🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃
*WATA ƘADDARA*
🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃
*Story*
*And*
*Written*
*By*
*Salma mas'ud nadabo*👑🖊️ *PEN WRITERS ASSOCIATION*🖊️
{'''we are here to educate our readers, alƙalami yafi takobi'''}
*WATTPAD*
*salmamasudnadabo*
*GARGAƊI*'''Wannan littafin da labarin daya kunsa duk mallakar marabuciyar littafin ce, ban yarda a juya min wannan labarin ba, ta kowace hanya, ba tare da izini na ba, dan haka a kula a kiyaye.'''
*TUNATARWA*
'''Labarin dake cikin wannan littafi ƙagaggen labari ne dan faɗakarwa da nishaɗantarwa haka kuma sunayan dake ciki'''
'''BISMILLAHIRAHAMANIN RAHIM'''
*Wannan littafin na kudi ne for those of you da suke san karanta liattfin complete zaku turo 300 kacal a account number na 2261453630 ummusalma mas'ud nadabo zenithbank sai kiyi screenshot na evidence of payment ki turo ta number na ta WhatsApp 07063683025 sai nayi adding ɗinki a group ɗin da nake posting, zaki iya turo katin Mtn for those of you da basu da account**Page: 1*
.......Misalin ƙarfe 12:00pm na dare wadda yayi daidai da ranar litinin gari yayi shuru yayinda iska ke kaɗawa kaɗan-kaɗan sakamakon garin katsina an samu ruwa aranar mai ɗan yawa duk da cewa garin sautari ana ruwa a samu garin da zafi, toh yau ɗin an samu ruwa mai yau da iska dan haka garin yayi luf gwanin daɗi wannan dalilin yasanya GRA tayi shuru tayi tsit dama kuma ba unguwa bace mai yawan tarin jama'a ba, unguwace ta ƴan gayu da masu faɗa aji a garin wayanda suka tara suka aje tafka-tafkan gidaje ne reras akan titin unguwar wanda gida ɗaya tilo yaso yayi zara acikin faɗin layin da alama dai gidan shararen ɗan siyasa ne mai faɗa aji a garin, duk yarda garin yayi lullumi gwanin daɗi wasu tuni sun jima da bacci kuma dama garin ba gari bane wanda mutane ke hada-hada ba har taletalin dare ba, wannan kwanciyar hankalin da aka samu a daren da ni'ima ban da gidan ALHAJI KHABIR, wanda yake maƙil da ƴan fashin da suka masu dira mikiya cikin wannna daren suna iya kiran wannna rana da baƙar rana mafi muni acikin rayuwarsu, tun daga masu gadin gidan har masu aikin gidan kwance suke a compound sunyi flat yayinda jikinsu ke mugun rawa tamkar mazari, wasu daga cikin su sun jima da fara fitsarin wando suna tsiyayar hawaye gami da addu'a yayinda wasu murɗamurɗan ƙati ke tsaye akansu, wasu na kai kawo cikin baƙaƙen kaya fuskarsu refe ruf bakin su da idanunsu ne kaɗai ke buɗe, da manya-manyen bindigu a hannayensu.
Cikin gida kuwa baki ɗaya mutanan gidan na babba parlour kwance suma suna kuka yayinda ALHAJI KHABIR ke tsare da bindinga, murɗeɗan cikinsu wanda ya fisu girma fuskarsa shima rufe yake da facemasks ruf yayinda wasu matasa ke bayansa wayanda baza su wuce shekara shatakwas a duniya ba, sosai ALHAJI KHABIR ya jiƙe da zufa yayinda ƴa'ƴansa uku kukansu ke tashi kaɗan-kaɗan mara sauti cikin kuka gami da rawar jikin ALHAJI KHABIR ya ce, "duk abinda kuke nema zan baku amma don Allah karku cutar mun da iyalli na roƙe ku," cikin husky voice murɗeɗan ƙaton ya bushe da dariya ya ce, "shege ALHAJI wato kana jin tsoron mu taɓa ma iyalli ba, zaman ka lafiya shine duk wani tsinke daka san na dukiyace acikin gidan nan katattaro ta ka bada shine zaman ka lafiya amma idan kaƙi..? fusgo matar ALHAJI ZALIHA ɗan fashin yayi wanda ke kuka mara sauti fuskarta tayi jajur saboda marin data sha lokacin da ƴan fashin suka zo tashinta cikin bacci, da alama buzuwace irin sadaka yala ɗin nan dan fara ce sosai, kuka ta saki yayinda da ƴa'ƴanta mata biyu da namiji ɗaya ke kuka masu ɗan wayau, dan babban cikin su bai wuce shekara sha biyar ba, mai bi masa sha biyu mai bi mata takwas ALHAJI daya rikice lokaci ɗaya ya ce, "na roƙeku don Allah karku cutar da ita Allah zan baku abinda kuke nema in dai kuɗi ne.! ALHAJI KHABIR ya faɗa bakinsa na mugun rawa yayinda ƙaramar cikinsu ke kuka tana cewa, "mama.! cikin daka tsawa murɗaɗan ƙaton yace, "yimun shuru ko kuma na fasa kanki da harshashi" ya faɗa yana ɗana mata kunamar harshashinsa, gum tayi da baki tana shasheƙa yayinda yaran suka ƙara curewa suna shasheƙar kuka suma ɗin yanayinsu kamar buzaye sai dai basu kai mahaifiyarsu ba, kasancewar sun ɗan ɗauko mahaifinsu dake cikaken bakatsine ɗan jahar bakori, ɗan matashin saurayin dake gefe ne ya matso gaban ALHAJI hannunsa riƙe da wayar ALHAJIN wadda ya ɗauko daga saman kujera ya ce, "maza kayi mana transfer ɗin duk wani kuɗi daka malaka domin satace ta saci sata, ɓarayin banza da wofi mun zaɓe ku dan ku mana aiki amma kuna nan kuna jin daɗin rayuwarku da iyallenku acikin manyen gidaje da unguwani masu kyau zaku ci ubanku ɗaya bayan ɗaya yan iska" guy ɗin ya faɗa akausashe ALHAJI da jikinsa ke mugun rawa da laɓɓansa ya ce, "account number ɗin.! karanto masa matashi yake ALHAJI na rubutawa cikin rawar jiki ya tura masu duka kuɗin account ɗin kamar yarda suka ce ,100 million akausashe yace, "duka kuɗin ka tura.?
"duka na tura wallahi duka ne duba ka gani" warce wayar guy ɗin yayi ya duba ya ce, "duk satar da kayi abinda ka tara kenan, ina sauran account ɗin naka.? suma ka turo mana kuɗin ciki baki ɗaya" wata zufa ALHAJI ya share ya ce, "wallahi summa tallahi wannan kaɗai ce dukiyata gaba da baya dana mallaka na rantse ma da Allah, sai kuma ƴan filayan dana siya kwana, kwana nan domin ban jima da fara aikin nawa ba, yanzu muka kafu a gwamnatin tamu, kuma wallahi summa tallahi kamar yarda gwamna ke faɗi babu kuɗi to wallahin babu kaji rantsuwar ɗan musulmi, wannan kuɗin ma dana turo har dana kwangila waƴanda ba nawa ba" kallonsa guy ɗin yake sosai ya ce, "idan ma akwai muka gane daga baya idan muka zo sai mun kashe ka na faɗa ma" Ogan ƴan fashin dake zaune saman kujera yana buƙar sigari ya ce, "you guys ku shiga ɗaku na gidan duk wani gwal daya kwana ya tashi atattaro mun shi a kawosa nan, dan nasan matar ɗan siyasa irin ALHAJI KHABIR bata rasa gwal.! ɗakuna gidan suka shige suna bincikawa ɗaya bayan ɗaya suna kwashe gwalagwalan HAJIYA ZALIHA da atamfofinta wayanda bata samu damar ɗinkawa ba, da duk wani abu mai tsada a gidan wanda ya kwana ya tashi.
Wani ɗaki ɗaya daga cikin ƴan fashin ya shiga wanda yake na ALHAJI, yana shiga ya samu nasara zame abunda ke kan fuskarsa yana maida numfashi da sauri-sauri da alama sabon shigane a harkar dan yarda ya jiƙe da zufa sharkaf kaɗai zai nuna ma halin da yake ciki, kyakyawan saurayine mai ji da ƙuriciya dan ba zai wuce shatakwas ba, black handsome ne naƙin ƙarawa baƙinsa irin mai sheƙi da walwali ne chocolete calour bakin bafulatani ne sumar kansa ta kwanta irin na fulani ta nannaɗe bakinsa daidai misali pink-pink, cikin saurin yake duba drawers ɗin ALHAJI yana kwashe duk wani file daya kwana da takaddun filayensa dana gidaje tare da gwalagwalan HAJIYA ZALIHA dake ɗakin da kuɗaɗen daya aje cikin drawer, har zai fita sai kuma ya dawo ya maida takaddun filayan cikin sanyin jikin gami da tausayin ALHAJIN daya shigesa, ya turasu inda babu wanda zai gani bandil ɗin kuɗin daya ɗauka cikin drawer ya cire daga jikinsa ya aje masa ƙarƙashin carpet, sannan ya ɗago da sauri, karaf idanunsa suka faɗa saman gadon ALHAJI yarinyace wadda bazata wuce 3years ba, ke zaune da alama yanzu ta tashi daga bacci farace tas gashin kanta wanda yasha ribbon sai sheƙi yake, hannunta ɗaya cikin baki, murmushinta me kyau take masa tana ɗaga masa hannaye alamar ya ɗauketa tana dariya, hakan yasa ya tsinci kansa da sakin murmushinsa mai kyau har fararen haƙoransa na bayana ya ɓoye bindigar hannunsa ya furta, "yaro man kaza bama ta san fashi na zo ba, amma sai wani washe mun baki take yarinya kun kusa fara talauci kema ki ji yarda muke ji munafuka.! dariya ta kuma saki tana zolo saman gadon kamar yana faɗa mata abun kirki rarafawa tayi daga kan gadon kamar zata faɗo ya taro ta da sauri, dariya ta kuma saki tana kai hannunta saman karan hancinsa wadda yake mai tsini tana raba idanunta da alama sosai ya shiga ranta kamar dama ta san sa tun ba yau ba, ɗage mata gira yayi ya ce, "kyakyawar baby.! ƙwalla masa kiran da akayi ne ya sanyasa direta ƙasa da sauri ya maida facemasks ɗinsa ya ɗauki jakarsa, kuka yarinyar ta saki tare da riƙe masa ƙafa cikin tsamun muryarta ta ce, "anbinka abu.! zame hannunta yayi dake jikinsa ya fice da sauri, ai itama kamar tana jira ta bisa tana kuka hannunta a baki, lokaci ɗaya mutanan parlour suka waigo kallo ya koma kan kyakyawar yarinyar dake kuka tana cewa, "abu..! cikin muryarta da bata fita hannunta a baki tana kuka bilhaƙi Ogan ƴan fashin baki ɗaya yace, "wannan fa mai kukan ina aka samota.? tona mana asirri zakiyi mai sufar aljannu ko kiyi shuru, ko kisha harshashi yau ga ƴar jakar uba kai." da gudu ta ƙarasa wajen saurayin da suka fito kusan tare ta kama masa ƙafa tana jan majina da sauke ajiyar zuciya, kallon-kallon aka shiga yayinda iyayenta jikinsu ke mugun rawa ƙirjinsu na bugawa da mugun ƙarfi, ganin yarda ta shegewa ɗan fashin ta kame ƙafarsa kamar ta ubanta, tana tsotsar hannu, ɗauka ɗaya oga ya mata ya tsilata, cikin iyayenta cikin kakkarwa iyayenta suka tare abar su wani irin ihu ta fasa kamar sun watsa mata ruwan zafi, wanda hakan yayi daidai da jiniyar ƴan sanda sakamakon maƙocin ALHAJI dayaga ƴan fashin sanda suka shigo gidan ALHAJI KHABIR ya ɗaga waya ya kira ƴan sanda, shima ɗin a kiɗime dan yasan suna iya shigowa gidansa da zarar sun gama da gidan ALHAJI KHABIR.
Bindinga oga ya ɗaga zai ɗauke kyakyawar yarinyar da harbi saurayi ya shiga tsakani yana cewa, "ka kyaleta BOSS karka taɓata yarinyace.!
"idan baka matsamun ba sai na fasa kanka da bullet" matsar da shi ogan yayi da ƙarfi yayi ƙasa dan ya fisa girma nesa ba kusa ba, ya ɗana kunamar bindigarsa da sauri ya miƙe ya shiga tsakanin su yayinda su ALHAJI suka ƙara takurewa suna kuka akausashe ya ce, "BOSS nace karka taɓata kana taɓata zan ɗauke ka da harbi.! ya faɗa cikin zare idanunsa yana nuna Ogan nasa da bindiga yana sauke numfashi ya tare iyallan ALHAJI, gefe ɗaya yarinyar kuka take saki Mamanta na toshe mata baki tana kuka mara sauti yayinda jiniyar ƴan sanda ke ƙara yawa cikin unguwar, ƙwacewa tayi daga ruƙon Mamanta tana cewa, "abu..! cikin kuka ta rarrafa ta ƙara komawa wajen wanda dai ta gani a ɗaki ta kama masa ƙafa ta riƙe gam tana shasheƙar kuka ɗaga ɗan yatsansa OGA yayi yana nuna saurayin ya ce, "bani da lokacin ka yanzu" da sauri ya shiga jidar jakunkuna da suka loda kayan gidan ALHAJI na dukiya yana jefewa sauran ƴan fashin dake waje suna caɓewa suna lodawa cikin mota, yayinda da saurayin ya tasa su ALHAJI ɗaki hannayensu saman kai, har lokacin kyakyawar yarinyar na biye da shi gam duk ta takura masa ta shige masa, suna shigewa ɗakin ya cire hannunta dake saman ƙafarsa ya turata ɗakin, kuka ta fashe da shi ta kuma riƙesa gam OGA ne cikin ɗaga murya ya ce, "kuyi da jiki mu bar gidan nan ƴan sanda are here ka rabu da su ka taho asirrin mu zai tonu.! gam yarinyar ta maƙale ƙafarsa ɓanɓare hannuta yayi da ƙarfi ta fashe da wani irin kuka har da tuma ƙasa ta miƙe da gudu tana bin bayansa, ganin haka kawai ya miƙa hannu ya ɗauketa cak ya fice da ita da sauri shima....
*Follow me on facebook page n group*: *salma mas'ud nadabo*
*Follow me on IG*: *Salmerh 777*
*VOTE*
*COMMENT*
*SHARE*~Taku har kullum salma mas'ud nadabo~
![](https://img.wattpad.com/cover/251826261-288-k339621.jpg)
YOU ARE READING
WATA ƘADDARA
ActionKo wani bawa nada tasa zanan ƘADDARA sai dai shi tashi tasha banban data saura, komai ya farune daga ranar da mahaifiyarsa ta kwanta ciwo, ya buga ya nema domin sama mata kuɗin magani dana asibiti duk da yana matashin saurayi mai ƙarancin shekaru ɗa...