_______________
_*MENENE MATSAYINA....*__Na_
_Hafssatu Musa💫_
_*Aunty hafsy💕*__Dedicated to my daughter Billy S Fari_💋
*9/10*
_Afuwan da rashin jina kwana biyu komai yayi daidai yanzu nagode💕_
Sanye take cikin wata bakar riga mai yarfin stone pink tayi rollig d'in da pink d'in veil fuskar ta ba wani make up sai lips Gloos dake ta kyalli a d'an madaidaicin bakin ta sai tashin kamshi take irin na mata masu aji da gayu, Knocking take Amma babu Alamun za'a bata ixinin shigowa harta hakura zata juya taji muryar sa can kasa yace "Yes."
Murmushi tayi kawai tare latsa wani Abu ta bud'a kyauren tashiga lumshe ido tayi saboda yadda k'amshi ya bugi hancin ta tana bud'a idon ta sukayi Ido biyu Gabanta ya fad'i saboda Idon shi ba k'aramin rikita yake ba basarwa tayi tare da nufar inda yake dafa table d'in tayi ''barka da Aiki Yallabai An bani izinin zama nazauna ne?"
Gyad'a mata kai yayiMurmushi tayi tazauna..
Shiru ya ratsa gun can tayi Ajiyar Numfashi tare da kallon sa ''Abdull meyasa baka tausayi na kasan yadda *CIWON SO*..(My book) yake da matuqar rad'ad'i A zuciya Please Abdull sai yaushe zaka sammin guri a zuciyan ka da martaba na da kunya na y'an mace Amma duk na kauda su saboda Azabar sonka dake Addabar zuciyata Abdull Kai kadai xuciya na keso nayi nayi na fidda ka raina Amma kullum kamar Ana k'aramin sonka da kaunar ka".. tashi tayi dasauri cikin kuka ta bud'a Office d'in tafita..Bin ta da kallo yayi har tafita tausayinta yaji d'ora kanshi yayi bisa table "Am sorry Maryam mace d'aya tal a duniyar na mallaka ma duk wata kauna bana kallon wata mace da sunan so face ita nagagara cire k'aunar ta araina kullum tunanin ta k'aramin yawa yake A zuciyana nasan k'aunar ta ne Ajalina dafe kirjin shi yayi dake mishi wani masifar ciwo nan da nan yafara tari sai kakin jini ta hancin sa idon sa ya juye daganan bai sake sanin kowace duniya yake ba..
"Hasheem" wani kallo ya watsa yana gyara rigar jikin sa Ina jinki minti 2 nabaki domin inada Abubuwa masu muhimmaci gareni''..
"Dama..dama ince yau kwana biyu babu kayan Abinci..".
Wani kallo yayi mata "Kina nufin kayan Abincin dasuke Wata 3 su suka k'are cikin wata d'aya to ba kud'in Banza gareni ba irin na ubanki da kuma wannan Banza d'an uwa naki.ko a fada miki ni b'arawon mahaifinki ne?"....
Dasauri ta miqe Fuskar nan ta tuni ta zubar hawaye "ya isheka Hasheem ya isheka duk wani cin mutunchi da zakayi ya tsaya wajena kada ka sake ka k'ara tab'anmi iyaye da Yah Abdul Adalilin ka Dalilin soyayar da farin cikin ka na guje kowa nawa A duniyar nan nayi nesa da kowa nawa Hasheem A sanadiyar ka Na guji masoyina d'an uwa na yayana mai kokarin faranta raina kodako shi nashi zai b'aci yayi ciwo saboda ni Am..."..marin daya d'auke dashi har sau 2 yaki bata damar cigaba da maganar da take..
"Ki k'aramin maganar wannan banza d'an uwa naki sai nayi k'asa k'asa dake meyasa kin san da hakan Kika zabi wani bayan shi waya san ma koyana biyo kinan har nan kuna kwartacin.."
''Wallahi Hasheem bazan yafe maka nagaji nagaji wallahi sai ka sakeni nakoma ga iyayena duk da ban San *MENENE MATSAYINA* gun su A yau sai ka sawwake min na tsane ka hasheem nayi kaico na ni Amal danayi lalube cikin duhu."
Fizge rigar shi yayi data rike tsaki yasaka tare da kallon ta ya fita yabar gidan kuka tasaka har ta nemi hawayen ta rasa..wani zazzabi ne ya rufe ta da wani irin ciwon Kai wata shakuwa tafarayi luuuu tayi tafadi bata sake sanin inda take ba Basma tasowa tayi ta hau jikin mahaifiyar ta tafara Kuka....
*Bayan Kwana biyu..*
''Abdul kana son kakara sakani cikin damuwa ko.?"
Hawaye ne suka zubo mata tashi yayi dakyar riko hannun ta yayi ’'don Allah Umma na karki kuka kimaida hawayen ki hawayenki Baban tashin hankali ne gareni Don Allah Umma na.."
"Meye silar tashin ciwon ka to?"
''Tunanin k'angaririyar yarinyar data Gagarin iyayenta ta zabi wani fiye daku.."... Dasauri suka maida fuskar su ga bakin k'ofar inda akayi maganar...
*Comment*
&
*Share*
YOU ARE READING
MENENE MATSAYINA...
Mystery / Thriller"Don ubanki wanki dana barmiki kimin shine kika kiyimin Kika zauna kika rungume wannan shegiyar d'iyar taki wallahi koki aje ta ko kuma yanzu jikin ki ya gayamiki nafada miki banza..." Fuskar jike da hawaye ta d'ago ta kalleshi cikin kyarmar murya t...