Wani irin zufa mai yawa yake sharcewa a ko wace kusurwa ta jikinsa. Tun tana 'yar ƙanƙanuwar ta yake ɗauke da buri a kanta, yake so ya biya buƙatarsa gareta dan cimma wata manufa ta shi guda ɗaya da yake rayuwa domin ta a doron ƙasar nan. Amma ko da yaushe ya yi yunƙurin cimma burinsa a kanta komai sai ya taɓarɓare masa. Shin hala bata san ta hanyarta kaɗai ce dukkanin burikansa za su cika ba? Shin hala bata san ita kaɗai ce shamaki ga dukkanin buƙatunsa ba? Har sai yaushe ne zai cika burinsa? Har sai yaushe ne zai samu biyan buƙatarsa? Shin har sai yaushe ne dukkanin mafalkansa za su zamo gaskiya? Kallonta ya yi a karo na farko da ya kunna wutar ɗakin. "Me ke tare dake ne da ke min katanga da buƙatuna Rumana?, Me ke tare dake ne?." Ya faɗa yana mai kafeta da manyan idanuwansa da suka zamo sak irin nata. Kasancewar ita ɗin kanta daga garesa aka sameta. Ku biyo ni dan jin cikakken wannan labari mai cike da sarkakikya iri iri. labari ne da zai iya taba zuciyar makaranci har ya iya fitar da kwalla a idanuwan mai rauni. zaku ji dadinsa zaku yi alfahari da shi zaku kuma soshi insha Allahu.
24 parts