FINALE

1.8K 94 9
                                    

_*MNNM*..._
_*NO..49+50*_

Zaune yake yana duba wani Abu A cikin lap top d'insa fitowa tiki tiki tana tafiya dakyar, dasauri ya tashi ya rik'e ta "sorry Maman twins."  Yauwa Hubby" samun gefen shi tayi tazauna inda yata zauna gefen shi cikin shawgba tafara magana "hubby k'afufuwana duk sumin nauyi mud'an je yawo gashi inason shan Agwaluma da cheese mufita nad'an motsa jikina".."Angama madam ko mekikace hakan za'ayi." Murmushi tayi tare da riko hannun Abdul k'ura mishi ido tayi fashewa tayi da kuka  dasauri Abdul yadawo ya zauna "meyafaru salma me akayi miki ne?"   Cikin kuka tafara magana  "Abdul don Allah ko bayan raina *KAR KA MANTA DANI*" Abdul kallon Salma yayi rungumota yayi jikin sa  "Salma wace irin magana ce kike hakan?" Abdul inajin A jikina tamkar wannan cikin shine Ajalin a shine zai rabamu da juna." Salma don Allah kidaina fad'in hakan zaki haihu lapiya mu kuma raini Abinda kika haifa tare harki k'aramin wasu 12 d'in." Murmushi Salma tayi kawai domin ita kad'ai tasan Abinda takeji .."banyarda da wannan murmushin ba kamo ta nan kamo tanan Matar Abdul." Dariya salma tasa Ajiyar zuciya  Abdul yayi bari nad'auko miki hijabin ki mutafi zamu biya gida zanyi ma Abba rakiya airport yau zasu kano weekend"  Abdul d'aki ya nufa don dauko ma Salma Hijabi binshi tayi da Kallo "Ina kaunar ka Mijina Abin Alfahari na duk danasan banice zabin ranka Amal rigani"..

****

A hankali jirgi ya dinga saukowa har yasauko ak'asa Airport d'in Abuja bada jimawa ba fasinjoji suka fara fitowa  Sanye take da doguwa riga bak'a sai tulin zannuwan dake jikin ta fuskar nan ta fayau   rungume take da basma wadda bacci ya d'auke ta sai wani d'an k'aramin Akwati dake hannun ta   iska taja "Alhamdulilah na shaki iskan k'asata duk ba gari bane tattakowa ta dinga yi A hankali har ta safko  tana tsaye tana tunanin inda zata dosa ta hau motar hayar dazai Kai ta kano jiniyace ta karkad'e filin airport d'in motar mopal ce sai kuma dunkulalar mota mai Azabar kyawu  guda biyu har gaban  motar  mopal d'in hakan tasamu kanta da fad'uwar gaba  Mai taxi take san samu d'agowar da zatayi wadda tagani yafito daga motar fuskar sa dauke da murmushi ya bud'e ma wata kyakyawar mace kofa tare riko hannun ta k'ara murza idon ta tayi inhar idon ta ba gizo yake mata tabbas yah Abdul take gani ya rike ma wata hannu bata dawo daga tunanin datake ba taga wani  sss ya bud'e gudar motar Umman tagani da Abban ta numfashin ta taji yana niyyar d'aukewa kwalkwalrta taji tana neman yamutsewa  da wani irin gudu ta nufeso "Abba na Umma na Yah Abdul.." yansanda ne suka tare Amal daga isa inda su Abba suke cire niqab d'in tayi "umma na Abba na nice Amal dinku yah Abdul daganan silalewa k'asa tayi umma da Abdul kuwa bansan wadda yariga isa inda Amal take ba "Umma Amal ce Basma kuka tasaka  ganin mahaifiyar ta kwance "ummi kitaci yince zamuce gun uncle Abdul da ummanki  da Abbanki, Abbi yadaina dukan mu.."  Abdul kallon Basma yayi rungumeta jikinsa yayi "Daughter Umminki tana tare ummanta da uncle Abdul kinji." Umma mutafi asibiti don ceton rayuwar Amal please."..Umma k'asa aikata komai tayi Abba kuwa duk dauriyar sa saiga hawaye na shatata A fuskar sa   handkicif yafiddo yafara share hawayen sa Salma itama Kuka tasaka Abdul d'aukar Amal yayi tamkar jaririya ya nufi mota umma kuwa d'aukar Basma tayi ta nufi motar da  aka saka Amal ciki Abba shima mota ya shiga suka nufi asibiti,
tafiya kano weekend tafasu...

**

A hankali tafara bud'a idon ta drip sanye da ita  kallon cilin d'in d'akin  take ciki tayi wadda tagani ne kusa da ita yasata zata mik'ewa dasauri Abba,Umma, yah Abdul sai matar data gani Abdul ya riko hannun ta  "Ya Allah ya ubangiji kasa ba mafarki nake ba ya Allah kasa su ummana ne gabana." Umma fashewa tayi da kuka   tare matsowa ta rungume Amal "Amal ba mafarki kike ba mune gabanki kinji ko." Kuka tafashe dashi Umma kitaimakamin na mik'e."
"Aaaah Amal babu dadi jikin ki fa " Basma ruguwa ta nufo uwar "Ummi na"  ''Basma." Ummi na "wai wannan yace shine uncle Abdul." Amal kallon Abdul tayi ido hud'u sukayi dasauri Abdul ya d'auke idon sa Amal murmushi tayi tare shafar kan Basma " Ehmana Yau kukana yak'are basma kinji  ko."
Salma matsowa tayi kusada Amal.."kidaina kuka Amal yau kukan yayanki yakare Amal d'in sa tadawo Farin ciki zakiyi da hamdala da ubangiji..cikin tsananin mamaki Abdul ya kalli Salma ta ina tasan Amal ta Ina tasan kukan shi yakare kuma Ina tasan hakan." Amal kallon Salma tayi wata k'aunar Taji ta kamata kallon Abdul tasakeyi taga idon shi baya k'anta "Abdul kuje gida kaga nauyi dake tare da Salma..kafin Abdul yayi magana Salma tamatso kusada Umma "aaah Umma inakusada Amal nidai ina farin cikin dawowar ta." "Babu inda zaki kwana kitafo mutafi gida akwai nurses din dazata cigaba da kula  da ita kafin goben Umma sai da safen ku zamutafi gida"..
dasauri Basma ta rugu "Uncle zan bika." Abdul Rik'e hannun basma yayi muje to Baby" Salma badon taso ba tabi bayan Abdul tayi musu bankwana Amal kuka tasa tasan tabbas! Abdul ya tsane ta yanzu bayason ganin ta.ganin shi da tayi yatada mata radadin son shi wadda ko Akan hasheem bataji hakan ba...Abba yanatsaye wadda haryanzu shima baima Amal magana ba..

MENENE MATSAYINA...Where stories live. Discover now