Alakarmu yana OkadaBooks ga yan Whatsapp nakudine take note 300 kacal and inkana son VIP is 500👌Zaku iya ta wadan nan hanyoyin kamar haka;
Account no: 0007600004
Acc name: hafsat Isa saleh
Bank: Stanbicbank
Ga masu turo card MTN Ko Zain zallah please inka/kin biya kituran receipt ta wannan no din; 08036319148.Free page👇🏼
Take note and pay o free pages is ending soon pay and send your receipt tunda nabada no a sama account Ko card anyone thanks.🅿️10
"Rahama! Ramzia! Ramz!"
Shiru kallon juna hindatu da Samira sukai suna mamakin ace wai bata Jin duk ihun da suke mata " meke damunta sam batama san inakiranta ba".
" tabata to mana!"
Samira tafada cike da mamaki tana kallon hindtu wacce ke nazarin Ramzia dake jingine kamar ice jikin bishiyar Kai hannu tayi ta tabota.
"Wa..." firgigit Ramzia ta farfado daga duniyar tunani datai nisa ciki, kallonsu tayi tare da share zufan daya tsurfo mata a fuska.
" Lafiya kuwa meyake damunki?" Hindatu tafada tana kallon Ramzia dake sauke nannauyar ajiyar zuciya, tare da kokarin sassai ta kanta zuwa normal.
" lafiyata kalau"
Tafada tana kallonsu ganin yadda suka zuba mata idanu kamar suna son gano wani abu tattare da lamarin nata, sa mayafinta tayi ta kara gogo fuskarta tare da kakabo murmushin dole, still dai ita suke kallo da mamaki.
" nafada muku I am fine Walh muje!".
Bata jira amsarsu ba ta juya ta nufi hanyar cafe din, kallon juna sukai Samira ce ta fisgi hannun hindatu dake tsaye har wannan lokacin tana kallon Ramzia suka bi bayanta.
Tun kan su karasa budurwar data gani dazu da hindatu Ke daga musu hannu inda abunda Ramzia ta tsana bai wuce yadda Hindatu Ke mu'amala da mata irinsu Amal ba narasa kamun Kai ga iskancinsu a zahiri suke, tana nuna musu seat amma Ramzia tayi kememe kamar bata gani ba ta zauna kan wani.
" Ramzy muje can!"
Ganin yadda Ramzia ta harareta yasa taja kujerar gefenta ta zauna tare da ma budurwar alamu da tazo.
" ita Kuma Amal yaushe kuka fara magana?" Samira ta tambayeta tare da tsareta da idanu.
" ahto help me ask her tacika kwashe-kwashe niban ma san meya kaita hulda da Amal ba".
Murmushi hindatu tayi " dadina daku kunsan abu amma sai kuyita surutu, kuna ganin yarinyar nan kunsan ae ta hadu meye a ciki dan na dan.....".
" uhm nidai Ina fada miki kikiyaye kanki da wannan huldar kinki banda abunki me zakiyi da mace? Mtsw!" Ramzia tafada tare da dan Jan tsaki.
" ahto nima abun hindatu naban mamaki ga maza sannan ga mata Allah dai ya shiryeki Ke kam"
Murmushin takaici hindatu tayi dan iya kula ta kula da zantukan su sosai " look kowa yayi abunda yake so, infact Kuma ae duk munafurci Ke hanaku yi badan Allah ba ni kunga tafiya ta I don't think zan tsaya a ashiga next lecture dani gaskiya!".
Tashi tayi taja handbag dinta batare data sauraresu ba ta isa gun Amal dake mata wani shakiyayyen murmushi suka bar gun suna kallonsu.
" uhm kigaishe Su!" Samira tafada da karfi dan hindatun taji ta, tako yi Sa'a ta juyo ta harareta. Nan suka zauna sukai order din drink da snacks.
" sweetyna why kika bar friends dinki, and kamar Ramzia don't like you with me at all Ko?".
Amal tayi tambayar lokacin da suka nufi inda motarta take.
KAMU SEDANG MEMBACA
ALAKARMU
AcakKarki kashe! Tsura ma screen din wayar tayi tana kallo, ta rasa me Rayhan yake nufi da ita sam a rayuwarta. Send me you pic I wanna see that beautiful face of yours please?! " mtsw" Taja tsaki tare da kashe datar komawa tayi kan bed din ta kwanta t...