Chapter 3

1.2K 54 1
                                    

Eid-Mubarak to all My fann🌝 inafata kowa yayi sallah Lafiya Allah ubangiji ya amsa Ibadunmu Ameen ya Allah👏

'ALAKARMU' is not Free but zan sake wasu pages Free a Whatsapp #300 a OkadaBooks each page will have it's price ga masu using Okada Ko masu Sha'awa intacan Akwai yadda zaka biya ka download Page dinka.A biya ta wannan Account make sure to send receipt dan insaka group na readers dina ta wannan no Whatsapp;08036319148 or 08081092825 zaka iya turo card but I prepare bank but anyway dai #300 thanks 👏
ACC No:0007600004
ACC Name:Hafsat Isa Saleh
Bank:Stanbicbank.
Receipt na biya kar a manta nagode.

           Dedicated to Aysha Seyoji wannan Page nakine Qawata kiyi yadda kikeso.


🅿️03

"Rahmatu!"

Ammi takira sunan Ramzia da kanta ke kasa, yanzu su kadai ne suke zaune a karamun falon.

A hankali Ramzia ta iya amsa kiran Ammin tasu, sanin bakaramun abu bane zaisa Ammi ta nema ganin ta ita kadai harta baro gida batare da ta kirasu ba tazo.

"Rahama inaso karki boye mun damuwarki kifada mun kinajin dadin zama da dan uwanki!"

Tambayar sosai tazo ma Ramzia a bazata, shiru tayi batare da ta dago ba saboda rashin sanin amsar da zata bata.

"Ke! Karki kuskura kiboyemun wani abu inda matsala ki sanar dani".

Cikin sanyayyar muryarta Ramzia ta bude Baki " bakomai Ammi".

" kintabbatar bakomai? dan kinsan cikin ku banso naga daya yana cutuwar daya, dan haka indai yana miki wani abu kina takura kan tafiye-tafiyen nan nasa kifadamun!".

Girgiza kai Ramzia tayi "toshikenan my doughter na yarda tunda kince bakomai na yarda, Allah yamuku albarka"

"Ameen"

"but duk sanda ya miki abu don't hesitate kinji ko? Dan ke 'ya tace banso Ko kadan naganki cikin damuwa".

Sosai jikin Ramzia yakara sanyi sam tasan rashin jindadin dan Ammi bazai sa taji dadi ba, dakyar ta lalubo murmushi saboda kallon da Ammi Ke mata ta ce "to Ammi insha Allahu".

Sam a ran Ramzia Akwai damuwa, amma sam bata jin zata iya fitowa ta fada dan tasha fada ma mahaifiyarta complain din, Amma sam momynta taki yarda saboda yadda yarta keson 'yar tata da kuma yadda Rasheed yake dawainiya da gidan nasu.

Shirune ya ratsa falon ganin haka yasa Ammi katse shirun.

"kinyi shiru Rahama wai yaushe zaki koma school din? kinsan banson kina zama haka nan sam walh".

Murmushi Ramzia tayi "jibi zamu koma Insha Allahu".

"To Allah yakaimu gobe zan aiko akawo miki sako kinji, yanzu haka akwai kaya da aka shiga dasu kitchen Ki tabbatar kina sha da madara Kinji Ko dazu natura ma yan uwanki nasu, dan haka kul kukai wasa mazan zamani sai a hankali".

Sosai Ramzia taji kunya zancen Ammi, dan koyaushe ita ke basu ma ganin mata kuma wai harda ita surukarta, lamarin Ammi na matukar bata mamaki sosai.

" haba hajiya gunta kika zo kenan kinmanta dani".

Rasheed yafada lokacin daya shiga karamin falon da suke zaune dukansu dariya suka saka mishi.

"eh din gun diyata nazo dan tafika damuwa dani, kai yaushe nake saka a idona Abdul-Rasheed? Amma ita kam koyaushe bata gajiya da kirana da kuma duboni".

ALAKARMUحيث تعيش القصص. اكتشف الآن