Inason yadda kuke comments...👌 shine dama kwarin gwiwar marubuci so will love to dedicate this page top one's when it comes to comment...👏
Dedicated to👇🏼
Aunty zee
Falmata
Wamu Rukayya
Ummita
Jikar kulu saura ban manta kuba Kuma Ana tare 👌🅿️13
9am....
Motar su Ammi tayi parking cikin gidansu Ramzia, karar motar yasa yaran suka shiga tsalle suna murna." Ammi! Ammi! Ammi is here".
Kan Ramzia tace kobo sunyi waje da gudu, bin bayan su tayi amma saita ga sun shiga mota already.
" Ammi tace kidauko mayafi mutafi" zainab tafada lokacin data zuro kanta waje.
Da sauri Ramzia taje ta sako mayafinta tafito, inda tashiga mota driver yaja. Har wannan lokacin kirjin Ramzia bai daina bugu ba saboda matsanancin tsoro daya addabeta.
Basu tsaya Ko inaba sai taga su nufi Airport, duk da tadan tsorata amma ganin Ammi na dariya yasa hankalin ta ya kwanta tabbas yanzu ta fahimci Rayhan ne yadawo, nan wani sabon fargabar yasame ta yadda zata fuskan ceshi wannan yana faruwa duk sanda zasu hadu.
Haka har suka isa ciki inda musa driver yayi parking. Kb shima yayi perking murmushi Ammi tayi me sauti.
" Munzo now Aleena zata canki what we are here for" zainab tafada tana dariya.
Girgiza head dinta Aleena tayi " no Aunt zee please tell us!" Aaina tafada cikin shagwababbiyar muryarta.
" Oya muje!". Ammi tafada tana musu dariya sosai.
Ramzia ce a farkon gefen kofar hakan yasa tabude kofar jin Ammi tace su sauka nan bugin kirjinta ya Kara tsananin ninkuwa.
Kai hannu tayi ta bude caraf kuwa ta hangoshi tsaye suna facing din juna cikin shigarsa ta kana nan kaya daya saba formal blue shirt ce jikinsa, sai wandonsa cream colour abunka da farin mutum yayi matukar yin kyau, sai black sunglass dinsa dake manne idannunsa, rataye yake da dark jacket dinshi yayinda daya hannunsa ke cikin pocket dinshi, gefenshi Kuma trolley-sleeve bag dinshi ne me kyau da daukar ido.
Tunda suka hada ido ya tsinci kansa cikin wani irin tashin hankali, saboda bugun da zuciyar sa take kamar zata fito. Dukansu biyu kallon juna suke sun kasa dauke idannunsu ga junansu.
" is Uncle Rayhan! Yeeee! Please Momy kibude muje gunsa". Ihun yaran ya fargar da ita duniyar data lula gaba daya.
Ammi shiru tayi tana mamakin abunda yafaru girgiza kanta tayi, sai dai tafi Alakanta hakan da haduwar jini da shakuwarsu, da wannan ta cire tunanin.
Tuni twins suka isa inda yake inda suka cika shi da surutu da ife-ife "Rahama muje mana!".
" Na'am!". Tafada dan sam hankalinta baya kan su Ammi sam, hankalinta yatafi gun Rayhan dake wasa da yara gaba daya.
" muje"
Zainab ta maimaita mata dan tuni Ammi ta karasa gun " kai! Kai! Kuyi a hankali karku ballamun da". Dariya su duka sukai.
" Ammi yarana nefa sunjima basu ganni ba, let them enjoy".
" to me 'ya 'ya saika wuce muje, idan munje gida saiku karata". Tafada lokacin data riko hannun Aaina.

DU LIEST GERADE
ALAKARMU
SonstigesKarki kashe! Tsura ma screen din wayar tayi tana kallo, ta rasa me Rayhan yake nufi da ita sam a rayuwarta. Send me you pic I wanna see that beautiful face of yours please?! " mtsw" Taja tsaki tare da kashe datar komawa tayi kan bed din ta kwanta t...