Hindatu Case🙄

1.7K 53 1
                                        

     Eid-Mubarak to all My fann🌝 inafata kowa yayi sallah Lafiya Allah ubangiji ya amsa Ibadunmu Ameen ya Allah👏

            

Dedicated to My Doughter Rahama and Mai-Dambu my Addalo also to this special people Darling Bagudo, Neesher my behen, Walidation, Dijat inuwa, Sis Real Shaxee and to My Pop Khaleesat Haydar and my Qawa Jikar Kulu Maryam Obam ana tare kema da Hafsat A Garkuwa duk inagaisheku sosai inayinku 💯

🅿️2

Tuni ta hau Keke Naphep ta nufi gida, cike da jin dadin gift din daya bata, ta san kuma dole account dinta zai cika zuwa anjima.

Tunda ta shigo layin tafara yatsine fuska. Dai-dai kofar gidan ta, tace da me keken ya tsaya, "nawa ne!"

Tafada tana yatsina fuska, Tana kokarin lalubo kudin, cikin yar handbag din nata.

"dari biyar zaki biya"

Dan zaro ido tayi tayi tana  kallon bayan shi.

"kuttt! lallai ma yau ake yinta, yanzu kai daga UTC zuwa malalin ne dari biyar? gaskiya bazan iya biya ba, in nama ka mutunci, shine inbaka dari".

Kallonta yayi me keken yana girgiza kai, "gaskiya hajiya kudin ki yafi haka gaskiya"

Tabe baki  tayi, ta wurga mai dari da hamsin ta juya abunta.

"hajiya! hajiya! Dan Allah Kitsaya, walh bazan karba dari da hamsin ba!"

Waigawa tayi ta kalleshi, "walh tallahi ban karama sisi kaji narantse maka"

Cike da mamaki yabi ta da kallo, gashi tasha hijab ga liqab ace tana haka, Amma ba mutunci! girgiza kai yayi cike da takaici "kije kyabani a can!".

Ko wai gashi batai ba tasa kai cikin gidan, bako sallama da mitar mai keken tashiga gidan.

yaran dake tsakar gidan ne suka nufuta da gudu "oyoyo Aunty!".

Sake hade fuska tayi sosai, kamar hadarin kaka.

"tab inma dan ledar hannuna kuke, to da baku bata lokacin kuba".

"A'a hannatu har kindawo!".

Wata mata wacce kana gani ta girma hindatu tafada sanda tafito daga part dinta, fuskarta dauke da murmushi.

"eh andawo maman shamsiyya!"

Ta bata amsa a takaici, dan bata son cigaba da zancen Sam. Amma a ranta cewa tayi "andawo din uwar sa ido! mtsw".

Ciro key din part dinta tayi ta bude tashige cikin falon nata. "mtsw mata sai shegen sa'idon tsiya,  Allah wadai da irin wannan jahilcin". Kozama bata yiba ta cilla jakarta kan kujerar, tare da hijab d liqab din, tana kokarin zama.

Wayarta ta shiga ringing ta jawo jakar tana yatsina fuska ta ciro, ganin sunan Ramzia yasa ta ja  dan tsaki tare da yatsina fuska "oh mayyar mata kinbi kin mamaye komai Amma sai takura mutum! mtsw".

Receive ta dannah lokacin da take kokarin kirkiro murmushi kan fuskar tata.

"hello bestyna ya akayi?"

"Lafiya kalau"

Dariya hindatu tayi me sauti kai kace tana gaban Ramzia. "Amarya ta Alh.Rasheed kina wuta fa ina angon naki?". Tana  dariya wanda zaka rantse ba komai ciki, Amma sam a ranta ba haka bane, bata da buri irin taji kawar tata cikin matsalar da za'ace itace gidan Rasheed ba Ramzia ba.

"Kai hindatu! ke dai baki gajiya da zolaya walh uhm Rasheed ya koma aiki?"

"mene!"

Tafada kamar da gaske abun yabata mamaki.

ALAKARMUWhere stories live. Discover now