WATA ƘADDARA

67 2 0
                                    

🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃
                   *WATA ƘADDARA*
🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃
*Story*
      *And*
          *Written*
                  *By*
*Salma mas'ud nadabo*👑

🖊️ *PEN WRITERS ASSOCIATION*🖊️
{'''we are here to educate our readers, alƙalami yafi takobi'''}

       *WATTPAD*
*salmamasudnadabo*
         

https://t.me/joinchat/VeIADhya0PsbdP9QSD1MDg

   *FREE PAGE*

*Page: 16*

            *Wannan littafin na kuɗi ne for those of you da suke san karanta littafin complete zaku turo 300 kacal a account number na 2261453630 ummusalma mas'ud nadabo zenithbank sai kiyi/kayi screenshot na evidence of payment ki/ka turo ta number na ta WhatsApp 07063683025 sai nayi adding ɗinki/ɗinka a group ɗin da nake posting, zaki iya turo katin Mtn for those of you da basu da account*

        
       ....Zaune suke office ɗin doctor bayan ya duba idanun BABY sosai ya ce, "me kike ji cikin idanun ki.? BABY dake zaune saman cinyar SHAHEED ta ce, "yana mun susa, yana mun zafi a school ma wani lokacin bana ganin rubutu sosai, aunty ta dinga mun faɗa idan bana note, farin abu na kashe mun ido har ya sani kuka"
    "daga nan babu wani abu.?
    "Eh babu ko Hamma.? ƴar dariya DOCTOR yayi kasancewar asibitin da suka saba zuwa ne ya ce, "wato ciwon da kike ji shima Hamman naji kenan.? ɗaga kai tayi tana kallon SHAHEED dake kallonta tayi ƙasa da murya ta ce, "hamma kai ma kana jin ciwo zafi a ido kamar yarda nake ji.? ɗaga mata kai SHAHEED yayi ya ce, "ko me kike ji ina ji BABY" maganar doctor ya katse su yana cewa, "BABY na buƙatar a mata glass, yanzu zan bata magunguna sati me zuwa ku dawo sai mu bata glass ko" SHAHEED ya ce, "batayi yarinya da glass ba duka six years take, idan ta fara anfani da glass yanzu zai iya kashe mata ido nake gani,"
      "A'a insha Allah babu abinda zai faru zamu bata wanda zai taimaka mata ɓangaran karatu ne, idan takai wasu shekaru ciwon na iya tafiya ma, amma yanzu dai tana buƙatar glass amma kafin nan bari na maka wani gwaji ka gani" fara paper doctor ya ɗauka yayi rubutu bisa takaddar ba wasu mayan ba sosai kuma ba ƙanana ba normal rubutu ya ɗan jasa baya kaɗan ya ce, "BABY me na rubuta nan.? ƙurawa rubutun ido BABY tayi can kuma tayi ƙasa idanunta da sukayi raurau ta ce, "bana gani hamma da gaske zan makance Hamma.?  girgiza mata kai Hamma yayi ya ce, "nope bazaki makance ba" doctor ya ce, "ka gani bata ganin abu idan ya mata nisa amma yanzu bari na matso mata da rubutun" matso mata da shi doctor yayi ya ce, "me na rubuta.? washe baki BABY tayi ta ce, "HANIFA Hamma SHAHEED"
       "Good girl, ka gani yanzu ta gani tana ma ƙoƙari a wannan age ɗin nata ta fara iya karatu" jikin SHAHEED sanyi yayi ya ce, "toh shikenan a mata glass ɗin" magunguna doctor ya bada SHAHEED ya amsa suka taso daga office ɗin shida HAKIM da BABY suka dawo gida.
     
       A parlour suka samu Umma tana ganin shigowar su ta tashi zaune kasancewar kishingiɗe take ta ce, "ya kukayi da likitan.? SHAHEED dake jaye da hannun HANIFA ya zauna yana cewa, "doctor ya ce sai an mata glass saboda bata gani rubutu sosai"
    "o'o ni yarinya ƙarama da ita zata fara anfani da glass, wannan ciwo ya sakota gaba, zo nan BABY naga idanun ki" Umma ta faɗa tana miƙa mata hannuta kama Umma ta ce, "sannu BABY Allah ya yayemaki wannan ciwo" da "amin" suka amsa baki ɗaya.
     
             Satin HAKIM ɗaya NIGER ya fara shirye-shiryen komawa nigeria, baki ɗaya sai SHAHEED yake jin babu daɗi ya saba kwana biyu tare suke zuwa kasuwa da HAKIM tunda ya zo, kuma yana samun damar faɗa masa duk wasu matsolinsa wayanda ya kasa faɗa ma Umma musanman akan abinda suka aikata.
       Bedroom ya shigo hannunsa riƙe da takaddu ya samu HAKIM na loda kayansa cikin ƴar jakarsa ta goyo, sosai yake jin babu daɗi wanda har fuskarsa ta nuna hakan ya ce, "ga takadun nawa na makaranta baki ɗaya sai ka fara nema mun Admission kafin na zo" amsa HAKIM yayi ya ce, "toh madallah komai ya kamala" wasu ƴan kunnaye da sarƙa SHAHEED ya ɗauko ya ce, "ka amshi waɗan nan ka fara business dasu ka gani yaya kasuwancin zai tafi"
    "Na gode sosai SHAHEED Allah ya bar zuminci"
     "Amin amma ka adana godiyarka dan bana so" murmushi HAKIM yayi SHAHEED na taimaka masa da haɗa kayansa har suka kamala haɗa kayan suka kwanta daren yau ma sun sha hira kamar baza suyi bacci ba.
   
   
      Washe gari kuwa tunda safe HAKIM ya ɗau hanyar nigeria, sosai SHAHEED ya ji babu daɗi kamar HAKIM ɗin ya dawo nan niger da zama haka yake ji, tunda can nigeria ma shi kaɗai ke rayuwa, sai kuma kasuwancinsa da karatunsa ba zaiyuyu ya aje su ba, jikin babu ƙwari ya dawo gida asanyaye cike da kewar HAKIM, haka yinin ranar ya wuni suku-suku dan ko kasuwa bai je ba yaron shagonsa ya bari kaɗai.
   
      
                       ******
   
   
    *KATSINA NIGERIA*
   
tsaye take cikin tangameman parlour su ta ƙurawa parlour ido tana kallo harma da kowani sasa na gidan, abubuwa da yawa na mata yawa cikin kwanya da zuciya baki ɗaya, wasu hawaye ne masu ɗumi zuka zubo mata kan fuskarta masu tsananin ciwo, wanda yau kimani shekara uku da ƴan kai take zubar dasu duk lokacin da tunanin ɗiyarta ya ɗarsu azuciyarta, musanman yau da take jin zasu bar gidan da take kallo tana tunata, akoda yaushe, TOFIK ne daketa ƙwallawa Mama kira yasa mama share hawayen kan fuskarta cikin shaƙaƙar muryarta ta ce, "na'am TOFIK menene kuma.?
  "zo ki gani Mama" ɗakin Abba Mama tanufa jin muryar TOFIK daga can tana shiga ta gansa riƙe da bandil na kuɗi da takaddun filaye, ƙarasawa tayi ta sauri ta ce, "TOFIK ina kaga wannan abun.?
    "ƙarƙashin carpet na gani"
    "Dama nan Abban ku ya aje.? Abba ne ya shigo ɗakin yana cewa, "don Allah kuyi da jiki mu wuce dan mu isa da wuri, sanin kan kune daga katsina zuwa Abuja akwai nisa.! Abba ya faɗa cikin ƙosawa da nawar HAJIYA ZALIHA Mama ce ta ce, "ka ga abinda ya tsaida mu Abban TOFIK" sororo Abba yayi ya ce, "ina kuka ga wannan abun.?
     "ƙarƙashen carpet TOFIK ya gani"
    "Ikon Allah na daɗe da cire waɗan nan takkadun a raina, idan ko har nan kuka gansu to tabbas cikin ƴan fashin da sukayi sata ne ya aje mun su, harma da kuɗi ya aje, ikon Allah how comes, ni dai a iya sanina tun randa akayi fashi a gidan nan na rasa waɗan nan kadarori, komawaye da wannan aikin ba sana'ar sa ba ce, sai dai ya tsinci kansa a ciki, ko kuma ya ajesu da niyar ya dawo ya ɗauka shi kaɗai" Abba ya faɗa da mamaki shimfiɗe akan fuskarsa takadun Abba ya amsa yana dubawa duk sunyi ƙura saboda ajiya kuɗaɗen ma gara duk ta cinye wasu, zuge trolley Abba yayi ya zuba su baki ɗaya ciki ya zuba kuɗin cikin aljihunsa ya ce, "mu je ko." kallon gidan Mama take sosai kamar karta barsa wasu hawaye na wanke mata fuska suka fito compound bayan sunyi sallama da ma'aikatan gidan suka shishige mota suka ɗau hanyar abuja.
   
      
                         *******
   
         Tunda HAKIM ya koma nigeria bai zauna ba sai daya tabbatar ya samawa SHAHEED admission a ABU zaria, cikin ikon Allah suka basa Artecture, ranar da HAKIM ya kira SHAHEED kan ya sama masa admission murna wajensa ba'a cewa komai kodaya faɗawa Umma tayi murna ganin zai cigaba da karatu tunda taga yana samu wajen aikinsa dan haka bata kawo komai a ranta ba sai fatan samun nasara ta masa.
          Cikin ɗan ƙanƙanin lokaci ya fara shirin zuwa nigeria kan maganar karatunsa duk da cewa HAKIM ya gama komai dan har registeretion ya masa nasa lectures ne, kuma shi ɗin sai time to time.
         Sannu rayuwa ta cigaba da tafiya yayinda SHAHEED ke zuwa nigeria karatu shima ɗin kasancewar malaman sun san uzurinsa suna ɗaga masa ƙafa sai wata-wata ko fiye da haka yake zuwa, inda ya ji daɗi yana da hazaƙa nan da nan ya kama karatu ya zauna kansa.
               Su BABY ma karatunsu suke hankali kwance babu abinda suka nema suka rasa na rayuwa yayinda yayenta baki ɗaya maza ke nuna mata gata, dan haka ta zama wata ƴar lele cikin yayenta maza, yanzu tana iya cewa ma sun kai uku dan HAKIM ba'a barsa abaya ba wajen ganin farin cikin BABY ba dan yana zuwa niger akai-akai, dan yanzu yana kawowa SHAHEED ƴan kunne da sarƙa daga nigeria zuwa niger dan haka sosai kasuwancin SHAHEED ke bunƙasa dan da dayawan ƴan niger wasu sunfi ganewa zuwa nigeria, amma da SHAHEED ya fara kawo kayansa ƴan nigeria tuni wasu da yawa sun koma siyaya shaguna SHAHEED, malam NUHU ma tuni ya dawo ƙarƙashen SHAHEED aiki ya saki driver mota.
     wasu lokutan yanzu SHAHEED na zuwa da NABIL kasuwa suna aiki tare idan ya dawo daga school dan a yanzu yana SS3 ya ƙara girma sosai, haka shima SHAHEED ɗin ya zama cikaken saurayi mai tashen kuɗi arziƙi sai san barka dan yayi gaba a harkar kasuwa.
            yanzu haka ya fara ƙera masu tanfatsetsan gida a unguwar harobanda wanda ya amsa suna sa gida, baki ɗaya sun sauya sun zama ƴan gayu.

WATA ƘADDARAWhere stories live. Discover now