WATA KADDARA

167 2 0
                                    

🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃
                   *WATA ƘADDARA*
🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃
*Story*
      *And*
          *Written*
                  *By*
*Salma mas'ud nadabo*👑

🖊️ *PEN WRITERS ASSOCIATION*🖊️
{'''we are here to educate our readers, alƙalami yafi takobi'''}

       *WATTPAD*
*salmamasudnadabo*
         

https://t.me/joinchat/VeIADhya0PsbdP9QSD1MDg

   *FREE PAGE*

*Page: 23*

            *Wannan littafin na kuɗi ne for those of you da suke san karanta littafin complete zaku turo 300 kacal a account number na 2261453630 ummusalma mas'ud nadabo zenithbank sai kiyi/kayi screenshot na evidence of payment ki/ka turo ta number na ta WhatsApp 07063683025 sai nayi adding ɗinki/ɗinka a group ɗin da nake posting, zaki iya turo katin Mtn for those of you da basu da account*

                ........Kwance take saman bed ta ruf da ciki tana karatun islamiyya dan an basu harda alƙur'ani a tahafiz, Umma ce ta shigo ɗakin HANIFA ta ce, "a sako aci abinci dai karki ilata kanki da yunwa" ɗaga kai HANIFA tayi ta ce, "toh Umma" tana ɗan murmushi ta aje littafin hannunta gami da ɗaukar cap ɗinta tasanyawa kanta ta sako ƙasa adining ta hango SHAHEED yana sanye cikin red t-shirt  yayinda murmurɗewar hannayensa ke bayane wadda yasha gym gashin kansa nata uban shining duk da sumar babu yawa, tsurawa faffaɗan gadon bayansa idanu BABY tayi tana kallonsa daga steps, yana waya yayinda yake serving kansa abinci ahankali take takawa, yayinda baki ɗaya idanunta na kan duk wani motsinsa har ta iso dining waigowa SHAHEED yayi yana kallonta ya ce, "good girl" abincin daya gama zubawa ya tura mata gabanta ya ce, "acinye yanzu" spoon ta ɗauka yayinda SHAHEED ke kallonta tana cin abincin ahankali take turo abincin har takai rabin abincin ta ce, "hamma na ƙoshi.! wani kallo SHEED ya watsa mata babu arziƙi ta kama turo abincin babu ƙaƙautawa harta gama ya tsiyayo mata ruwa ya ce, "humm.! amsa tayi tashanye tana jin tamkar abinci zai dawo, hannayenta SHAHEED ya kama ya burkita tafukan hannayenta yana kallon tafin hannunta sannan ya matso kusa da ita sosai ya zare glass ɗin idanunta ya buɗe brown eyes ɗinta waƴanda ke white, ajiyar zuciya ya sauke ya ce, "ki kwashe dishes ɗin nan sai ki koma bedroom ki samu rest bacci kawai karkiyi karatu you need some rest" ɗaga masa kai HANIFA tayi tana mamakin wannan abu na Hamma SHEED yau kimani 5years kenan yana kaita asibiti kuma duk bayan kwanaki sai ya mata haka da zarar yaga tana hidima zaice ta wuce hutu, a iya saninta matsalata ɗaya ce ta rashin son abinci sai na rashin kuzari shima ba kullum ba, da wannan tunanin HANIFA ta wuce kitchen koda ta aje dishes ɗin a sink sai itama ta duba tafukan hannunta, amma sam bata fahimci mai yake gani ba sam har ta juya zuwa ɗakinta, tabi lafiyar gado dan maganar SHAHEED kamar yankan wuƙa take wajen HANIFA.

               Ranar wednesday su HANIFA suka gama JSSCE ɗin su sun sha picture a school kam agajiye ta dawo gida, sai kuma hutun da zasu sha kafin a koma hutu su shiga SS1.

              Fitowarsa daga bath kenan yana sanye da bathrobe white jikinsa, baki ɗaya jikinsa da damshin ruwa black skin ɗinsa sai mugun glowing yake, kuma dama skin ɗin SHAHEED irin skin ɗin nan ne wanda daka kalla zaka san mai mugun taushi ne, dan babu wuya abu kaɗan ya ji masa rauni saboda laushin fatarsa, kuma tun fil azal haka jikinsa yake koda yana ruga, wayarsa dake saman bed ce ta ɗauki ruri hannu ya kai saman bed ya ɗauki wayar sunan HAKIM ne ya bayana saman wayar, danna wayar yayi gami da karata akunnasa yana tunanin me zai biyo baya dan yasan HAKIM sarai da complain, aiko yana ɗauka da sallama HAKIM ya ce, "me kake nufi danine SHAHEED baka zuwa biki na ne.? yau biki saura sati biyu amma babu alamar zuwanka kuma kasan da kai zamuyi komai, bani da aboki sama da kai ko baza ka zo bane.? waje SHAHEED ya samu ya zauna bakin gado yana saurara HAKIM dake banbama masifa yayinda eyes ɗinsa ke lumshe buɗe idanunsa yayi ahankali ya ce, "zan zo mana HAKIM kai ma ka san zan zo fa.!.
   "When zaka zo sai ranar ɗaurin aure zaka zo, kome.? to indai haka ne kayi zaman ka bana buƙatar ka a biki na"
   "ka jika da wani zance kuma HAKIM zan zo fa, ina shirin yarda zamu zo baki ɗayan mu ne shiyasa HAKIM, kai kanka kasan dole zanyi attending wedding naka no matter how dude"
"Hmm kai dai ka sani.! HAKIM ya faɗa SHAHEED ya ce, "then me ke going nan.?
  "Babu abinda ke going kamar yarda baka zo ba, haka nima babu abinda na shirya" HAKIM ya faɗa a ƙufule SHAHEED dake saurarasa ya ce, "am sorry dude Allah kau zamu zo mu duka next week"
"toh Allah ya kai mu, kunyi waya da RASHID kuwa.?
  "Tunda ka bani number har yanzu ban kira ba, amma zan kira"
"okay then sai munyi magana" HAKIM ya faɗa yana datse kiran da idanu SHAHEED yabi wayar da kallo yasan cewa HAKIM fushi yake duk da ya basa haƙuri, shi ba zuwa bikin HAKIM ba har yanzu zuciyarsa fal take da fargaba musanman idan yaji Umma na faɗin sai sun je masu gindai village kuma ya san cewa, wannan karan sam Umma bazata saurara masa ba dole su je katsina kuma shi sam baya son tuno yana da wasu dangin uba dan basu da anfani arayuwarsa, domin sune silar afkawarsa fashi wanda abun ke cin zuciyarsa ko wace daƙiƙa na rayuwa.
               Miƙewa yayi ya ƙarasa dressing mirror ya ɗauki body lotion yana shafawa, kana ya ƙarasa bakin drawer ya ɗauko blue shadda wanda akayiwa ɗinkin helf jumper, kasancewar yau friday kuma duk ranar friday manya kaya yake sanyawa, shiryawa yayi cikin kayan he look masha Allah, kafama kansa hula yayi mai ratsin white blue sai ƙafafunsa daya zura cikin takalmin fata mai mugun tsada black, hannunsa na sanye da agogo rolex, jikinsa ya feshe da turare wayoyinsa dake saman bed ya kwashe kana ya fito daga part ɗinsa baki ɗaya.
             Ahankali yake taka steps ɗin kamar wanda baya son takawa saboda yarda yake jin kansa yau ɗin, sam baya son a ambaci nigeria, duk lokacin da yaji nigeria yakan tsinci kansa ciki faɗuwar gaba, tun bayan daya gama degree ɗinsa tunani barkatai ne acikin ransa wanda ke haifama zuciyarsa wani irin nauyi, BABY da fitowar daga bedroom kenan ciki wata black abaya mai stones mai shegen kyau da hijab hannunta da sallaya, tayi bala'in kyau sosai, kayan sun amsheta duk da cewa sam basu nuna shape ɗinta ko kaɗan ba amma tayi kyau, sai farinta dake walwali saboda black kaya data sanya, brown idanuwanta ta ɗago tana kiciniyar parking gashin kanta wanda fir taƙi masa kitso, ganin SHAHEED ya sanyata tunkararsa da murmushi kan fuskarta sosai ya mata bala'in kyau cike da yarinta ta ce, "hamma please ɗaure mun gashina na kasa parking" ta faɗa tana juya masa ƙeyarta SHAHEED ya ce, "ki je Umma ta maki ni masallaci zan tafi yanzu" turo baki HANIFA tayi ta ce, "nima masallaci zan bika fa please kamun" kama gashin kanta SHAHEED yayi wanda ke mugun ƙamshi BABY ta miƙa masa ribbon ya ɗaure matashi tamau, sannan ta sanya milk hijab ɗinta wanda ya mata mugun kyau mai maɗauri a baya, ɗakin Umma ta leƙa ta ce, "umma mun tafi masallaci da hamma"
   "toh BABY ku dawo lafiya"
"Allah yasa.! HANIFA ta faɗa tana ficewa da saurinta SHAHEED dake zaune gaban mota yana danna mata horn ganin zata ɓata masa lokaci, da sauri ta ƙarasa bakin motar har zasu fice NABIL ya fito shima cikin shigarsa ta manya kaya brown, tare suka fice daga gidan zuwa babban masallacin juma'a na niamy.

WATA ƘADDARAWhere stories live. Discover now