_______________________
_*MINENE MATSAYINA...*_© _Hafssatu Musa_
*Indon K'auye**NO..30*
_*Nagode da duk Add'oi'nku gareni Alhamdulillah na warware insha Allah da Amincewar mahallacina bazan kara muku delay din post ba har nagama muku Amma fa kusani comments dinku ne zaisan hakan Nagode da soyayya❤️*_
_*TUSHEN LABARIN.*._
_*MAFARIN KOMAI*..._Zaune take tayi tagumi sallama Ake batasan Anayi ba har saida ya zauna kusada ita Fateema! dasauri tadawo daga tunanin datafi tare da share hawayen fuskar ta "Sannu dawowa." Kallon ta yayi yadda take k'okarin d'auke damuwar daga fuskar ta."
"Lpy lau Alhamdulillah."
Mik'ewa tayi da Alamun wani Abu zata d'auko rik'o hannun ta yayi tare d'orata bisa jikinsa Fatyma meyasa kike k'okarin b'oye damuwar ki gareni ne Faty na meke damunki har nashigo bakisan nashigo ba?''
Kuka tasaka mishi tare da d'ora k'anta bisa k'irjin ta shafa bayanta yafarayi A hankali ta sigar rarrashi saida yaga tayi shiru sannan ''to fad'amin damuwar "Don Allah yah Aliyu kayi Aure ko munga yara na zarya a tsakar gidan ko Gwagoo taga jikokin ta.." Ture ta yayi daga jikin sa cikin tsananin fushi ya mik'e yabar tanan murmushi tayi kawai tare da mik'ewa tabishi cikin d'akin iske shi tayi kwance bisa gado ya dafe kanshi zama tayi kusadashi tare riko hannun shi cikin sanyi murya tafara magana ''yah Aliyu na kayi hakuri banfad'i hakan da wata manufa ba kayi hakuri don Allah karkayi fushi dani kayimin Afuwa kasan fatynka bazata iya jurar fushin ka katausaya ma marainiyar ka,"..Shiru yayi batare da yayi Mata magana ba tsawon d'an wani lokaci mik'ewa tayi zata bar gun riko ta yayi ta fad'a bisa jikinsa,
''Fatima kinsan nima ban iya fushi dake meyasa kikemin maganar da raina ke b'aci Kin manta haihuwa ta Allah ce yana bayarwa ga wadda ya so bana daga cikin mutanen da jahiltar rashin haihuwa,Haihuwa lokaci ne kamar yadda mutuwa, Aure keda lokaci karki manta komai *RUBUTTACCE* ne daga Allah kai bawa baka isa ka musaya Abinda Allah ya rubuta ba domin tun ran gini tun ran zane,"
''Kayi haquri maigidana baxan sake ba na fahimci maganar ka da nasihar ka taso muje kayi wanka Abinci yana jiranka.".. ''To Matata yar Aljanna Allah yayimiki Albarka"...____________________
"Aliyu wai mekaka d'aukeni baka d'auke ni uwa ba ko kafi d'aukar matar ka da muhimmaci akaina ko?''
"Gwago bahaka bane don Allah kiyi hakuri karkice haka."..''Tun yaushe nake fad'a maka inason ka k'ara Aure ne Ina buk'atar naga jikokina sun baibayeni Nima",
"Kiyi haq...".
"Dakata Aliyu banason jin komai daga gareka wallahi nabaka Wata daya inhar baka sake Aure ba zan zab'a maka duk wadda tayimin na fad'a maka kafara lissafi daga yau." Cikin fushi ta mik'e tabar gun..*Waye Aliyu?*
_______________Shi d'aya ne tal A wajen iyayensa Asalin su mutanen Adamawa ne kasuwanci ne yadawo da mahaifin sa Kano ta Dabo _*Center of commerce*_ Mahaifin Aliyu yanada dukiya sosai inda baisan yawan ta inda shima ya gajeta gun mahaifinsa Mahaifin Aliyu mutum ne Mai taimakon gajiyayu a kodayaushe nadaga cikin Aliyu ya had'a karatun sa dinsa A kasar England A fanni kasuwanci inda acan ya hadu da matar sa Fatyma inda Asalin ta balarabiya ce yar k'asar Egypt ce Fatyma marainiya ce inda tarasa iyayenta duka sanadiyar wani had'arin jirgin sama su 3 wajen mahaifan su namiji daya Mata Biyu, Fawwaz, Jameela, Fatyma,inda takoma gidan yayanta da zama dama lokacin ta kamallah secondry school d'in ta ta nemi yayanta yakaita England ta cigaba da karatu, bada jimawa ya neman ta Lokacin dataje Aliyu yana Last year ne A hakan har soyyaya mai matukar k'arfi ta shiga tsakanin su mutane da yawa a school yadda Fatyma take soyayya da Aliyu y'an uwan ta larabawa da turawan babu wadda bai nuna Mata soyayya ba Amma taki Amincewa,
Sunyi ma junan su Alqawarin Aure bayan Aliyu yadawo gida Nigeria,__________
An sha fama matuqa kafin famliyn din fatyma da wasu daga cikin dangin su kafin Amincewa da Auren su inda Aliyu ya dan zauna England saboda karatun fatyma inda shima yake yafara had'a masters d'in sa bayan Fatyma ta kamallah karatun ta Aliyu ya had'a Masters dinsa yafara k'okarin dawaowa Nigeria saboda mahaifinshi daya takura mishi yadawo Nigeria dakyar Fawwaz (Yayan Fateema) da Jameela (Sister dinta) suka Amince da tafowar ta Nigeria, da sunce saidai ya rabu da ita ansha fama sannan da sharadi duk bayan wata 2 zataxo gida Aliyu ya Amince Fatyma ta tafo cikin Kuka da kewar y'an uwan ta wadda take musu kallon mahaifanta,__________
Dawowar Aliyu Nigeria bada jimawa ba Mahaifin sa yarasu bayan ya mik'a mishi ragamar dukiyar sa duka inda ya kwanta yar gajeruwar rashin lapiya Allah yakarbi Abinda Gwagwo wadda sunanta Bilkusu taji mutuwar mijinta Amma ba yadda zatayi tabishi da Add'ua inda Aliyu yake jagoran duk Abinda mahaifin sa yabar mishi shima bai fasa taimaka talakawan ba, har zuwan lokacin Fatyma ko b'atan wata bata tabayi ba gwagwo tafarayima Aliyu magana ya dinga rarrashin ta inda yanzu ta yanke wannan hukuncin,...._*INAFATAN KUNA GANE INDA MUKA DOSA🥰*_
_*NEXT PAGE*..._
_*LOADING*.._ 😍
YOU ARE READING
MENENE MATSAYINA...
Mystery / Thriller"Don ubanki wanki dana barmiki kimin shine kika kiyimin Kika zauna kika rungume wannan shegiyar d'iyar taki wallahi koki aje ta ko kuma yanzu jikin ki ya gayamiki nafada miki banza..." Fuskar jike da hawaye ta d'ago ta kalleshi cikin kyarmar murya t...