Heart touching

901 48 19
                                        

Dedicated to all my Fans inayinku sosai da sosai👌

🅿️16

" Momy wai ya kuka kare kan batun Ramzia ne?" Kanwar Ramzia Islam tafada tana kallon momynsu dake kishingide kan taburmar, tana fifita saboda zafi daya korota tsakar gida ba wuta.

Tabe baki Momy tayi " uhm! Kedai bari Islam saura kadan yaya yau ta tado mana zaune tsaye Allah yataimaka dai Alhaji ya kau da zancen.

"Ni Walh haryanzu ya Ramzia haushi take bani fa!" Tafada tare da jan dan gutun tsaki.

" kul Islam karna karajin wannan zancen ba kinki Walh, koma me tayi 'yar uwarkice banaso".

" Amma Momy ita sai yaushe zatai hankaline dan Allah? Duba da kiga tarin dukiyar da ya Rasheed ya tara amma ita duk ta tara hankalinta kan ya Rayhan wanda haryanzu kwakwaran aiki bashi dashi, sai dai komai a mishi Kuma ae ya Rasheed yafi shi hankali" kallonta momynsu tayi tare tabe baki.

" uhm nidai nariga nafada mata ta kama mijin ta dan wannan yaron ba lallai ya iya rike ta ba koda iyayen sun yarda anmaida auren kanshi".

"Ahto ni bama wannan ba Momy itafa ko kwaso kudi ba tayi amata abu kiduba ya habiba har gida take dashi abunta Kuma tare akai aurensu amma ita ya Ramzia hmm" takarashe tana girgiza kanta cike da takaici.

" hmm Rahama ai kaf cikin ku Walh ita daban ce ba wayau, wannan yaushe ma take zuwa gidan inta zo mintuna nawa take ta tafi, kullum ita gata nan ne Allah dai ya ganar da ita".

Tsaki Islam taja " Kuma fa kawar ta Hindatu ba haka take ba walh!" Murmushi Momy tayi.

" tabdi kya hada Hindatu da Ramzia banda abunki itafa wannan Rahama ajebo ce, ita da yaran Ammi basu da banbanci basu San tanadi da rayuwa ba, tunda komai gani suke su samu koni da yaya bakiga muna da banbanci ba".

Dariya Islam ta sheke dashi " kai Momy! Ammi baiwar Allah da kin motsa zata turo Ki amshe sai business dinki kike banajin tana da abubuwan da kika mallaka a yanzu".dariya momyn nasu tayi.

" uhm! Baku bar Ramzia ba bare Ammi, kedai Islam baki da kunya walh". Tahir dake saurarensu tun tuni yana matsa waya yafada yana kallonta.

" Momy kinjishi yo meye nafada badai-daiba!".

" Allah yakawo ranar da itama ya Ramziar zata san halin ku tunda a gabanta kuyita damuwa da ita da Ammi da kunga bata sa.....".

Jifar da Momy ta mishi da takalmi yasa ya tashi da gudu " ai gaskiya nafada meye Ammi bata mana ita da ya Rasheed da ya Ramzia amma ku wannan gaskiya ba yi bane" Yafada lokacin daya fice.

" Au ni kake fada ma irin wannan maganar Tahir?". Momy tafada yana jinta Sarai yafi ce abunsa.

" kinji mun da Ko Allah yakyauta". Tafada suka cigaba d hirar su daga nan har labarin makwaftansu suka dasa wannan na daga cikin halayen Momy da Ramzia sam bata sani ba tunda tun tana shekara uku tabar gidan intaje Kuma Momy da 'yan uwan banda kulawa ba abunda suke nuna mata har ta koma bata Ko kwana wani sa'in hakan yasa bata wani zauna dasu ta sansu ba.

1week later....
Falon banda hayaniyar su Aleena dake kallon cartoon baka jin komai, kamar su kadai ne a falon amma abunda zai baka mamaki tana zaune falon.

Sai dai gaba daya tayi zurfi cikin tunanin rashin ganin Rayhan tun randa yadawo dasu daga gidan Ammi bata Kara ganin shi ba sai jakarta daya bayar aka kawo mata.

ALAKARMUWhere stories live. Discover now