_______________________
_*MINENE MATSAYINA...*_© _Hafssatu Musa_
*Indon K'auye*_*NO...40*_
*After 10 Month's*
(Silar komai💔)Tsaye take gaban madubi a goga waccan a shafa waccen fuskar ta kad'ai zaka kalla kasan tana cikin farin ciki da Annunshuwa ma'adanar kaya ta bud'a tarasa wadda zata saka can ta jawo wani material orange mai yarfin stone doguwa riga ce fitde gown Amma bata matse mata jiki ba gammo tayi mata tulin gashin ta ta tura cikin kallabin data d'aura..wani mayafi Blue ta d'auko tasa Masha Allah tayi kyau sosai wayar tadauko ta d'auki kanta photo Murmushi tayi ''babu wadda zai fara ganin make up d'in tafiya school d'inan sai yayana ya Gani what apps ta shiga ta tura ma Abdul wadda saving da My Yah Abdul..gani tayi last seen din shi tunjiya wajen 9 da yasauka bayan sungama fira yace ta sauka hakanan bayason dadewar ta online d'i nan inbahaka zata daina what apps d'in...dama dakyar ya yarda ta bude shi tare da kafa mata sharudda ta Amince da hakan contact ta shiga ta danna mishi kira. ..
Kwance yake tunda yayi sallar Asuba bacci mai nauyi ya d'auke shi k'ara wayar yaji sama sama special ringtone d'in da yasamata yagane ko wacece ke kiran shi dasauri ya mik'e video call ta kirashi d'auka yayi
"Good morning ya Abdul.''
K'ara murza idon shi ya zubo mata mayattun idon shi wadda ke rikita yan Mata Amal dariya tasa ''Ya Abdul good morning fa nace maka baka Amsamin ba "Baby nakasa Amsa gaisuwar saboda kin rikita z...dasauri ya canza kalar xance nasa ''Amal Ina zaki ne kikayi wannan kwaliyyar kodon ki gwada ma brother d'inki ne?'' Cikin shagwba ta Fara magana mai rikita Abdul koda yaushe ''Ya Abdul ka manta yau Monday zanfara zuwa school..bai kamata ka manta bafa." Dariya yayi ''Amal duk wani Abu daya dangan ceki
ina matuqar bashi muhimmaci fiye da nawa Abun dake gabana..." Amal Murmushi tayi ''Yayana bantaba ganin wadda ke nuna ma kanwar shi kauna ba kamar yadda kake nunamin tsantsanar kulawa baka taba Bari nayi kuka Kanason kaga dariya kodayaushe ya Abdul.." Abdul Murmushi yanajin wata k'aunar Amal nakara shiga zuciyar shi .. ''Amal"
Kallon shi tayi ya tattaro gabaki d'aya natsuwar shi yabata tasan maganar daxasuyi babu wasa inhar yayi mata irin wannan kallon ''na'am yayana'' ''Inafatan kina rike da Alqawarin da kikayimin baxaki taba kula kowane namiji da sunan soyaya namijin da yayi daidai dake ya kusa bayyana Amal wadda zai baki farin ciki had'e da kulawa yanan zuwa gareki banyarda da kulawa wani namiji ba Abokiya ma sai wadda tayi daidai da irin tarbiyanki da mutunchi gidan mu Amal inhar nasameki da aikata ba daidai ba zanyi fushi dake'' yaya nayi maka Alkawarin hakan baxaka tab'a samu da hakan ba insha Allah"... Yauwa Baby na Amma kinsan bada wannann Dressing d'in zaki school kije gun Umma kice tabaki sakon danace duk ranan da zaki school tabaki ki kirani inki Amso." Tam yaya dasauri datse wayar ta zira takalmin ta ta nufi gun Umma A bisa dinning table ta iske su zumboro baki tayi ta nufi gun Abba ''Abba shine zakuyi Breakfast kaida Umma Allah sarki ya Abdul d'ina duk lokacin dayazo hutun school baya Breakfast sai ya jira nafito ko karfe nawa zankai ban farka ba.."
Umma dundun takaima Amal A baya sai na bar Mijina nawa baiyi Breakfast har lokacin da kika fito wannan sai kijira lokacin da Abdul d'in yadawo.." Umma ya Abdul yace kibani sakon da yace kibani ranan da zanfara zuwa school.."
''OK jeki b'angaren gwagoo kice mata tabani Ajiyar Abdul."
"Tam Umma"
D'aukar Apple tayi cikin wani Dan Basket ta nufi b'angaren gwagoo tunkafin ta shiga tafara doka Mata kira kakus gwagoos takwaras kina ina" Gwaggo shiru tayi ta kyale ta har ta shigo Amal rike kugu tayi tare da zumboro baki ''shine kinajin Ina kiranki kikayi shiru Kika kyaleni"..gwagoo kallon Amal tayi kawai tamaida kanta ta cigaba da shan kunun k'anwar ta da kosai dake gefen sai soyyayar doya Amal Kusada gwagoo taje ta zauna "Tsohuwa zansha kunun da kosai." Rankwanshi dataji tsakiyar kanta yasa bata ida fadar Abinda zata fada ba ''kincin gidanku Bilki..". "Kai gwaggo don Allah kidaina cemin Bilki tunda kinrama shikenan"
Dariya Gwagoo tayi ''Jikale na tsoka d'aya tamkar a miya Allah nuna min Aurenki da A. ." Dasauri gwagoo tayi shiru Amal kallon ta tayi ''Aure dawa kuma kika kasa ida fad'amin."
''Angon ki mana"
Murmushi Amal tayi tare da jawo cup ta zuba kunun kanwa ta dinga hadawa da soyayar doya suna fira da gwagoo wadda yawancin Firar duk na Abdul ne saida tayi Kat! Sannan ta kalli gwaggo ''Gwaggo Umma tace kibata sakon ya Abdul wadda tabaki Ajiya kinsan gwagoo yau zanfara zuwa school..."
YOU ARE READING
MENENE MATSAYINA...
Mystery / Thriller"Don ubanki wanki dana barmiki kimin shine kika kiyimin Kika zauna kika rungume wannan shegiyar d'iyar taki wallahi koki aje ta ko kuma yanzu jikin ki ya gayamiki nafada miki banza..." Fuskar jike da hawaye ta d'ago ta kalleshi cikin kyarmar murya t...