ALAKAR HINDATU DA RASHEED

830 28 0
                                        


🅿️19

Yafito cikin makarantar ya hangota tsaye da wani guy suna magana sai dai baya iya ganin fuskarshi parking ya nema guri yayi da sauri, dan ganin Ko shine Haydar din, amma yana fitowa ya hango guy din ya shiga wata mota yata yar kan yayi yunkurin tsallakawa tuni yaja motar.

Murmushi hindatu sai dai me kamar ance kalla ta hangoshi tsaye jikin mota ya harde hannayensa yana kallonta, nan take annurin fuskarta da walwala ta dauke, tuni kirjinta ya shiga dukan uku-uku sunkui dakai tayi ta samu ta tsallako tana kokarin wuce sa taji ya kira sunanta.

" Hindatu!".

Da irin muryarsa data tsana a duniya saboda furgitata sosai wannan muryar tasa take. Cak ta tsaya jin baikara mata magana ba yasa tafara yunkurin daga kafarta daga gun.

" Maza get in!".

Waigowa tayi taga yamata alama da motar, tsura mishi idannunta tayi marasa gaskiya. " uhm...bro mu....nada Le...".

" I said get in!". Yafada da karfi har saida student dake gurin suka shiga kallonsu cike da mamaki.

Hindatu kamar wacce Kwai ya fashe mata a ciki tawuce ta shiga wasu mamaki suke Ko mijinta ne Ko wanta, ba abunda yafi ba kowa mamaki sai yadda hindatu Ke matukar tsoronsa kamar taga mala'ikan daukar rai.

Tana shiga ya maida sunglass dinsa yashiga motar yaja, kamar wanda zai tashi dama yake figarta cikin hindatu sosai yagama durar ruwa. Dan tun suna yara Rayhan bai wasa da ita sam yatsane ta Ko ALAKARTA da Ramzia bayason don dai Ramzia na nuna bakomai yasa yabarsu.

Tafiya yayi da ita mai mugun nisa kamar zasu bar gari sai da yatabbatar da inda bamai ganinsu yayi parking din motar.

Ajiyar zuciya hindatu ta sauke me nauyin gaske tare da runtse idannunta wanda shida kansa yana iya ji. Kallonta yayi lokacin daya gyara zamansa yadda zai dunga kallonta dakyau.

Bude idannunta tayi jin yayi shiru a hankali ta dago kanta ta kalleshi ganin yanayinsa yasa tayi saurin sunkuyar da kanta. " Please Rayhan let me! Mena maka zaka hanani lectures ka kawoni nan please". Tafada lokacin da take tattaro iya karfinta ta furta mishi cike da courage.

Murmushi Rayhan yayi ganin courage dinta, wanda hakan yabarta tsoro harta dago ta kalleshi.

" Wow! I am impressed, walh sosai saboda courage dinki na yaba wow I should clap for you right?!". Yakara she yana kallonta cikin yanayin barazana.

" So hindatu have the got Ko Ko bude dirty mouth dinki kimun irin wadan nan questions din after all the bad things dakike". Yafada yana nodding kansa cire glass din dake makale a face dinshi yayi.

Hindatu wacce jikinta yadauka tunanine barkatai a ranta kar dai yagama sanin halin da take ciki?shine tambayoyin da take jero makanta cike da tashin hankali.

Tsura mata ido yayi yana nazarinta ganin yadda hannunta Ke motsawa da jikinta, wani irin hadiyar miyau yagata tayi me wahala. Nodding kansa yayi cike da takaicinta.

" please Rayhan what....".

" Shut up!". Yafada da karfi kamar zai bugeta, tuni ta gama runtse idannunta wanda ba abunda take jira sai saukar mari.

Dariya yayi me sauti ganin yadda tayi Amma cikin idannunsa jawur suke ba alamun wasa ciki. " Hindatu!".

Takira sunanta da karfi " Na....am". Tafada jikinta na rawa.

ALAKARMUWhere stories live. Discover now