💗💗💗💗💗💗
SIRRI NE
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
(SEX STORY)*STORY & WRITTEN*
*BY*
*AUNTY AYSHA J.B*
*Ki biya kafin ki ka/ karanta d'ari Biyu ne cakal , 200 ki tura katin MTN ta wanna number 08062068839 sai ka ki/ min screen shot ta WhatsApp number na 07061631956*
®🌁
*FARIN JINI WRITER'S ASSOCIATION..📚📚*
{{Ƙungiya Domin wayar da ƙan mata , Farin jini writer's domin ci gaban, Mata.}}★{{F.J.W.A}}★📖🖊️
https://www.facebook.com/Fajin-jini-writers-association-109611777388680/
_DEDICATED TO _
*AYSHA A BAGUDO*
Page 45_46
Fuska kwance da tsantsar farinciki Abbu ya shigo d'akin Hajiya Nan yaga umma harda Rauda duk Suna zaune rauda Kuma na danna wayarta maganar ummanta ne ya katse Mata tunani "a a Abbun rauda wannna murmushin fa" Kara fad'ad'a fusk'ansa da murmushi yayi kafin yayi gyaran murya Nan Hajiya ta Gyara zama i'tama tana murmushi kwashe komai yayi ya fad'a musu Karan fad'uwar abun da sukaji ne yasa su juyowa da sauri Rauda dake tsaye zai zubda hawaye take yi tsaban firgicewa ne yasa ta saki wayar ta batare da ta sani ba ganin Suna Kallonta yasa ta nufi hanyar fita da cikin k'akk'ausar murya Abbu yace "RAUDA zonan" a hankali ta juyo hawaye har d'iga yake a kasa durkusawa tayi a gabanshi tare da fashewa da kuka shuru d'akin yayi bakin komai sai sautin kuk'an Rauda matsowa umma tayi tare da rumgumeta "Kiyi shuru rauda Kiyi hakuri ki Mana biyayya a matsayin mu na mahaifanki Karki sani jin kunyar kishiya kinji plz mamana ki daina kuka Allah ya riga ya kaddara Uncle d'inki bashi ne Mijinki ba gashi shi ya barki Yana ta shirye shiryen Aurensa" kuk'an da Rauda ta saka ne yasa tayin shuru Tausayin ta sukaji sosai domin sun lura har yanzun Uncle Umar na Nan a ranta.
Sai da tayi kuka sosai Sannan tace "shik'enan na Amince" farinciki fal ransu sosai suka ringa sa Mata Albarka mikewa tayi tare da nufar part dinta tana shiga ta zube akan bed Nan ta shiga rera kuka ji take zuciyarta na Mata wani i'rin zafi duk da tasan Farouq d'in Amma Bata ta'ba jin d'igon kaunarsa a cikin zuciyarta ba har ummanta tayi Sallama ta shugo Bata San ta shugoba domin tayi nisa a duniyar kuk'an da take yi Zama tayi tare da fad'in "mamana kuk'an ya i'sa Haka Kiyi hakuri Allah ya Miki Albarka ubangiji ya Baki 'ya'yan da zasu share Miki hawaye kamar yanda Kika share nawa hawayen Allah ya sanyawa rayuwar Aurenki Albarka"Kuka ta Kara fashewa dashi cikin shesheka tace "Umma shik'enan yanzun na rabu da uncle shik'enan yanzun wani daban zan Aura ? wayyo zuciyata zafi take min ummana ya zanyi?" Sosai rauda ta Bata tausayi share Mata hawayen fusk'anta sannan tace "RAUDAH kiyi hakuri kinji ki cire shi a ranki yanzun ya riga da ya manta ma dake tunda gashi yanata shirye²n Aurensa kema ki ciresa a ranki.." katse ta Rauda tayi da sauri "a a umma uncle na yana Sona nima na sani Yana mugum kaunarta Nima Kuma inna Sansa kaunarsa a jinina yake nasan da kaunarsa zan mutu na hakura nakura badan bansan sa ba, sai dan nayi biyayya ga Iyaye na..."ta karasa maganar tare da saki wani marayan kuka,
rumgume ta umma tayi sosai Rauda ta Bata tausayi rarrashin ta tayi sosai sai da ta nutsu ta daina kuka sannan umma ta bar d'akin,
Yau dubban jama'a su shaida d'aurin Auren Rauda Kabeer da angonta Umar Faruq Sai'd Uncle na Gurin dan shi ya bada Auren ta in ka gansa sai ka tausaya masa fad'a sosai Abbun rauda ya Masa domin shima yaune d'aurin Auren sai Uncle Umar bai ce Masa kala ba saima sunkuyar da k'ansa kasa da yayi jan hannunsa Abbu yayi suka nufi part d'insa dake Gidan har suka karaso d'akin k'ansa na kasa d'ago sa Abbu yayi ganin yaki Magana Nan yaga hawaye a Kan fusk'ansa,
cikin rud'ewa Abbu yace "Umar lafiya?" Girgiza Masa kai Uncle yayi kafin ya fara Magana hawaye nabin fusk'ansa "Ina kaunarta sosai Amma ta haramta a gare ni Sonta a jinina yake bazan ta'ba daina jin kaunarta ba, har kasa ta rufe min i'do inna tsananin kaunarta sosai" rumgume Abbu yayi Yana kuka kamar karamin yaro sosai jikin Abbu yayi sanyi "Kayi hakuri umar ka d'auki hak'an a matsayin kaddara kaima ka rumgumi matar ka Fatima ka cire rauda a zuciyarka , gashi yanzun ka jawo Magana Sarki sai Kira yake Yana fad'a abin da kayi bai ji dad'in hak'an ba..." Katseshi Uncle yayi "uhm bazai ji dad'i ba k'an Nima nazo bada Auren 'yata kuma abar kaunata bazan ta'ba K'aunar wata 'ya mace bayan Rauda ba domin rauda soyayyarta daban ne a cikin zuciyata Ina sonta sosai Ya-ya" ya fad'i Haka hannunsa na bisa Kirjinsa har wani lumshe i'don yake Fita Abbu yayi Yana fad'i "jira ni"
Tun lokacin da aka tabbatar da an d'aura Mata Aure taji kanta ya Mata nauyi murna zatayi ko bak'in ciki wai yau i'tace matar Aure lokacin da ta tuna bada Uncle d'inta bane aka d'aura Mata auren k'anta ne yayi wani i'rin mugum sarawa, kuka ta sake da karfi tana birgimi kowa na Gurin sai da ya tausaya Mata kamata Shema'u tayi suka nufi d'akin umma dake damk'e da jama'a Nan kowa ya shiga tambaya "lafiya ..?" Babu wanda suka kula Haka suka nufi uwar d'aka inda suka tarar da umma zaune tana had'a wasu Kaya da sauri ta bar abinda take yi ta nufo Fu tare da furta ,
"Lafiya mai'yasa meta ?" Fad'awa jikinta Rauda tayi tana saki wani i'rin Kuka kuka take tamk'ar ranta zai fita Gabad'aya jikin Kawayen nata yayi sanyi alama umma ta musu da su fita Nan suka fice rarrashin duniyar Nan umma ta Mata akan tayi shuru amma inna rauda har wani shid'ewa take yi rumgume ta umma tayi tare da fashewa da kuka cak, Rauda ta tsaya da kukanta tana sauraron kuk'an mahaifiyarta abin da Bata ta'ba gani ba wai yau i'tace ta saka mahaifiyarta kuka ? Da sauri ta share Mata fusk'a harda sakin murmushin yake "ummana dan Allah Kiyi hakuri wlh na daina plz ki daina kuka kinji mamana" girgiza mata kai umma tayi kafin tace "Dole nayi kuka nasan kin bi zabin mu ne badan kina so ba, nasan kin Amince ne dan ki faranta ranmu nasan kina kuk'an bak'inciki ba Uncle d'inki Kika Aura na Rauda nagode Nagode sosai da Kika min biyayya Allah ya albarkaci rayuwar da zakiyi ubangiji ya Baki 'ya'ya nagari ,
"Allah ya dawwamar dake cikin farinciki kamar yanda Kika Sanya mu Kiyi hakuri Rauda ki yafe min bisa tilas Miki da nayi.." da sauri RAUDAH ta katseta "a a ummana ki daina bani hakuri Baki min komai ba uncle kuma na riga na cireshi a raina tunda nasan yanzun Haka yana tare da matars..." Wani kuka ne ya kwace Mata, Abbu dake tsaye Yana Kallonta Gabad'aya yarinyar tasa ta bashi tausayi sai yanzun yake ladamar kin bawa masoyinta i'ta matsowa yayi tare da fad'in. "Uncle d'inki yana kaunarki har yanzun Domi ya bar nasa Auren yayi tattaki har Zuwa nan ya bada Auren ki tabbas uncle d'inki mai K'aunar ki ne kaunar na gasken gaske taso muje kuyi ban kwana domin shima a yau zai koma"
Koda suka je d'aki Yana tsaye yanda Abbu ya barshi sai kallon agogen dake tsitsiyar hannunsa yake ga wayarsa dake ruri yaki ya d'auka sallamarsu ne ya katse masa tunani da sauri ya d'ago Nan i'danunsu suka sarke cikin na juna kallon junansu suke kamar wanda Basu ta'ba sanin juna ba har gabansa Abbu ya kaita tare da fad'in "Gata minti Goma na Baku kuyi Sallama ..." Daga Haka ya bar d'akin zuciyarsa Cike da tausayin su tana ganin fitarsa tayi kan Uncle tana sakin wani i'rin Kuka rumgumeta yayi kamar Wanda za'a kwace ta sosai take kuka d'agota yayi Yana share Mata hawayen fusk'anta, hancinta ya lakata tare da mike Mata 'yar manuniyar yatsarsa sai da ta kallesa sosai tana sakin wani i'rin lallausar murmushi sannan ta lakace Masa hancinsa i'tama yatsa ta Mika Masa Nan suka had'a yatsa shi ne ya fara furta "inna Tsantsar kaunarki Baby nah" hawaye ne ya sauka a k'an fusk'ansa a hankali ta matso sosai kamar zata Masa kiss bak'insu kad'an ya rage bai had'uba, "inna Mugum Kaunar ka inna tsananin Sonka Uncle nah" ta karasa maganar tana sakin wani i'rin Kuka makullin dake hannunsa Guda biyu ya Mika Mata d'ayar ya nuna tare da fad'in "gata Nan na Machin d'in da kikace kina so tun lokacin da na hanani hawa napep wannna kuma Na gidana dake gra Daman na Gina Mana ne Amma yanzun ya dawo mallaki ki Rauda sanki a jikina yake Haka Rabbi ya tsara Daman ke ba Matata bace Amma duk da Haka Rauda da Sanki zan koma ga mahaliccina......
_wayyo niiii Allah Sarki Soyayya har na tuna nawa masoyin🤪_
AYSHA J.B
YOU ARE READING
SIRRI NE
RomanceLabarin Sex labari mai tsuma zuciya tayi Biyayya duk da ba'ason ,ranta ba Amma daga karshe taga riban biyayya tayi farin ciki tana godiya ga Allah daya Bata i'kon yiwa iyayenta biyayya Gashi tana zaune cikin aminci da kwanciyar Hankali mijinta na ka...