61&62

4.3K 71 3
                                    

61_62

Kamar ya d’aura hannu akai ya fasa ihu haka yake ji, kallon rauda dake cikin halin rayuwa ko mutuwa yayi ganin har yanzun tana sume ga jini sai bin jikinta yake, kara kallon Hajiya saratu, yai still itama kallonsa take “maganarki bata kan hanya hajiya! Zan kai matata asibiti a cetomin rayuwarta domin inna bukatarta a duniyata! Ina bukatarta kusa dani bazan iya barin ta cikin wannan yanayinba” da k'arfi ya figi motar Hajiya na qwala masa kira lna! ran maza ya baci tuni aka bude masa get ya cilla hancin motarsa asibiti dake kusa dasu ya nufa da i'ta cikin gaggawa aka tarbesu daki na musammam aka bata yaso ya bisu Amma sai nurse ta dakatar dashi ,tsayawa yayi yana kaiwa da komowa da sauri ya koma mota ya d'auki wayarsa Alhj ya kira ya kora masa halin da ake ciki kwantar masa da hankali mahaifinsa yai ta hanyar sanar masa yana nan zuwa nan da kwanaki ..
Bayan kwana biyu sai da rauda tayi kwana biyu kafin tasan inda kanta yake cikin wanan kwanakin ko lekota Hajiya batai ba, Sajida ke sintiri da rana misalin shabiyu ta fara bud'e idonta tun tana ganin dishi dishi har ta bud'e ldon tarr da sauri Farouq ya matso tare da kama lallausar hannunta “baby rauda sannu kin tashi yajikin ina yake miki ciwo mai kike so sannu” lokaci d'aya ya jero mata tambayar binsa kawai take da ido ganin yanda ya rame ya zabge sai uban hanci da idunuwa tubarkallah d'an murmushi ta sakar masa a hankali tace “bana bukatar komai sai ganin mahaifana farouq dan Allah ka saukwake....” bata karasa maganar ba taga ya sunkuyar da kansa kasa hawaye tagani yana d’iga akan tattausar hannunsa dake rike da nata cikin tsananin tashin hankali yace “ki dubi darajan ma'aiki manzon Allah kiyi hakuri ki daina abatan saki wlh bazan iya rayuwa batare dake ba ina kaunarki rauda! Ina tsantsar sonki ina bukatarki tare dani dan Allah karki barni” ya karasa maganar Yana langwa'bar da kansa .. ..

wani mugun tausayinsa ne ya kamata da sauri sajida ta bar d'akin tana mai tsananin tausayin yayanta , kwananta biyar aka sallamesu tattali tarairaya soyayya kauna kulawa duk farouq ta nuna mata ya dage sosai yana kula da ita bak'inciki kamar ya kashe Hajiya ganin ko fita baya yi, tayi masifa tayi fad'a har tagaji ganin ko sauraronta baiyi ba,

rauda kan ta kasa kwantar da hankalinta domin kullun cikin kuka da rokon Farouq ya saketa take shima sai dai ya samata kuka duk lokacin da ta bukaci haka haka suka kwashi wata guda zuwa wannna lokacin rauda ta warke rass Alhj ma ya dawo sosai Hajiya ta shiga taitayinta amma tana ganin Farouq da Alhj sun fita Nan zata shiga gallazawa rauda tare da saka ta aiki mai wahala rauda duk ta rame ta susuce bata cikin nutsuwarta yau tunda ta tashi take jin bacin rai gashi kanta na mata wani i'rin sarawa shi kansa Farouq yau shakkarta yake ji ganin yanda ta had'e rai bai ta'ba ganinta cikin wanan yanayin ba Haka yayi shirinsa matsowa yai gareta tana kwance sai jan tsaki take i'ta kad'ai d'agota yai tare da d'aura k'ansa saman Kirjinta bin nonuwanta yai da kiss tare da fad'in “baby rauda nayi missing d'inki sosai plz ki tausaya min ko kad’an nayi mana tunda kin warke ina bukatarki” wani i'rin Kallo ta watsa masa kamar zatayi magana sai tayi shuru ganin yanayin da take ciki ne ya sashi manna mata hot kiss a lips dinta kwantar da i'ta yai “ilove you har kullun kaunar ki na dad'e ,qaruwa   a cikin ,zuciyata inna sanki matata” kallonsa tayi kawai bare da tace masa komai ba.

Haka ya fita ya barta kwance fitarsa da kamar minti biyar saiga Hajiya ta banko kofar “shegiya fito kimin wanki, kin sami gado kin kwanta kamar gidan ubanki karuwar banza duk anbi an mallakemin d'a” mikewa Rauda tayi kanta a sunkuye suna tafiya hajiya na zungurar kanta sai zaginta take  ran rauda ne ya Kara baci aii bata san lokacin da ta juyo a fusace ta danki wiyar hajiya cikin wani i'rin murya take magana “mun tara ki yayi yawa yau kin kaimu bango ita baiwarki ce da Zaki ringa azabtar da ita? ko jakarki ce i'ta?!” jikin Hajiya ne ya fara wani i'rin rawa sai gwale idanuwa take.

saukan bulala ta faraji a jikinta fiyat fiyat ta rasa ta inna bulalar yake gashi har yanzun rauda rike take da wiyarta wani ihu hajiya ta kurma sajida dake barci ta tashi da sauri waje ta fito iya kakarinta tayi dan ta kwaci hajiya abin ya gagareta i'ta wlh Aljanun rauda sun birgeta sosai taji dadi kuma da suka mata haka da kyar makota suka kwaci hajiya ai da mugun gudu ta nufi daki ta kulle kanta sai ajiyar zuciya da shafa wiyarta take "ashe daman mayyace ban sani ba cabb da sauran aiki gabana dan wlh bazan bar mayya da d'ana ta cinye min shi ba" sajida ce ta kira farouq yana tsaka da aiki jin abinda ke faruwa ne yasashi bari aikin babu shiri ya dawo gida rauda ya tarar tsaye kik'am idanuwanta sai jujjuyawa suke kai kana ganinta kasan wannan ba ita kad'ai bace cikin fargaba da tashin hankali ya kama hannunta amma ko didin ko motsi batai ba yin duniyar nan yayi su shiga d'aki abin ya gagara Alhj ya kira ya shaida masa halin da ake ciki cikin gagggawa shima ya nufo gida nan ya kira limamin anguwar rukiya aka fara mata kafin malam ya kai aya daya sun sun kai biyar da kyar dai suka barta bayan sun jijjigata sosai domin buka kanta ta ringayi da bango tana wani irin murkususu sai nannadewa take kamar wata macijiya kai koni sai da na tausaya mata domin a wannan lokacin ko kai mara imani ,ne muddin kaga halin da rauda ke ciki sai ka tausaya mata..

SIRRI NEOnde histórias criam vida. Descubra agora