🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃
*WATA ƘADDARA*
🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃
*Story*
*And*
*Written*
*By*
*Salma mas'ud nadabo*👑🖊️ *PEN WRITERS ASSOCIATION*🖊️
{'''we are here to educate our readers, alƙalami yafi takobi'''}
*WATTPAD*
*salmamasudnadabo*
https://t.me/joinchat/VeIADhya0PsbdP9QSD1MDg
*FREE PAGE*
*Page: 15*
*Wannan littafin na kuɗi ne for those of you da suke san karanta littafin complete zaku turo 300 kacal a account number na 2261453630 ummusalma mas'ud nadabo zenithbank sai kiyi/kayi screenshot na evidence of payment ki/ka turo ta number na ta WhatsApp 07063683025 sai nayi adding ɗinki/ɗinka a group ɗin da nake posting, zaki iya turo katin Mtn for those of you da basu da account*
.....Jingine jikin machine ɗinsa yake jefi-jefi ya duba tsadadan agogon dake ɗaure atsintsiyar hannunsa yana duba mutanan dake firfitowa daga tasha, fuskarsa washe da annuri, ɗago kan da zaiyi idanunsa sukayi tozali da HAKIM dake tsaye da jakar goye yana waige-waige yayi fes dashi cikin ƙanana kaya baki ɗaya ya sauya shima yayi haske, kuma dama fari ne sai dai RASHID duk ya fisu haske wadda shima ayanzu SHAHEED bai san ina yake ba, kuma dama ko tun can jini su yafi shaƙuwa da HAKIM kuma dama tare suka taso sukayi karatunsu primary da secondary, haka shima RASHID ɗin secondary sukayi tare a ƙafur daga nan suka zama abokai su duka uku,
Kyakyawan murmushi ne ya kwacewa SHAHEED dan ya gane HAKIM da sauri ya ƙarasa wajen HAKIM dake tsaye hannayensa zuɓe cikin aljihu SHAHEED ya ce, "HAKIM..! cikin tsananin farin ciki faɗaɗa murmushi HAKIM yayi ya ce, "SHAHEED kai ka koma haka.? HAKIM ya faɗa yana waro ido ganin yarda SHAHEED yayi fresh ya goge daka gansa kaga ɗan masu maiƙo, ɗan ware hannu SHAHEED yayi ya ce, "ni ne naka SHAHEED"
"Oh my goodness haka ka zama ka ganka kuwa wayyo Allah na" HAKIM ya faɗa ya kai masa mugun hug shima SHAHEED ƙanƙamesa yayi ya ce, "kai ma baki ɗaya ka sauya HAKIM kayi fresh da kai" sakin juna sukayi HIKAM na cewa, "wane ni wai ka ganka ne yarda ka zama SHAHEED wallahi ka ƙaro wulaƙanci fiye dani" yar dariya SHAHEED yayi ya ce, "kai fa baka rabo da tsokana, toh yanzu ya nigeria.?
"hmm nageria nanan lafiya lau sai dai bata mun daɗi ko kaɗan saboda babu kai"
"karka wani damu nima wata rana zan dawo amma ba yanzu ba sai na saita rayuwata tukun"
"da kyau abokina gara ka dawo zama ni kaɗai babu daɗi toh ya su Umma.?
"Duk suna lafiya lau, yanzu dai mu ƙarasa wajen abun hawana"
"Toh." HAKIM ya faɗa SHAHEED na amsar jakarsa dake goye ya aje gaban machine HAKIM na baya suka ɗau hanyar gida.
Daga ɗakin SHAHEED HANIFA ta fito bayan ta gaji da zaman jiransa, ta koma ɗakinsa amma sai taga wayam alamar ya fice daga gidan, duk da irin dibara da Umma ke mata amma saida ta koma ɗakinsa domin kiransa, fuskarta a kumbure ta fito daga ɗakin tak take jira ta fashe da kuka ta nufi wajen Umma dake zaune tana gyaran zogale tana kallon shirin da ake a tv, saman cinyar Umma HANIFA ta kifa kanta tare da fashewa da kuka ta ce, "Umma kinga Hamma na SHAHEED ya bar mun gashina babu gyara Umma yamun wayau ya fita" HANIFA ta faɗa tana ƙara fashewa da kuka harda jan majina Umma ta ce, "ya isa mana, me na kuka duk dare ya dawo sai ya gyara maki gashin ki"
"amma Umma shi yace na jirasa fa, kuma shine ya gudu ya barni" HANIFA ta faɗa tana kuma sakin kuka kanta na kife saman cinyar Umma tana shafa kanta ta ce, "toh kiyi haƙuri mana ke ma sanin kanki ne dole ya gyara maki, ko mun dare kuwa"
"ai ni yanzu nake so Umma"
"Toh ɗauko mun kit ɗin na gyara maki da kaina, tunda yanzu kike so" ɗage kaffaɗa HANIFA tayi ta ce, "naki da zafi ai ni kuma bana son zafi"
"aiko zama ya ganki kuwa" kuka HANIFA ta kuma zaki jin furucin Umma NABIL da shigowarsa gidan kenan sanye cikin kayan ball ya ce, "Lafiya kika cika mana gida da kuka.? ɗago kanta HANIFA tayi cikin shashekar kuka ta ce, "ba Hamma na SHAHEED bane." taɓe baki NABIL yayi ya ce, "kunfi kusa ni bana shiga irin wannan fitinar, ki cigaba da kukan ki har ya dawo" Umma dake zaune takalmi ta rarumo zata wurga masa yayi ɗaki da sauri Umma ta ce, "Babban kawai maimakon ka lallasheta shine kake ƙara ɗaurata hanya ta cigaba da kuka" zaunar da ita Umma tayi sosai saman cinyarta tana cewa, "ya isa haka kukan, shi kuma Hamma zaizo ya sameni duk ma inda ya tafi" kuka HANIFA kawai take tana jan majina.
Tunda SHAHEED ya faka machine ɗinsa compound yake jiyo kukan BABY sama-sama parlour suka nufa a tare shi da HAKIM da sallama suka shigo baki ɗayan su, BABY dake jikin Umma tana sana'ar kuka ta ɗago manyan idanunta ta kalli SHAHEED tare da sakin kuka, ta miƙe daga jikin Umma zata wuce ɗakin Umma da saurinta SHAHEED ya damƙota yana cewa, "Haba BABY me yayi zafi haka nine fa SHAHEED na HANIFA" turo baki HANIFA tayi tana cewa, "ba kai bane ka tafi ka barni ba Hamma, kuma baka gyara mun gashi na ba" HANIFA ta faɗa tana son fashewa da kuka SHAHEED ya ce, "ai yanzu gani kuma yanzu zan gyara maki gashin ki maza share hawayen ki" SHAHEED ya faɗa yana ɗaukarta cak ya sanya hannu yana goge mata hawaye Umma ce ta kada baki ta ce, "o'o ni duniya ka shigo da baƙo ka barsa sororo tsaye, kana fama da wannan ja'ira mara haƙuri, ka ga samu waje ka zauna ka biyewa kallon waɗannan sai ka gantalle tsaye" Umma ta faɗawa HAKIM dake tsaye sororo cike da al'ajabi gami da mamakin yarinyar wato har yau tana nan da ƙulafucin SHAHEED duk da ta ƙara girma da wayau.
Gaishe da Umma HAKIM yayi cike da girmamawa, fuska washe Umman ke amsashi tana cewa, "yaka baro mutanan nigeria.?
"Lafiya lau Umma"
"Madallah ya kakar ka da jiki.? ina fatan jikin nata yayi sauƙi yanzu.? Umma ta faɗa kasancewar ta san kakar HAKIM sosai dan sau biyu tana zuwa gidanta lokacin suna gida, saboda SHAHEED dan kakar HAKIM akwai zuminci da son yara wani lokacin takan zo ma SHAHEED da kayan taɓawa, HAKIM da kansa ke ƙasa ya ce, "Allah yayi ma kaka rasuwa da jimawa tun barowar ku daga nigeria"
"Allahu akhbar, Allah ya jikanta da rahama HAKIM"
"Amin Amin Umma"
"to kai yanzu kana inane da zama.?
"Na koma can dangi Mamata kaduna"
"Toh madallah, Bari na kawo ma wani abun ka taɓa kafin abinci ya sauka ko" Umma ta faɗa tana miƙewa zuwa kitchen yayinda SHAHEED ya zauna yana facing HAKIM BABY na bisa cinyarsa sasauta murya HAKIM yayi ya ce, "SHAHEED karka faɗa mun yarinyar nan ce ta zama haka.? SHAHEED dake sakin murmushi ya ce, "uhm ita ce" washe baki HAKIM yayi ya ce, "masha Allah, itama tayi tsahon ƙafa" kallonsa SHAHEED ya maida kan BABY ahankali ya ce, "baki gaida Hamma HAKIM ba"
"ina wuni" HANIFA ta faɗa HAKIM ya amsata ataƙaice gami da miƙa mata hannu ya ce, "ya sunaki.? HANIFA dake zaune saman cinyar SHAHEED ta ce, "Sunana biyu ana ce mun HANIFA da BABY kuma ni HANIFA Hamma SHAHEED ce"
"inyee da kyau BABY Hamma SHAHEED" aje farantin da Umma tayi ne gaban HAKIM ya maida ahankalinsu kanta Umma ta ce, "ga wannan ka taɓa kafin abinci ya sauka ko," sannan Umma ta maida hankalinta kan HANIFA ta ce, "mu je BABY" saukowa BABY tayi daga jikin SHAHEED tana cewa, "Hamma na SHAHEED yaushe zaka gyara mun gashi na to.? ta faɗa bakinta gaba SHAHEED ya ce, "idan mun gama lunch sai na gyara maki okay" jinjina kai BABY tayi tabi bayan Umma.
After sun gama lunch ɗakin SHAHEED suka shiga suna zaune saman bed suna tattaunawa da HAKIM can SHAHEED ya ce, "ni kuwa HAKIM kana jin labarin RASHID.?
"Rabo na da RASHID since wata rana da muka haɗu dashi, yana shirin barin nigeria zai tafi america karatu, baki ɗaya yanzu behaviour ɗinsa sun canza ba kamar yarda muka sansa ada ba, am think ma RASHID ya cigaba da harkar fashin"
"Allah ya kyauta to, amma idan haka ne ban ji daɗi ba, so yanzu zaka huta ne kafin mu je kasuwa tare gobe"
"A'a ni babu wani gajiya jikina mu tafi amma first sai nayi bath"
"ok then akwai hita aciki, kawai fresh up zakayi before then nayi ma BABY gyaran gashi" ƴar dariya HAKIM ya saki yana cewa, "na lura dai BABY ba ƙaramun waje take samu wajen ka ba, ko dai da BABY nan za'ayi ne ka jira har ta girma" wani irin kallon SHAHEED ya watsa masa ya ce, "god for bit na auri ƴar cikina am sure lokacin da zatayi 18years ma nayi aure nama fara furfura wallahi, sometimes sai ku dinga magana kan abin da bai taba faruwa ma, yama za'ayi na auri BABY taya zanyi facing ɗinta as husband you are sick HAKIM" dariya HAKIM ya saki ya ce, "magani dai, ni dai miƙo mun towel nayi bath" drawer SHAHEED ya buɗe ya ɗauko masa new towel white ya miƙa masa ya shige bathroom shi kuma ya fita zuwa bedroom ɗin Umma .
Kwance saman bed ya hango BABY tana busy karatun ta na islamiyya dan BABY akwai ƙoƙarin maida hankali kan karatu, ɗan yatsun ƙafarta ya ja ya ce, "BABY.! ɗagowa tayi ta ce, "hamma dama kai nake jira na ɗauko kit ɗin.?
"Yes ɗauko" sakowa tayi daga saman gado ta nufi dressing mirror ta ɗauko kit ɗin ta dawo bakin bed ta zauna ƙasa, SHAHEED na saman gado kit ɗin SHAHEED ya buɗe ya ciro comb da maya-mayanta na gyara gashi ya fara gyara ma kamar mace, sosai yasan sirrin gyara gashin kan BABY yana binta ahankali dan ya lura sam bata son zafi, shiyasa ko kitso bata son zuwa sai yayi fama da ita, sometimes da kuka take dawowa daga gidan kitso saboda ko kaɗan bata son ana ja mata gashi da ƙarfi ko yayane, idan ko SHAHEED ne ke mata gyaran gashi har bacci tanayi sai ya gama tsaf zai lura ta jima da bacci, har ya kamala gyara mata gashin yayi parking nasa ya fito masha Allah ya miƙa mata kit ɗin ya ce, "ungo maida" amsa tayi ta maida tana cewa, "na goda Hamma na" ja mata karan hanci SHAHEED yayi ya ce, "my rigimarmar BABY" washe baki tayi tana dariya kana SHAHEED ya fice daga bedroom ɗin.
Tsaye gaban dressing mirror SHAHEED ya samu HAKIM har ya fito daga bath SHAHEED ya ce, "har ka fito kamar kayi jiƙa-jiƙa" harara HAKIM ya cila masa ya ce, "dayake kowa irin ka ne mai jimawa a toilet kamar zai canza skin"
"naji ba komai amma ai ina tsayawa na fita"
"kuma hakan bai sa ka fini haske ba ko" HAKIM ya faɗa yana sakin dariya yayinda yake shafa lotion ya ce, "kana jin daɗin ka mutumina komai naka in classy way" waigowa HAKIM yayi sosai ya ce, "baka faɗa mun yarda kukayi da Umma ba bayan ta warke"
"hmm bazaka gane bane baki ɗaya zama makarancin dole nayi, up to now Umma tana thanking ina aiki under wanine i never tell her ina da shago sai dai with time everything zaiyi setling, the only thing dake ɗaga mun hankali HAKIM duk sanda BABY tagane who i am to her, am scarad about this mess HAKIM, duk da ina ɓoye damuwana but deep down something is hurting me, bani da wanda zan faɗamawa damuwana sai kai HAKIM gashi kamun nisa sai yanzu dana samu chanse nake faɗa ma pain ɗina" dafa kaffaɗarsa HAKIM yayi ya ce, "insha Allah nothing bad will happen SHAHEED only god know dalilinsa na haɗa ka da wannan KADDARA, amma insha Allah babu abinda zai faru okay" jinjina kai SHAHEED yayi ya ce, "i hope so, tunda ka gama shiri mu je ko"
YOU ARE READING
WATA ƘADDARA
ActionKo wani bawa nada tasa zanan ƘADDARA sai dai shi tashi tasha banban data saura, komai ya farune daga ranar da mahaifiyarsa ta kwanta ciwo, ya buga ya nema domin sama mata kuɗin magani dana asibiti duk da yana matashin saurayi mai ƙarancin shekaru ɗa...