💧💧
*MENENE MATSAYINA*..
💦💦💦
_*HAFSSATU MUSA*_
_Aunty Hafsee💕__*Littatafaina*✍🏻_..
_*1 Ciwon so.2 Dare Daya..3Abin Duhu..4 Muna tare..5..Yaxeed..6 Samu da rashi..7 Naga duniyar Aure.. 8 Sangarttaciyya..9 Mata ko Baiwa..10..Hafeez..11 Habeeba*__*My daughter BILLY S FARI 💋 daga farkon wannan littafin har karshen sa Mommyn ki ta mallaka miki shi kiyi duk yadda kikeso dashi naki ne Allah miki Albarka daughter na LYSM*_
*5&6*
Sauke tukunyar tayi tareda kashe gas d'in wata wankakiyar Warmer's ta d'auko ta juye leqawa tayi taga bai tafo ba dasauri tasamu wani kwano tadebi indomie yadda baza'a gane haka shima farfesu ta diba kuka tafashe dashi ganin Abinda tafi karfinsa tasan ko naman d'awisu taso ko babu shi Nigeria yah Abdul zai nemo Mata shi a kowace k'asa dake duniyar nan domin farin cikinta..
Goge hawayen tayi tare da d'aukar wani tire ta jera Warmer's d'in ta nufi d'akin shi dasu sallama tayi taji shiru sai wani nishi sama sama datakeji k'ara kutsawa tayi sakin tiren d'in hannun ta tayi kayan suka watse.
Dasauri suka dawo hayyacin saurin sakin saima yayi ita kam saima k'ara shige mishi tayi...''uban me ya shigo dake ne baki nemi izini ba?"
''Kayi haquri inata sallama naji Shiru kallon kayan data watsar yayi wani kallo ya watsa mata jikinta yad'au kyarma don tasan bazai mata da dad'in ba.
"Kayi hakuri don Allah.".
''Baby yanzu Abinda xanci ta zubar dashi haka saboda salon wulaqaci..''Am sorry honey.."
Nufo inda take tsaye yayi bai duba da goyon dake jikin ta yakai mata wani mari.."da rashin kunya irin naki Abincin xaki xubar a kasa ne." ''Kayi hakuri..." Saukar belt d'in dataji a jikinta ya hanata ida k'arasar magana..wata k'ara Basma tasa domin babu inda belt d'in ya sauka sai jikin Basma bai duba da k'arar da ta saka ba ya shiga Auna musu belt d'in ajikin sai da yaga taka numfashi sama sama sannan ya kyale ta..Kallon saima yayi..."Baby tashi muje restaurant kici Abinci daganan sai wuce hotel.." Miqewa tayi tagyara mayafin jikinta ta dauki jikar ta haka suka fita suka tsallaketa.
A hankali tad'an bud'a idon ta tare da miqewa sauko goyon basma tayi gani tayi kamar bata numfashi "Basma''
K'ara tasaka tare da Ambatar sunan Basmar da k'arfi..."Hasheem ka kashemin Basma..".__________Goge hawayen fuskar tayi dasauri tareda k'akaro murmushi "Abdul har kadawo daga office d'in ne'' gyada Mata kai yayi ''Umma yaushe xaki rage tunanin Amal ne a ranki Umma .."
"Abdul kodayaushe tunanin Amal yaki bari zuciyana ina yawan mafarkin ta tana cikin wani Hali Abdul.."..
"Add'ua zamu cigaba dayi Umma kirage damuwa nan din don Allah miqewa yayi dasauri yabar gun part d'in sa ya nufa takalman sa kawai ya cire yafada bisa gado kuka yasaka mai tattare da tausayi ''Amal tunaninki yakasa barin zuciyana Ina daurewa ina nunama su Umma babu komai Amma nasan tabbas nafiso shiga damuwa na rashin ki Amal wata loka ce yace ya bud'e wani diary ya d'auko yayi rubutu yana kuka ya d'ora mishi bisa kirjin sa "Amal Ina kikashige ne kika zabi soyayan Akan farin cikin Umma da Abba.. Amal kece farin cikina...
_Hmm turkashi wai yawannan Abu yakene...kubiyoni A hankali Zan war ware muku Komai..nasan yanzu kunfara korafin rashin typing dayawa😞_
*Comments& Share.*.
YOU ARE READING
MENENE MATSAYINA...
Mystery / Thriller"Don ubanki wanki dana barmiki kimin shine kika kiyimin Kika zauna kika rungume wannan shegiyar d'iyar taki wallahi koki aje ta ko kuma yanzu jikin ki ya gayamiki nafada miki banza..." Fuskar jike da hawaye ta d'ago ta kalleshi cikin kyarmar murya t...