__________________
_*MENENE MATSAYINA......*_
© _Hafssatu Musa_
*Indon Kauye**2020*
*January*Not Edited❌
*17/18*
Tsaye take kitchen itada wasu yan aiki ''don Allah Uwani ku tabbatar da antsara komai daidai bana son Asamu Matsala".
''Angama uwar d'akina yanzu komai zai kamallah."
''Yauwa Uwani Nagode"
Fita tayi daga kitchen d'in Fuskar ta daka kada kasan tana cikin farin ciki." Uwani ce ta kalli wadda suke tare ''wallahi Kande Hajiya salma tanada matuqar kirki tasan darajar d'an Adam bata raina mutum ko yayake tana bashi darajar shi"''Wannan haka yake Uwani Allah ya tabbatar da Alkhairi yabata Miji nagari." "Ameen Amen"
(Yabon halayyen salma suka dinga yi)Salma tana fitowa d'akin ta nufa toilet ta zarce kawai ta sillo wanka tafito ta tsaya gaba mirrow tana shiryawa tana cikin shafa powder Aka turo k'yauren d'akin Aka shigo ''Yauwa Mammy na don Allah ki zab'ar min kayan dazan saka."
Murmushi tayi ta ida isowa gun Mirrow d'in "Salma duk shirin tarbar Abdul d'in haka ake tayi."
Sunne Kai tayi.
Mammy, wadrope d'in tabud'a wata Atamfah ce mai golden had'e da mayafin ta d'auko mata
''Yanaga baki make up bane?"..
"Mammy kinsan make up d'in bata dameni na shafa powder & lips gloos kawai ya isheni."..
''Aaa salma In law d'in nawa zaizo sukutum kice bazaki make up ba nida kaina zan miki''
Mammy kit d'in kayan kwaliyar tajawo tafara shirya salma..💫💫💫💫
Tsaye yake gindin mirror ya shirya cikin wani green d'in boyel light ya d'ora hula wadda tayi too much da boyel d'in woww Masha Allah Abinda na furta kenan domin ba k'aramin kyawu Abdul yayi ba feshe jikin sa yayi da turarinka masu dadi da sanyin kamshi, tare d'aukar key d'in motar shi ya fito,
Cin Karo sukayi da Umma ''Aahhh cancand'i gayu, tubarukullah My son kagako yadda kayi kyawu."''Thanks Umma na"..
Kallon dinning table tayi
''Abdul kako ci Abinci?"
''Aaah Umma na sai nadawo zan ci."''Inkuma surukar tawa ta cika maka ciki shikenan''
Murmushi yayi wadda har gefen bakin sa ya lotsa (Dimple)"Umma na nidai da nadawo xanci Kayana"''Shikenan jirani nazo."
Umma d'aki ta komo bata jima ba tadawo d'auke da wata leda
''Amsa ka Kai Mata Ina gaishe ta,"''Tam Umma na sai nadawo."
Fita yayi inda Umma tabishi da kallo kwalla taji sun cika Mata ido k'ujera ta samu ta zauna tare da tallafe kuncin ta
''Ina Amal take wace irin Rayuwa Amal take ciki ne tabbas jikina Yana bani Amal ba tattare da kwanciyar hankali Allah sarki y'ata Allah yatsaremi ke A duk inda kike ya bayanna min ke y'ata kidawo gida"...Abdul yana fita ya Shiga mota sai unguwar su salma har ya iso gidansu (dayake yasan gidan nasu)Maigadi ya bud'e mishi ya shiga Salma dake tsaye bakin window taga shigowar shi sakin labulen tayi tare da Ajiyar numfashi tare kara kallon kanta ga madubi yadda mammyn ta ta tsara Mata kwalliya takara feshe jikin ta da turare sannan ta koma ta zauna..Abdul gun maigadi yaje suka gaisa komawa yayi cikin mota ya fiddo wayar shi ya danna number Salma,
Salma tana zaune taji wayar ta tana tsuwwa kamar bazata d'auka ba tasa hannu ta d'auka wadda tagani yana kiran ta ne yasata zaro ido *HUBBY* Abinda tayi save number Abdul dashi kenan.. dasauri ta d'aga,💧💧💧
Gudu kawai take batasan inda zata dosa wani daji ne mai duhu babu kowa a ciki sai kukan tsuntsaye datakeji da namun dawa cin karo tayi da wani taga taga tayi zata fad'a wata rijiya riko ta yayi dasauri tafad'o bisa kirjin sa maida Mata gashin da yabarbazu a fuskar ta yayi ''My Amal ina kika tafi kika barmu kullum cikin tunanin ki kinsan ko halin da kika samu My Babe.." D'agowa tayi razane jin muryar dabata tab'a tsammani ba gani tayi yayi wani haske kyawun shi ya k'ara fitowa runkukumeshi tayi ''yah Abdul My tom don Allah katafi dani gun Abba na da umma na na rokesu su yafeman Ya Abdul kayafeman kaima don Allah.." Riko hannun ta kawai yayi zasu tafi Basma taji daga bayan ta na kiranta itada yah Abdul d'in suka juya ''Amal wannan yarinyar fa?"
''Y'ata ce Yah Abdul."
Yanayin fuskar shi taga ya canza can kuma yayi murmushi nufar basma yayi ya bud'a hannu ta tafo gareshi wata ce tagani fuskar lullube da mayafi ta nufo gun Abdul ta riko hannun shi...Ruwan sanyi da taji jikinta yasa farkawa tare da Ambatar Yah Abdul da karfi...Yah Abdul!!!!!!!......*Wallahi typing No sauki😭 ko kadan😩*
*Comment*
&
*Share*#TEAM HASHEEM
#TEAM ABDUL
#TEAM AMAL
#TEAM SALMA
YOU ARE READING
MENENE MATSAYINA...
Mystery / Thriller"Don ubanki wanki dana barmiki kimin shine kika kiyimin Kika zauna kika rungume wannan shegiyar d'iyar taki wallahi koki aje ta ko kuma yanzu jikin ki ya gayamiki nafada miki banza..." Fuskar jike da hawaye ta d'ago ta kalleshi cikin kyarmar murya t...