an iska kike duk Abinda kikeso Amal dubeshi kwata kwata baiyi tsari da rayuwar ki ba"..Amal cikin kuka tafara magana ''Nidai ka kyaleshi kada kashe shi ya Abdul don Allah.." Abdul ko sauraren Amal baiyi ba juyowa yayi wajen Hasheem ''kafita daga rayuwar Amal tunda wuri nafada maka ba'asar Auren yan iska bane irin ku masu hure ma y'ay'an mutane kunne  yan iskan gari."..
Wani naushi zai kaima Hasheem ji yayi An rike Hannun ''Abdul sake shi.."
Abba ne ya gani tsaye
Abba kallon hasheem yayi "bakai ba  y'ata tabbas nak'ara ganin ka da ita duk Abinda ya biyo baya Kai ka siya da kudin ka   tanada Mijin ta..Abba wallahi hasheem nakeso ni." Wani hauri Abba yakaima Amal "Wuce kibani waje..." Dasauri Amal ta shiga gida tana gunjin kuka  Abba gargad'i yak'ara ma hasheem Akan yafita rayuwar Amal tunda wuri tunkafin yayimishi munin k'askanci.."..Abba riko hannun Abdul yayi suka shiga ciki, Hasheem  binsu da kallo yayi shafo hancin sa yayi jini yaji  runtse idon sa yayi maganar da Abdul da Abba ya dinga tariyowa  ''tabbas Don bana yafiya wallahi sai na kuntata muku  fiye da yadda kuka kuntata min tunda nake babu wani mahalukin dayataba dukana sai kai har kafiddo min jini."
Cikin tsananin b'acin rai hasheem yashiga motar shi   yatada kura yabar gun, mashaya ya *nufa don yaje ya tutulama cikin sa giya shi kad'ai zai ragemishi rad'ad'i...

Abba cikin tsananin fushi yashiga cikin gida Umma tana tsaye tana zarya dasauri ta tari Abdul ''Abdul meke faruwa ne meyasameka ne naga rigar duk jini ne?" Abdul dora kanshi yayi bisa kafad'ar Umma ''umma Amal batasona Umma zuciyata rad'ad'i takemin Umma mutuwa zanyi rayuwata batada Amfani." Kuka Umma tasa  innalillahi wa Inna illahin raj'un Abdul bazaka mutu don Allah kadaina furta wannan maganar kaji yarona."
Abba kuwa kuwa wani mugun tausayin  Abdul yakamashi ganin namiji kamar  Abdul yana zubar da hawayen shi Akan Amal  zuciye ya nufi d'akin Amal duka ya rufe ta ta ko ina ihun Amal sukajiyo dasauri Abdul ya mik'e "Umma  Abba ke dukan  Amal" dasauri  Abdul ya nufi d'akin Amal "Don Allah Abba kadaina dukan ta..''Abdul kafita daga d'akin nan tunkafin na had'a dakai wallahi."
Abba bazan bari ka duki Amal gabana gwara a sa sanda aita dukana wallahi"   dakyar Abdul yasamu yadaina dukan Amal cikin tsananin fushi Abba ya juyo ya kalli Amal ''baki isa ki canza min ra'ayi ba bana kuma magana d'aya narage kwanakin Auren ki da Abdul nan da kwana bakwai za'a d'aura muku Aure Abba juyawa yayi gun Abdul saikaje kafara shirye shirye.". Amal k'ara tasa "Abba yah Abdul bashi ne zab'i na ba.'' Fad'uwa tayi numfashin ta ya d'auke.. Firgece Abdul ya nufo ta Abba ta suma Abba don Allah don Annabi kabama Amal zabin ta bansan *MENENE MATSAYI NA* gun Amal ba in na aureta." . "wallahi Abdul sai na d'aura maka Aure da Amal saidai inkai kace kafasa." Juyawa yayi ya fita Umma nufo Amal tayi Abdul d'akin sa ya nufa yad'auko first aid don ma bama Amal taimakon gaugawa Amma babu niyyar numfashin ta zai dawo d'aukar ta yayi kamar wata baby doll ya nufi mota  inda umma itama ta d'auko mayafinta suka nufi Asibitin mahaifin Anwar Abokin Abdul...

MENENE MATSAYINA...Where stories live. Discover now