39&40

4.1K 60 0
                                    

💗💗💗💗💗💗
SIRRI NE
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
(SEX STORY)

*STORY & WRITTEN*
*BY*
*AUNTY AYSHA J.B*


*Ki biya kafin ki ka/ karanta d'ari Biyu ne cakal , 200 ki tura katin MTN ta wanna number 08062068839 sai ka ki/ min screen shot ta WhatsApp number na 07061631956*

®🌁

*FARIN JINI WRITER'S ASSOCIATION..📚📚*
{{Ƙungiya Domin wayar da ƙan mata , Farin jini writer's domin ci gaban, Mata.}}

★{{F.J.W.A}}★📖🖊️

https://www.facebook.com/Fajin-jini-writers-association-109611777388680/

_DEDICATED TO _
*AYSHA A BAGUDO*


Page 39_40

...... Umar zaune shida mai martaba Yana Masa fad'a ganin yanda ya d'auki damuwa ya saka a ransa duk ya rame saboda magabatan sa sunje niman Aure suka tarar da har an saka Rana Nanda wata d'aya , Sosai Uncle ya shiga cikin damuwa ganin Haka yasa Mahaifiyarsa da suke Kira Ummi tace. "Ga yar k'anwata da take rik'o tasan Halinta ciki da bai tanada ladabi da biyayya shine take so ta had'asu da Umar badan ransa yaso ba ya Amince kasancewar shi ba yaro bane baya jayayya da babba Amma shi har ga Allah raundan sa yake so kuma Yana ji a jikinsa matarsa ce i'tama Wanda Ummi ta bashi ba laifi tana da k'yau Amma Rauda ta fita kasancewar Rauda fara ce sol i'ta Kuma Fatima bakace Amma bak'inta mai k'yau ne gata da Nutsuwa bata da haniya sai da Ummi ta nimi Amincewarta Sannna ta sanar da Mai'martaba shima yayi farinciki sosai Haka d'ai aka tsayar da Rana wata biyu masu Zuwa" yanzun ma mai'martaba ne ya kirasa yana sanar dashi an Sanya ranar bik'insa da Fatima dafe qirji Uncle yayi cikin sanyi murya yace.

"Baffa yanzun shik'enan na rasata Wlh ina matukar sonta bana so RAUDA tayi Aure inda za'a hulak'antata bana so ta Auri wanda zai Mata Gori" kasancewar ya sanar ma mahaifinsa komai babu abinda ya boye Masa game da Alakarsu da Rauda dafa kafad'ar shi sarki yayi Sannan yace. "Umar ka d'auki hak'an a matsayin kaddara sannan ka Mata Addu'a inshAllah zata Auri Wanda zai ga kimarta da mutumcinta da yardan Allah babu mai Mata Gori domin babu Wanda ya huce kaddara..." Maganarsa ne ya katse lokacin da Wayar Uncle yayi kara d'an murmushi yayi tare da Kallon Sarki shima kallonsa yake , shafa 'kansa yay yana d'an sunne K'ai kasa, sarki yace. "d'auka Mana " d'aukar Wayar yayi tare da sawa a H_free "Hello beby kinji ni shuru ko yi Hakuri kina Raina wani uzirine ya Sha min Kai" jin sheshshek'an kukanta ne yasa shi fad'in "Lafiya ,What Happen to You beby ..!?" A hankali tace. "Uncle Nah Faruquna muna cikin babban matsala yanzun shik'enan na rasa ka ... shik'enan bazamu Kara kasnace tare ba Anya Zan i'ya rayuwa ba tare da k'aiba Hasskena" Ajiyar zuciya ya sauk'e harda lumshe i'don shi da k'ansa yasan bazai i'ya hakurin rashinta ba Amma Babu yanda zaiyi Haka Allah ya kaddaramusu a hankali yace.

"Beby Mai KE faru ne ? Fad'amin ina ji kamar wani Abu ya faru yau tunda na tashi nake ji kamar kina cikin wani Hali plz .. tell me" kuka ta Kara fashewa dashi sai da tayi sosai shi kuwa Yana aikin rarrashi sai da taji yace. "Wlh Nima zan Miki Kuka in baki fad'amin ba Beby plz Stop crying kinji" shi ya ma manta da Sarki na Gurin, da kyar ta i'ya bud'ar bakinta tace . "Uncle Ina da Ciki..." A matukar firgice ya Mike tare da fad'in. "What !!!! Innalilahi wainnailaihi raji'un Allahumma ajirni fi musibati wa'aklifni khairan minha Astagfirullah ...." Abinda Sarki da Uncle suke maimaitawa Kenan.
"Kina lna yanzun ? "Ina Gida , "ok ki riƙe waya Zan zo yanzun plz Karki saka damuwa a ranki Zan zo yanzun" kallon a gogon d'akin Rabi'a tayi sannan tace. "Rauda dare yayi shida fa yaushe zaizo ..." Share hawayen fusk'anta tayi sannan tace. "Uncle ka Bari Gobe dare yayi Kuma kasan yanayin Garin ba'a cika Tafiyar dare b..." Katseta yayi cikin tsawa "Karki Kara cewa komai gani Zuwa" kashe Wayar yayi tare da cilli dashi dafe k'ansa yayi bai Ankara ba yaji Hawaye ya wanke masa Fuska, dafashi da yaji akayi ne ya juyo da sauri Ganin Sarki ne yasa ya fad'a jikinsa tare da fashewa da kuka.

*****
Rarrashi sa sosai Sarki yayi sannan yace. "Da ka bar Tafiyar Nan gobe Umar" d'agowa yayi tare da share hawayen fusk'ansa. "Baffa bazan i'ya ba kuka fa take yi nasan yanzun Haka Yaya Ummanta Suna cikin matsala nasan sunsha Gore a Gurin kishiyar ta (Mom) wayyo ya zanyi Wlh nayi nadamar wannan Alakar tamu yazanyi ne ya zamuyi da ciki kuma gaskiya ni bazan Bari a Zubar ba.." Sarki yace . "Hakuri zakayi ciki Kuma dole a zubar tunda Aure zatayi" Girgiza Masa kai Uncle ya shiga yi daga karshe ya tashi da sauri ya nufi kofar fita Sarki yace. "Umar... Tsaywa yay ba tare da ya juyoba "da kamar tafiyar Nan gobe".

"Gsakiya Baffa bazan i'ya ba kamin Addu'a kawai in banje ba bazan samu kwanciyar Hankali ba".

"Shik'enan kaje Ubangiji ya tsare ka Amma karka je Gidan su ka Bari Gobe".

Gyaɗa Masa K'ai Uncle yayi sannan ya fita motarsa ya nufa fad'awarsa na ganin Haka suka tunkaroshi dakatarda su yayi alamar baya bukatar kowa , motarsa yaja Aguje ya bar Gidan gudu na fitan hankali yake zuwaba a Kan titi kowa sai kauce Masa yake domin in har Basu kauce ba ta k'ansu zai bi.

Karfe Shida da rabi ya bar *Nassarawa lafia* Karfe 8:20pm sai gashi cikin Garin BENUE ganin dare yayi ne yasa ya nufi Gidansa badan ranshi yaso ba, sai da yayi wanka tare da yin Sallah sannan ya Kira ta a waya ya shiga rarrashin ta dan alokacin Zeey sun koma sai da ya tabbatar da hankalinta ya kwanta Sannan sukayi Sallama.

*Washe Gari*

_Tofa mai zai Faru Ga dai Uncle Umar yace. "Baza'a zubar Masa da Ciki ba, shin ya Maganar Aurenta da Munnir ya makowar Mom da Rafi'a duk dai KU kasance tare Dani .._

AYSHA J.B

SIRRI NEWhere stories live. Discover now