53&54

4.4K 60 0
                                    

*SIRRI NE*

_Ki  Biya Kafin ,ki /Ka karanta 200 ne Kacal👌🏻 MTN ta wannan Number 08062068839, Screen shot ta WhatsApp number Na 07061631956,_

53_54

Jikinta ne ya fasa rawa numfashin ta ya fara fita a hankali d'agowa yayi tare da kallonta wani d'an murmushi ya sake tare da rumgumeta ta tsam a jikinsa "Rauda mai yasa kike fad'amin Magana son ranki haba Matata uwar 'ya'ya na inna kaunar fa sosai" wani Ajiyar zuciya ta sauke kafin tace "niba uwar yaranka bane domin da uncle na kad'ai Zan haihu ka tashi min a jiki ni bana K'aunar ka,Kuma bazan ta'ba Sonka a raina ba" jikinsa yayi mugum mutuwa a Hankali ya zare jikinsa daga nata toilet ya shiga ya Kara yi wanka kafin ya fito ko inda take bai kalla ba , i'ta ma shareshi tayi sai da ta shirya cikin Kampala d'inki doguwar riga sosai d'inkin ya Mata k'yau Zama tayi bakin Gado tare da rafka tagumi yunwa take ji sosai katse Mata tunani yayi  "ki zo muje ki gaisa da Hajiya" mikewa tayi tare da d'aukar himar d'inta a bakin kofar d'akin Hajiya sukayi Sallama cikin yatsina da had'e Fuska ta Am'sa musu tana zaune Kanwar sa Sajida na gefe tana had'a Abinci a tre wani i'rin kallon tsana take aikawa Rauda dashi da sauri tayi kasa da k'anta durkusawa sukayi shi ya fara gaidata Baki na rawa Rauda tace "Am uhm Mama lna kwana...." Bata Gama rufe bakinta ba Hajiya saratu ta katseta cikin masifa "da ban kwana ba Zaki ganni Eyyy !! karki kara cemin mama domin ni ban haifi karuwa ba kuma bazan haifa ba, Dan Allah dubeta kamar na Allah har da saka Himar Bayan an Gama tambad'ewa harda tsaraban cikin Shege shine aka yiwa d'ana rufa rufa an barbad'eshi da asiri an Bata Mana sunan zuri'a"

da sauri sajida tace "haba  haba  hajiya  wannan cin  fuska  ne bai kamata  ki ringa faɗar maganar da ba  haka   bane..."
"dalla  rufemin baki  nayi dake ne  wlh sajida ki fita  hanyata " shuru sajida tayi kuka sosai rauda take da tasan cin mutumcin da zata zo ta tarar kenan wlh da bata zo ba, farouq ma ransa ya sosu  da maganar mahaifiyar tasa gabaɗaya yaji babu daɗi bai ankara ba yaji fitar mutum da gudu ɗogowar da zai  yi yaga Rauda ce har ta  nufi par ɗinsu  da sauri ya  mike jikinsa har  wani rawa yake yi zai  fita ƙenan yaji hajiya saratu ta  fashe  da kuka "shiƙenan sun gama min da kai  wato har wani rawar  jiki kake aƙan wannan karuwar wayyo"  runtsa ido yayi da karfi  ransa yayi matukar baci sosai  jawoshi tayi tare da faɗin "wlh bazan  yarda ba  sai ka kara  aure ka  auri budurwa sabuwa ka  buɗeta a ledarta Allah yasa ma  baka  kwanta da wannan shegiyar ba,  domin wlh in har ka mata  ciki sai na tsine maka albarka kuma sai ka biya ni nonona da kasha sai ka biyani rainon ka da  nayi..." wani irin juyi yayi sai gashi durkushe a gabanta kuka ya saka mata  "kiyi hakuri Hajiya dan Allah karki tsine min wayyo karki ce haka hajiya inna san matata wlh ko yaya take  inna kaunarta.

"bazan iya had'ata da kowa ba hajiya dan Allah kiyi hakuri ..." wani kallo ta watsa masa wanda yasa ya kasa karasa maganar sa "ai kuwa baka isa ba tunda ubanka ya nuna min nashi ikon dole nima kayi min  biyayya  in kuma  ba  haka  ba  wlh  sai  in tsitstsine  maka" kuka yake yana ronka ta ta janye  maganarta yana son  matarsa  Amma  sam  taki  kulashi  karshe ma  abinci ta  haɗa masa  tare  da tura masa  shi gaban  sa "maza  maza  cinye  duka  kafin  ran ka  ya  baci" da  sauri  ya jawo abincin  yana ci badan yana  jin daɗin sa  ba , hasali  ma  wani ɗacinsa  yake  ji sajida kuwa  ganin  bazata iya  jure wanan rashin  imanin  mahaifoyarta ba  yasa  ta  meƙe  ta shiga  ɗaki,  yana gama  cin abincin  ta  aikeshi kallonta  yayi tare  da faɗin "Hajiya dan Allah kiyi hakuri na duba matata bataci  komai  ba tun  jiya   gashi  azahar  ne  yanzun bari  in kai  mata  abinci..." wani zagi ta sake kafin tace "ni  kake  cewa  matar  ka to  bari kaji  ma na  faɗama  maka i'ta  da baiwa  basu da banbanci  abinci  kuma  baza  taci  ba ta  mutu  da  yunwar  tashi  ka tafi min  aike"  Allah sarki ji yayi  kamar  yayi ihu  dan tsananin tashin hankali gashi Alhj baya gari  bare  ya  takawa hajiya birki haka ta kasa  ta tare sai da taga  tashin motar sa sannan ta dawo  ta zauna  "haka kawai  duk an kanannaɗe min ɗa? duk ya susuce akan ta wlh  anyi kaɗan ke  kuma Yarinya sai kin ɗan ɗani kuɗar ki sai na azzabtar dake shegiya kawai"

tana shiga ɗakin ta zube  akan gado  tana  wani  irin kuka mai cin rai tayi kuka  sosai  ganin bai shigoba  abin ya sake bata  mata rai  gashi wani mugum yunwa take ji kichin ɗinsu kuma ba'a saita kayan girki ba da tayi, tayi kuka har  taji  babu daɗi  dafata taji  anyi da sauri  ta juyo sai ganin sajida tayi kawar da ƙanta tayi gefe a hankali sajida ta zauna tare da ajiye kayan abincin da ta ɗauko ba tare da sanin  hajiya  ba, cikin kwantar da  murya tace  matar Ya farouq dan Allah kiyi hakuri da abinda Hajiyar mu takimi plz kinji" girgiza mata kai rauda tayi tare da sakin murmushinkarfin hali "lahh wlh babu komai ƴar uwa" ta faɗi haka tare da share hawayen fuskanta

sosai sajida taji daɗin maganar ta kallonta tayi kafin tace "ni sunana SAJIDA nice Autar hajiya na kammala karatuna yanzun haka sakamakon jarabawata nake jira inna da saurayi har an karɓi kunɗin Aure na amma fa inna daɗa kara baki hakuri sai kinyi hakuri da mahaufiyar mu domin bata sonki hasali ma wata yarinyar familiy ɗinta take so Ya farouq ya aura sai kuma hakan bai faru ba yayana yana kaunarki sosai baki ga tashin hankalin daya shiga ba"

kallonta sosai rauda take a kalla sajida zata kai shekara ashirin amma yanayinta ya nuna bata da girman kai gashi tana da surutu sosai katse mata tunani tayi da faɗin "ga abinci kici nasan kina jin yunwa " Allah sarki da sauri rauda ta karɓa tare da faɗin "nagode sosai Sajida.." wani irin bankaɗo kofa akayi hajiya ne ta faɗo kamar daga sama karɓan plet ɗin hannun rauda tayi tare da watsa mata a binci a jikinta zafin da taji ne yasa ta sakin kara cikin faɗa hajiya ta fara magana "wlh ko ruwan gidan nan bazaki sha ba ke kuma" nuna sajida tayi kafin ta cigaba da faɗin "zan saba miki sajida ki  fita idona na rufe uban wa yace kin bata abinci ohh dan kinga na shiga Sallah ko ? to billahil azim bazata ci ba zo ki fita" da gudu sajida ta fita tana kuka kallon rauda dake kwance a kasa tayi dai dai saman kirjinta da ta watsa mata abincin rauda ta rike tana wani irin kuka mai cin rai "rufe min baki shegiya mai farar kafa tunda aka aurawa ɗana ke komai ya jagule masa gabaɗaya jarinsa ya tafi wlh zaki yi ladamar auren ɗana da kikai" fin cikota tayi tare da tunguɗata gurin da tulun kwanunuƙan wanke wanke suke "oya maza maza na baki minti biyar ki wanke min su in kuma ba haka ba saina kona wanan jemammiyar fisƙan taki da ruwan zafi" tana gama faɗar haka tayi hucewarta ,

da sauri Rauda ta nufi gurin jikinta na rawa sosai take jin tsoron matar haka ta kaɗa ruwan omo tana wanke kwanuka tana kuka, sajida dake tsaye jikin windo itama sai hawaye take wani mugum tausayin rauda ne ya kamata da sauri ta ɗauki waya ta shiga can kuriyar ɗaki ta kira wayar FAROUQ lokacin da ta kira yana hanyar dawowo tsayar motar yayi tare da ɗaukan kiran

"Hello yaya kana lna ne?"
da sauri yayi magana jin muryanta cikin damuwa "lafiya mai ya faru? ko wani abin hajiya ta sake yi" cikin inda inda tace "kazo in zaka zo ka tahowa Aunty rauda da abinci"

"what   !! abinci baki bata abinci bane?" kuka ta saka masa cikin daka tsawa yace "SAJIDA !! ba magana nake miki ba" murna na rawa ta kwashe komai ta sanar masa "innalillahi" kawai yake ta furtawa ko kashe wayar baiyi ba yaja motar a guje sai da ya siya mata abinci tare da abubuwa sosai kafin ya nufi gida.

tana gama wanke kwanuƙan ta nufi part ɗinsu da kyar ta iya jarasawa domin wani jiri dake ɗibanta ga shi sai ɗingisawa take domin kasanta zafi yake mata, a daddafe ta shiga ɗakin tare da cire rigan jikinta nan taga yanda nononta ya kunbura gashi ko motsi kaɗan tayi sai taji wani azababben zafi kuka ta saka tana cije laɓɓanta a waje a ajiye motarsa domin bai so hajiya tasan ya dawo cikin sanɗa ya shigo gidan Allah ya temake shi har ya shiga part ɗnsa bai ji motsin hajiya ba da sauri yayi sallama tare da rufe kofar daidai lokacin da ake kiran sallar magari ba, ganinta cikin wani hali ne yasa shi sakin leɗar hannunsa da sauri yayi ƙanta tare da kiran sunanta "RAUDA tashi maiya same mi" wani kuka ta saka masa ɗaukarta yayi tare da ɗaurata jikinsa "subahanalillah mai ya sameki?" ya karasa maganar tare da kallon nononta domin shi bai ɗauka hajiya zata aikata abin da sajida ta faɗa masa ba ashe gaskiya ne maganar rauda ce ta katse masa tunani "Dan Allah ka kaini gurin ummana na rokeka ka sauwake min wlh bazan iya zaman gidan nan ba kaji tausayi na karka illatama ummata ni kaji tausayin mahaifiyata ni kaɗai gareta gashi ana kokari kashe mata ni dan Allah mai sunan Uncle ka sake ni..." cikin rikicewa da tashin hankali ya fara magana kamar zaiyi kuka "dan Allah kiyi hakuri wlh bazan iya rabuwa dake ba mai kike so yanzun naji zan kaiki gurin umma" da kyar ta iya faɗin "yunwa nake ji"

tofa wata sabuwa inji ƴan caca 😟😟 Allah sarki RAUDA wlh kin banj tausayi sosai😢😢 ummul naseen mamana ta kaina duk naji korafin ku kuma wlh kun bani dariya barin ma maman Rauda ...😂😂 wai kaida sunan ɗanka amma sai ka ringa bashi RUƊA😜


AYSHA J.B


SIRRI NEWhere stories live. Discover now