_______________________
_*MINENE MATSAYINA...*_© _Hafssatu Musa_
*Indon K'auye**NO...33*
''Ba'aja da Zuwairah d'iyar ladingo ba Asiri ba boka ba malam makirci na d'aya ya isa ya dunkule kaunar da kuke ji da ita,
Fatima suna shiga d'akin kwantar da kanta tayi jikin Aliyu tafara sharbar kuka rarrashin ta yafarayi ganin tayi yana niyyar ja musu bargo dasauri ta raba jikin ta dana shi ya ''Aliyu ka manta yanzu bani d'aya bace kayi k'ok'arin yin Adalci tsakanin mu don Allah katashi kaje gunta"..
''Babu inda zani ki kyaleni ." A'ahh yah Aliyu banason fushin ubangiji da na gwagoo ya hau kanka don Allah don Annabi katashi kaje gun matar ta inhar nabari kahadu da wannann fushin biyu tabbas ban maka Adalci ba kuma bankasance mai kaunar ka tsakani da Allah ba don Allah katashi kaje muje ma natayaka wanka kar kaje gun Amarya".. Toshe hanci tayi tana dariya Dariya shima yasaka ''kin raina ni ko Fatima nice ke wari?" rufan asiri ya Aliyu muje dai nayi maka wanka d'in '' toilet suka nufa ta tayashi wanka ta fashe mishi jiki ta turarika, fitowa sukayi zuwairah tana sauna tana kallo (lokacin sai gidan wane da wane keda kayan kallo)
Dasauri ta mik'e ta ''tundazu inan nakasa bacci inata jiranka."
Aliyu kauda fuska yayi tare da jan tsaki Fatyma murmushi tayi "gashinan Ai nakawo miki." Fatyma sumbatar Aliyu tayi ''Good night.'' Aliyu shima sumbatar ta yayi "innalillahi karuwanci za'ayi gabana..Fatima bata fahimci komai take nufi ba bankwana tayi ma Aliyu ta nufi d'akin ta Aliyu wata harara ya watsa ma Zuwairah ya nufi d'akin sa zuwairah cikin kwarkwasa tabi bayansa...____________________
*AFTER 2 MONTHS*Duk wani kissa da makircin zuwairah tayi Amma haryanzu hak'an ta bai cimma ruwan ba tsakanin Fatyma da Aliyu saidai takaima gwagoo ita kuma tahau sama ta zauna ta dinga yima Fatyma masifa Zuwairah ce y'ar so itace wadda zata Haifa Mata jikoki..
''Allah Inna har yanzu shiru kamar k'ara musu son juna ake baya tab'a ganin laifin ta ita kuma bata fushi ko kad'an duk Abinda nake Mata fa bata barin daina kulani fa"... Kallon ta tayi Haba zuwaira sai kace ba jinin ladingo ba kinsan lokaci dana d'auka inason na had'a jini da Bilki ko to duk wata hanyar da zamubi sai bin wallahi don mallakar dukiyar Aliyu kibani wani lokaci kadan wannan karon dole naje gun Boka gobe da nisa Amma kibani wani lokaci kamar musa gaggawa." angama Inna.'' Tafawa sukayi kamar wasu k'awaye..
∆∆∆∆
Fatyma ta matsaa ma Aliyu tanason zuwa Egypt kawai mafarkin Aunty jamila take kuma suna waya Amma kwata kwata ganin ta takeson yi , dole Aliyu yafara mata shirye shiryen tafiya ba tare zasu ba akwai aikin da ya tsayar dashi zuwairah tayi murna da tafiyar ta tasan kafin tadawo sunyi sunyi duk shirye shiryen su wataqila taki dawowar ma don tafi son hakan
*EGYPT*
Rike take da hannun ta gam tamkar za'a kwace mata ''Aunty jamila bakuyimin Adalci ba ku kyautamin Aunty jamila haka kika koma Allah sarki y'ar uwata Allah yabaki lapiya Aunty jamila meyasa ba'a kusanar dani ba"?
''Autar Ummi kiyi hakuri banason d'aga miki hankali ne shiyasa nace ma Ya fawwax kada ya sanar dake ban lapiya ne .."
Fatima haka ta rungume Y'ar uwar tamkar z'aa rabasu da juna inda Abinda kedamunta fiye da 4 year's Cancer din mahaifa inda data samu ciki sai ya zube ko kuma ta dinga wahala tana zubar da jini sai ancire cikin inda yanzu taci karfin ta
¶¶
______________
_*After 2weeks*_Fatima tana kusada y'ar uwar ta konan da nan bata matsawa duk ranan jikinta ya rikece ya Fawwax mijin Aunty jamila fatima haka zasu had'e sita kuka babu mai rarrashin wani domin sai Add'ua..
Rike take da hannun fatima ''ukhti nabar miki Abdul har Abada ga Abdullahi nan kice mahaifiyar shi dama can riko hannun wani k'aramin yaro tayi dazaiyi 8 year's "Abdullahi Daga yau Ummin Fatima itace Ummanka kada ka b'ata mata rai kaji kada kabari tayi kuka inka b'ata ma rai nima zanyi fushi dakai Abdul..Abbien Abdul kada kahana zahra Abdul nabarta shi har Abada kuyafemin..Fatyma rikon hannun Aunty jamila tayi cikin shashekar Kuka....
Follow me on wattapad
#vote
#comment
#share
YOU ARE READING
MENENE MATSAYINA...
Mystery / Thriller"Don ubanki wanki dana barmiki kimin shine kika kiyimin Kika zauna kika rungume wannan shegiyar d'iyar taki wallahi koki aje ta ko kuma yanzu jikin ki ya gayamiki nafada miki banza..." Fuskar jike da hawaye ta d'ago ta kalleshi cikin kyarmar murya t...