🅿️20A get me keke naphep din ya sauke ta, knocking tayi me gadin ya bude yayi mamakin ganinta ba'a mota ba. Tana shiga KB yataso " hajiya baki ki.....".
Kallon harabar gidan tayi ganin ba motarsa ta sauke ajiyar zuciya sam bata ji karshen zancen KB ba. Tayi Knocking kofar falon amma ga mamakinta Islam ce tazo ta bude mata kofar.
" oyoyo Aunty Ramzia!". Tafada lokacin da take hugging dinta, murmushin mamaki Ramzia tayi sai dai bangaren Islam harararta tayi ganin bata iya gani.
Dagota Ramzia tayi " Ke! Kece yau a gidan lallai za'ayi ruwa da kankara tab". Ganin yadda Islam Ke kalle-kalle yasa ta kalleta.
" Mekike lekawa?". Ramzia ta tambyeta lokacin da take waigawa itama.
" Bro mana!". Tabata amsa.
Gaban Ramzia ne yayi wani irin mugun faduwa. " bro Kuma! Wani bro kike magana?". Kallon Ramzia tayi sama da kasa irin na raini.
" wafa, inba Rayhan ba!." Da sauri Ramzia ta dago idannunta suka hada ido, ganin yadda Islam din ta kafeta da ido yasa tayi saurin tureta tashige ciki, wanda kana gani zaka fahimci rashin gaskiya.
Murmushi Islam tabi bayanta dashi tare da girgiza kanta.
" Mezai zo nan din yayi?". Rahama ta tambaya lokacin data Kara bakin dinning tana tsiyayar ruwa amma hannunta na rawa.
" ba tare kuka fita ba?!". Jug din hannunta ne ya subuce yayi kasa nan take ya fashe, tayi kasa da sauri jikinta na rawa.
" Naji ance jiya baki da lafiya a nan ya kwana". Juyowa Ramzia tayi tana kallonta a tsorace.
Hannun Islam harde take wadan nan zantukan, cikin kwanciyar hankali abunta. " Ouch!".
Ramzia tafada saboda yankewar da tayi. " Wayoo yi a hankali Aunty Ramzia!". Tafada lokacin data karasa gun.
" Lazima! Lazima! Maza zoki tattara gun nan!". Tafada tana kallon Ramzia data tashi tana kallonta, ganin irin kallon da Ramzia Kebinta dashi yasa tayi saurin shafa cikinta.
" wash! Walh Aunty yunwa nakeji gashi Abincin da bro yayi yakare". Takara she tana Kara tsura ma
Ramzia ido wacce hankalinta gaba daya yake son gushe mata." to meyasa baki girka ba da kika iso?". Tana fada tabar gun ta koma can kan kujerar ta zauna.
" yo ina natuna girki, walh sai yanzu naji yunwa but sis..". Shiru tayi tana kallon Ramzia, ganin bata tanka mata ba yasa ta nema gefe ta zauna.
" da kike ciwo jiya baki tunani ko zee ba sai Rayhan, and inda bai dawo bafa!". Tafada tana Kara tsura mata idanu.
" And ya kwana yana jinyarki kardai kice har yanzu ku....". Saukar marin da Ramzia ta sauke kan kumatun tabe yasa tayi saurin tashi a gigice rike da gun wanda saida wani duhu ya ziyarceta.
" Meyasa zaki maren?!".
" Na mare ki din Kuma kika Kuma furta abunda kika fada walh saina Kara miki". Ramzia na fada ta tashi a zuciya ta nufi hanyar hawa upstairs dinta cike da takaici da bacin rai dama Kuma tana da babbar damuwa a gabanta.
" Aw dan nafada miki gaskiya shine zaki mareni?!" Tafada da karfi wanda hakan yayi sanadiyar tsayuwar Ramzia cak, waccce Ke mamakin yadda kanwarta ta daga murya tana mata irin wannan zancen.

أنت تقرأ
ALAKARMU
عشوائيKarki kashe! Tsura ma screen din wayar tayi tana kallo, ta rasa me Rayhan yake nufi da ita sam a rayuwarta. Send me you pic I wanna see that beautiful face of yours please?! " mtsw" Taja tsaki tare da kashe datar komawa tayi kan bed din ta kwanta t...