59&60

3.8K 64 0
                                    

59_60

cikin tashin hankali ya matso gareta hannu ta d’aga Masa , “dakata karka yarda ka karaso!” cak ya tsaya zamewa tayi ta kwanta a Gado tare da fashewa da kuka “wlhy zamana a gidan ya kare ko ka sake ni kona tattara na koma gidan iyayena” ai baisan sanda ya fad’a gadon jikinsa na rawa yace “dan Allah Karki min Haka plz Karki barni bazan i’ya rayuwa babu ke ba. ..” wani i'rin kallo ta watsa masa kwace hannunta tayi cikin bacin rai ta bar gadon ji sukayi an banko kofa “Hayaniyar me nake ji?” ko kallonta rauda batai ba ganin duk sun Mata yasa tace “ba magana nake ba” a tak'aice yace “babu komai!” wani i'rin Kallo tabi rauda dashi kafin tayi kwafa ta fita shuru sukai babu wanda ya sake magana a cikinsu kitchen ta shiga a Gurin taci abincin da Sajida ta girka musu bayan kwana bakwai zaman doya da manja haka suke in ba shi ya Mata maganaba ko zai mutu bazata ce mishi kala ba tana kwance misalin k'arfi Tara tana saka wannna ta kwance wancen kanta na kallon saman celling “assalamu alaikum” bata d’ago ba amma ta Am'sa masa sallamar zama yayi bakin gadon tare da jawota jikinsa shuru ta masa tana jin yanda ya sunsunarta “lafiya?” tambayar da ta Masa kenan tana Gyara rigan daya ke kok'arin cirewa “ita ta kawo hak’an”. dan tsaki taja tana shirin sauka a jikinsa rai a bace ya kamota d’aga hannu yayi kamar zai mareta kome ya tuna sai ya barta rai a bace ya tureta ta fad’a saman gado..
Ledar daya shigo dashi ya Mika mata sai da ta kawad da kai gefe kafin ta karba nono ne ,wanda aka damashi da fura da sauri ta sauka ta nufi kitchen cup ta d'auko ta juye a ciki yana ganin shigarta ya saki d’an murmushi tun daga kitchen d'in ta shanye tana fitowa ta nufi gado tayi kwanciyar ta Bata ce masa kala ba , shima haka yaje yayi wanka ya kwanta Kusa da i’ta cikin zuciyarsa yana tunanin anya ya mata adalci inda ya zubar da cikin nan! tunda ta nuna Masa kiri kiri tana son abinda mai'yasa bazai barta dashi ba Haka yayita tunani har barci ya daukeshi can tsakiyar dare ta tashi jin wani i'rin murd’i da cikinta ya mata tun tana daurewa har ta kasa “Farouq!!” dakarfi ta Kira sunansa cikin barci yaji muryanta da sauri ya farka “rauda lafiya?” lumshe i'don tayi kafin tace “ka zubar min da ciki hankalin ka ya kwanta!! ka zabi sabawa ubangiji ka ko Farouq Ashe soyayyar da kake i'kirarin kana min kariyace ba gaskiya ba!! ashe...” wani kara ta saka tare da dafe mararta wani mugum tausayinta ne ya d'arsu a zuciyarsa danasani da ladama ne suka Masa dirar mikiya a zuciyarsa ganin halin da take ciki ne yasa shi mikewa tsaye yana tunanin wani taimako zai bata “karka yarda kace zaka kaini asibiti ka barni na mutu a yanzun nafi kaunar mutuwata fiye da komai” shuru yayi yana kallon yanda take murkususu kusan minti talatin kafin ta sauk'e wani ajiyar zuciya da kyar ta i'ya mikewa ta nufi toilet wanka tayi tare da wanke kayan duk cikin karfin hali take yi tana fitowa ana Kiran sallah ganin Yana Nan yanda ta barshi ne yasa taja dogon tsaki bai ji zafinta ba a wannan karon domin yasan shi mai laifi ne ya caccanci fiye da haka .
Zame zanin gadon tayi shima sai da ta wanke cikin gida ta nufa tayi sanya tana dawowo tayi sabon shinfid'a kwanciyarta tayi tana tunanin mafita “Farouq in ka gama tsayuwa sai ka nufi masallaci” ajiyar zuciya ya sauk'e haka ya nufi toilet wanka yayi tare da alwala Yana fita ta Kira Ummanta a waya “hello mamana da asubar fari inna fatan lafiya?” cikin dakiya tace “ummana...” sai kuma ta saka kuka “a a subahanalillah menene kuma?” da kyar ta i'ya daidaita kanta “ya zubar min da ciki” mikewa umma tayi tare da barin d'akin kar Abbu yaji domin hankalinsa ne zai tashi amma abinda Bata sani ba tun sanda suke Magana yana ji haka yabi bayanta ba tare da ta sani ba  “innalillahi wainnailahi raji'un Allahumma ajirni fi musibati wa'aklifni khairan minha Astagfirullah Astagfirullah RAUDA ba abinda zance Miki sai dai ki d'auki Wannan a matsayin kaddara kiyi Hakuri ki Kara hakuri Insha Allahu zaki ga riban biyayya...” da sauri Rauda ta katseta da “umma !! Hakuri! riban biyayya duk ba gashi Nan Inna gani ba! Uwarshi bata sona sannan shima ya zubar min da ciki shik'enan ni bazan ga d'ana a duniya ba...” karban wayar Abbu yayi cikin sanyin murya yace “ki Kara Hakuri Rauda karki yarda kuma kice zaki zo Nan ki zauna tare da Mijinki” Haka sukayi ta tausarta da kalamai masu dad'i a Haka har ta hakura badan taso ba suna Gama waya tace “Allah nagode maka rabbi ka bani i'kon yin biyayya a karo na biyu”
Tana kwance taji ance “ke tashi ki fito ki wanke min kaya” gabanta ne ya fad’i bata san lokacin da tace “Hajiya b..a.b..banida lafiya” wani tsawar da ta daka mata ne yasa ta sauko babu shiri har ta manta da wani ciwo haka ta nufo cikin Gida nan taga tulun wanki hawaye ne suka gangaro mata babu yanda zatayi haka ta fara wanki tana matsan kwalla ga wani ciwo da cikinta ke mata Sajida ta fito a d'aki da sauri tace “haba haba Hajiya gaskiya abinda kike bakya kyautawa mai yasa kullun bakya son ganin farincikin yarinyar nan gaskiya bai dace ba ki sauya hali..” wani mari Hajiya ta mata cikin bacin rai tace “kar in kara ji kiyi magana idan kuma ba Haka ba sainayi mugun saba miki fita ki bani guri  kuma karki kuskura kije kusa da i'ta”
daki Sajida ta koma tana tsaye jikin window sai kallon Rauda take tana share wayan fusk'anta..
Farouq ne ya shigo ganin rauda na shanya ya sashi tsayawa yana kallonta tunani yake Wannan kuma kayan waye bayan zanin gadon data wanke yasan Basu da wanki domin shi yake wanke kayanshi dana hajiya gudun Magana ma a toilet yake sai ya Bata ta fito ta shanya ... Matsowa yayi kusa da ita Nan ya ga kayan Hajiya jikinsa har wani tsuma yake tsaban bakin ciki da bacin rai “Rauda!” ko kallonsa batayi ba Haka ta karasa shanyan ta,koma taci gaba da wankinta karasowa yayi tare da saka hannunsa shima ya fara wankewa d’agowa tayi da jajjayen idunta “idan kana kaunar Allah ka cire hannunka in kuma so kake ka jamin wani magana to” hajiyace da karaso gurin cikin bacin rai tace “tashi a nan!” shuru yayi kamar bada shi take Magana ba juyowa tayi Gurin Rauda “wato kin kirashi ki nuna min kin gamadashi ko kai kuma zanci mutumcin ka in baka tsame hannunka a cikin nan ba” mikewa yayi cikin dacin zuciya yace “haba Hajiya gaskiya abin kike baki kyautawa Bata da lafiya fa” zaman dirshan Hajiya tayi a kasa wani ihu ta saka “umaru ni kake fad'awa magana akan wannan yar isk'an matar ka to wlh Bari na Kara jajjada maka karka kuskura ka ma wannan karuwan ciki aure zan maka in aura maka Yar mutunci kamila ba karuwa wanda tayi cikin shege ba abin takaici da bak'inciki ma kanin ubanta ne ya mata cikin wlh zanci mutuncinka in baka bar nan gurin ba wayyo an shanye min d’a” hankali a tashe yace “dan Allah Hajiya kiyi Hakuri” wani tsawa ta buga masa “tashi ka bari guri  kafin na kwashe maka Albarka”
d'aura hannunsa yayi akai Yana kallon Rauda dake kuka kasa kasa gurinta ya nufa kamar zai rumgumeta tsayawa yayi yana tunanin mafita hannunta kawai yaja suka nufi d'aki kulle kofar yayi da sauri Hajiya ta zo jikin kofar tana bugawa “wlh umaru ka bud'e kofar nan kafin na Saba maka ke kuma zaki gamu dani basai kinyi haka bane zai nuna kin mallakeshi saina kara mishi mata Nan da lokaci kad'an”

_aikin banza na d'auka yanzun Zaki Kara mishi matar ashe dai nan da lokaci kad'an ne kai Hajiya ki kiyaye mu fa😏😏kafin mu tada aljanu🤣_

Shuru Farouq yayi yana kallon Rauda dake kuka cire da mararta matsowa yayi gareta cikin tashin hankali yace “dan Allah kiyi Hakuri” da kyar ta mike ta nufi kitchen binta yayi cikin rawar murya yace “zan miki” wani mugum kallo ta Masa kafin tace “me?” gas d’in ya kunna kafin yace “abinci” tsaki taja “banso ka fita! Mahaifiyarka na kiranka plz ka barni mana dame zanji wlh a halin yanzun ko fuskanka bana kaunar gani” jiki a sanyayye yace “kiyi hakuri Rauda...” cikin tsawa tace “da akayi me kaga Malam ka barni fa” fita yayi ya zauna a kujewa ruwan zafi ta zuba cup sosai tasha ruwan domin kishi take ji tana Gama shan ruwan cikinta yayi wani i'rin murd’awa durkuwasa tayi kasa tana murkususu ganin jini ne yasa ta sakin ihu take numfashin ta ya tsaya cak da sauri ya nufi kitchen d’in gass d’in ya kashe tare da yin kanta “rauda! rauda!!” inna ko numfashi batayi d'aukarta yayi yana jijjigata da sauri ya nufi kofa da i'ta Yana bud'ewa ya ci karo da Hajiya har yanzun tana tsaye ko kallonta baiyi ba ya saka rauda a mota yana Shirin tada motar Hajiya ta bud'e murfin motar gefen da yake cikin bacin rai tace “karka kuskura ka fita in kuma ba Haka ba saina tsine maka Albarka gwara ta mutu kowa ya huta” da sauri ya kalleta sannan ya kalli rauda Kara kallon Hajiya yayi cikin tashin hankali yace “hajiya .....” katseshi tayi da “kar ka yarda ka musa min..........

*Aysha J.B*

SIRRI NEWhere stories live. Discover now