_______________________
_*MINENE MATSAYINA...*_© _Hafssatu Musa_
*Indon K'auye**NO...31*
Kallon ta yayi har ta shige Ajiyar zuciya yayi tare da mik'ewa ya fito daga gidan mota kawai ya shiga ya nufi gida tana kitchen tana girki taji shigowar sa d'auraye hannun ta tayi iske shi tayi ya dafe kanshi dasauri ta nufe shi ''yah Aliyu harka dawo ya wajen gwagwon d'in?''
"Lapiya lau tana gaishe ki"..Ya Aliyu sai naga kamar kana cikin damuwa Amma banason jinta yanzu bari nad'auko maka ruwa kasha kaji sanyi A zuciyar ka Habibi na", nufar fridge tayi ta d'auko masa ruwa masu sanyi ta tsiyaya mishi karb'a yayi tare kafa cup d'in A bakin sa har sai da ya shanye, Mik'ewa "zanje office Akwai wasu baki da zamuyi ne Mik'ewa tayi tare da kwanto da kanta bisa kirjin sa "Allah kiyaye Abin qauna ta nisful hayat Allah yadawo min dakai lapiya ya tsaremin kai da tsarewar shi yabaka Halak d'inka A duk inda yake," Aliyu k'ara matse Fatyma yayi jikinsa saboda jindadi Add'uar ta gareshi yana matuqar Alfahari da fatyn shi mace ce mai matuk'ar biyaya A gareshi ga magagunu masu sanyaya zuciya A kodayaushe zaman shi da ita bata b'ata mishi rai Amma tsakanin harshe da hakori Ana sabawa,"Ameen Ameen Matata..."
________
*BAYAN KWANA BIYU*''Ya Aliyu na lura Akwai Abinda ke damunka bazaka fadamin ba ne na lura kana cikin damuwa nayi shiru ne na d'auka Sana fadimin kaki fadaman kadainmin walwala kadaina cin Abin ci kafara gajiya dani ko yah Aliyu naki haifa maka baby's..."
"Yo badole ya gaji dake ba mace juya taki haihuwa saidai taci taba masai Aikin kenan.." Fatyma bin gwagwo tayi da kallo datake zabga masifa duk da wata hausar bata fahimta da Abinda take fada domin haryanzu bata kware da harshen Hausa ba,
''Sannu da zuwa gwagwo''
Kusan tare suka furta hakan Fatyma da Aliyu."
Samun kujera yayi tayi ta zauna Fatyma mik'ewa tayi ta kitchen ta shiryo ma Gwago drinks and food, gwagwo bud'a baki tayi taci tayi kat! Domin tana matuqar son girkinta,Fatyma mik'ewa tayi zata bar gun ''dawo." Fatyma komawa k'asa tayi ta zauna giwiwar ta k'asa kanta sunkuye "wato Aliyu don nace kayi Aure shine kad'aukemin kafa daf baka ba labarinka ko ke ki hana yayi Aure ne kunfi son kuta zama gidan shiru babu haniyar yara?"
''Aaah gwagwo nifa inason yayi Auren inafada mishi hakan kiyi hakuri karkiyi Fushi dashi don Allah", Dasauri Fatima ta mike ta nufi d'akin ta saboda kukan da yatafo mata baki d'aya Gwagoo tab'e baki tayi tare da mik'ewa tafita driver d'in ta yajata suka tafi Aliyu cikin sauri ya mik'e ya nufi Daki don rarrashin Fatima
"Ya Aliyu dama wannan yasa kashiga damuwa indai na hanaka Aure nazama mai son kaina ina maka fatan Allah yakawo wadda zamuyi zaman Arxiki da ita don Allah ya Aliyu kada ka wulakantani kaga Kai kada'i gareni a Nigeria kaine nakema kallon family d'ina kaine uwata kaine ubana"...
Fatima Ina sonki ina kaunar ki bazan taba wulakantaki ba har Abada kece d'aya tal a raina babu wata bazan iya Auren wata na hadaku ba nasan bazan yi Adalci ba tsakanin ku zan rarrashi gwagwo tabar maganar nan Kawai.....
*Anya kuwa gwagwo zata rarrarasu ko malam Aliyu?...*
Low battery Ayi hakuri dashi...
_*NEXT PAGE.*._
_*LOADING.*._
YOU ARE READING
MENENE MATSAYINA...
Mystery / Thriller"Don ubanki wanki dana barmiki kimin shine kika kiyimin Kika zauna kika rungume wannan shegiyar d'iyar taki wallahi koki aje ta ko kuma yanzu jikin ki ya gayamiki nafada miki banza..." Fuskar jike da hawaye ta d'ago ta kalleshi cikin kyarmar murya t...