WATA ƘADDARA

87 5 0
                                    

🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃
                   *WATA ƘADDARA*
🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃
*Story*
      *And*
          *Written*
                  *By*
*Salma mas'ud nadabo*👑

🖊️ *PEN WRITERS ASSOCIATION*🖊️
{'''we are here to educate our readers, alƙalami yafi takobi'''}

       *WATTPAD*
*salmamasudnadabo*
         

https://t.me/joinchat/VeIADhya0PsbdP9QSD1MDg

   *FREE PAGE*

 
*page: 4*

    
     *Wannan littafin na kuɗi ne for those of you da suke san karanta littafin complete zaku turo 300 kacal a account number na 2261453630 ummusalma mas'ud nadabo zenithbank sai kiyi/kayi screenshot na evidence of payment ki/ka turo ta number na ta WhatsApp 07063683025 sai nayi adding ɗinki/ɗinka a group ɗin da nake posting, zaki iya turo katin Mtn for those of you da basu da account*

   
                ....Kuka take rairawa ahankali tana shafa cikinta SHAHEED ya ce, "yunwa.? ɗaga masa kai tayi tana turo pink laɓɓanta shafa kanta yayi ya ce, "ki ɗan ƙara haƙuri baby yanzu su HAKIM zasu dawo okay" saman cinyar SHAHEED ta ɗaura kanta tana shan hannu yana shafa kanta ahankali.
          Ɗaga labulen ɗakin da akayi ne yasanya SHAHEED miƙewa tare da ILHAM ganin su HAKIM, ledojin hannayensu suka miƙa masa ya amsa, suma waje suka samu suka zauna suna tunanin ta ina zasu shedawa SHAHEED UMMA ta koma gida.
                ledar dayake tunanin ta abincin ce ya buɗe chips ya gani harda kwai ya buɗe ya ce, "zauna ki ci abincin ko.? zama tayi ta tanƙwashe ƙafafunta tasanya hannun hagu ƙaɓe hannun SHAHEED yayi ya ce, "ba kyau cin abinci da hagu" da wannan zaki ci SHAHEED ya faɗa yana kama hannunta na dama raurau tayi da idanu tana ɗaukar abincin ahankali rabin abincin na zubewa ƙasa, matso da abincin kusa da shi SHAHEED yayi ya ce, "zo nan.! miƙewa ILHAM tayi ta ƙaraso wajensa ya ce, "zauna" zama tayi idanunta raurau da ruwan hawaye chips ɗin ya ɗebo ya ce, "haaa.! buɗe bakinta tayi ya tura mata dankalin abaki ta amsa tana ci haka ya dinga ɗebowa yana bata tana amsa hannu tasa ta ɗebo abincin ta nufi bakin SHAHEED ganin yana ta bata shi bai ci ba ta ce "haaa.! ɗan murmushi SHAHEED yayi ya ce, "ci abunki ni na ƙoshi" raurau da idanunta ILHAM tayi tana kallon abincin hannunta ƙasa tayi da kanta, chpis ɗin ya kai bakinta ta kawar da kanta cikin maganarta da batayi ƙwari sosai ba ta ce, "na ƙoshi nima.! shafa kanta SHAHEED yayi ya ce, "baby rigima.! buɗe bakinsa yayi ya ce, "haaa.! dankalin ta tura masa baki ya amsa lokaci ɗaya UMMAN sa ta faɗo masa arai ya jefa masu HAKIM tanbaya da cewa, "ya jikin UMMA.? ƙasa da kansu sukayi RASHID ne  ya ce, "Ka gama cin abincin tukun na"
        "ni dai ku faɗa mun halin da UMMA ke ciki" RASHID ne ya ce, "UMMA sun koma ƙafur saboda babu kuɗin magani koda muka je bamu same su ba.!  shuru SHAHEED yayi can  ya ce, "ya zamar mun dole na bar wajen nan yau"
       "Toh ya zakayi da yarinyar bayan itama anata cigiyarta gidan TV"
         "Duk yarda zanyi koda gidan sune sai nayi ƙoƙarin maidata"
        "Baka da hankali SHAHEED wani irin maidata gida, yarda ka taho da ita haka zaka cigaba da rayuwa da ita ko kuma asirrinka ya tonu kasan dole ciki biyu za'ayi ɗaya" RASHID ya faɗa, SHAHEED ya ce, "ya zan tafi da ita me zan cewa Ummana, baki ɗaya yarinyar ta rusa mun plan" RASHID dake cin abinci ya ce, "yarda ka taho da ita haka zaka cigaba da rayuwa da ita kuwa, tun yanzu ma ka fara tunanin yarda zaka tsara ko wani plan da ita na rayuwarka, kuma zaɓi biyu ya rage ma ko kayi nisa da ƙasar nan ko kuma ka bar gari ko kuma asirrinka ya tonu, sai dai ina me faɗa ma karka kuskura suna ɗaya daga cikin mu ya fito..! RASHID ya faɗa cikin ɓacin rai SHAHEED da RASHID ya fara ƙulesa ya ce, "toh nace zan tona ka ne.? ka bari idan nace zan tona ka sai ka fara faɗa mun magana, ni na taho da yarinya dan haka ku zuba mun ido ku ga yarda zanyi da ita, bana son ƙananan maganganu"
  "ai dama idon zamu zuba ma, kuma kai ke cikin wannan chakwakiyar ba kowa ba SHAHEED.! wawan naushi SHAHEED ya kai ma RASHID akan fuska dan bai iya musayar yawu ba, yana watsa masa wani matsiyacin kallo, dafe kumatunsa RASHID yayi yana kallon SHAHEED da tuni ya fasa masa baki, a fusace ya ɗago rikici ne ya ɓale tsakanin SHAHEED da RASHID HAKIM ne ya shiga tsakanin su yana cewa, "ya isa haka don Allah ku barmu muji da abinda ya damemu mana, me haka kuke tsakanin ku.? SHAHEED dake sauke ajiyar zuciya saboda yarda ransa ya ɓaci ya saki tsaki ya kama hannun ILHAM ya ce, "kin ƙoshi.? ɗaga masa kai tayi sam bata wani ci abincin da yawa ba duk da yarda take rakin yunwa, kayan da su HAKIM suka kawo mata ya ɗauka yasaka mata ƴar duguwar riga ya kama hannunta suka fice daga tantin.
       
           
       
              ******
       
        Kuka kawai take muryarta har ta dashe yayinda ƴan uwa da abokan arziƙi suka wuni suna zuwa jajenta masu abinda ya faru, ABBA ne ya shigo ɗaki ya samu Mama har yanzu tana sana'ar kuka ledojin hannunsa ya aje ya ce, "ZALIHA.! ɗago jajjayen idanunta tayi ta zubawa ALHAJI wayanda har lokacin suna fidda hawaye ya ce, "don Allah ki ragewa kanki wannann damuwar, har yanzu ƴan sanda na iya bakin ƙoƙarin su ganin cewa ILHAM ta dawo lami lafiya, yanzu haka daga office ɗin ƴan sanda nake" Mama take kuka ta ce, "uhm.! tana mai ƙara rushewa da kuka mai ciwo Abba ya ce, "kiwa Allah ki rage wannna kukan kin dai ji abinda likita yace, jinin ki ya hau ko dan abinda ke cikin ki ya kamata ki rage wannan damuwar," cikin shasheƙar kuka ZALIHA ta ce, "dole na damu ABBAN ILHAM, tun jiya babu labarin anga ɗiyata har ta kwana da yini ɗaya amma babu labarin ILHAM ya ake so nayi da raina,.?
             "Addu'a zakiyi ZALIHA ba kuka ba insha Allah ILHAM zata dawo cikin ƙoshin lafiya, nima ina jin ciwo a raina ZALIHA sai dai ba abinda zanyi wadda ya wuce addu'ar Allah ya bayanata, haka suma ƴan uwanta ki duba ki gani yarda suma yini ɗaya suka shiga damuwa, mu ya kamata mu daure mulallashe su ZALIHA kin ji" ALHAJI ya faɗa yana ɗaura kan HAJIYA ZALIHA saman ƙaffaɗarsa.
       
       
                 ******
       
       
         Bayan an kasawa kowa kuɗinsa sun tashi da maƙudan kuɗaɗe bana wasa ba dan ko aranar da sukayi fashin gida uku suka shiga, aranar gidan ALHAJI ne gida na ukun kusan baki ɗaya dukiyar da aka kwaso gidan ALHAJI KHABIR SHAHEED ne ya sameta, da duk wasu gwalagwalan gidan duk tsinken da aka kwaso na gidan ALHAJI KHABIR SHAHEED ne ya kwashe galimar gidan, suma sauran kowa ya samu abinda yake so dan haka murna fal acikin zuciyoyinsu, SHAHEED kuwa har tsorata yayi da dukiyar daya samu bai ma san ina zai aje su ba, cikin baƙaƙen jakunkuna suka jidda kuɗaɗen da suka samo kowa ya goya abarsa kuma dama Ogansu ya kawo sabin machine kowa ya haye nasa bayan duk sun gama sallama da juna.
               Ogansu ne ya ƙaraso wajen SHAHEED dake riƙe da hannu ILHAM ya shafa kan ILHAM cikin hausar sa da bata fita ya ce, "Allah ya tsare ka SHAHEED amma ina jin tsoro sosai koda asirrinka ya tonu..! SHAHEED ne ya katsesa da cewa, "bazan taɓa tonaku ba domin ka taimake ni.! SHAHEED ya faɗa rungumesa PETER yayi yana buga bayansa ya ce, "Allah ya ba UMMAN ka lafiya" da  "amin.! SHAHEED ya amsa, OGA PETER ya ce, "Anjima motar kaya zata zo sai ka bita ku wuce ƙafur, ka tabbata kayi nisa da ƙasar nan SHAHEED dan mindin ka zauna Nigeria sai asirrinka ya tonu, kayi nisa da ƙasar nan.! jinjina kai SHAHEED yake idanunsa cike da hawaye bandil uku na kuɗi PETER ya zaro ya ce, "ga ƙari cikin kasona kamar yarda kamun alƙawari zakayi kasuwanci ka gama fashi ka tabbatar mun da haka, ko bayan raina SHAHEED ka gina rayuwa mai kyau ba irin namu ba ina ji ajiki na wata rana zanyi alfahari da kai.! duk da SHAHEED yaso ƙin amsar kuɗin amma PETER ya dage sai daya amsa HAKIM da RASHID ne suka rungume SHAHEED HAKIM ya ce, "duk inda ka koma arayuwa karka manta dani kai ɗin abokina ne ko ina ka je arayuwa ka tuna dani SHAHEED"
          "insha Allah HAKIM bazan manta da kai ba" SHAHEED ya faɗa yana ƙara rungume HAKIM, RASHID dake tsaye ya ce, "sai wata rana SHAHEED duk inda ka shiga ka sheda mana ko ziyara ne na kawo ma" rungumesa SHAHEED yayi ya ce, "am sorry for the misunderstanding" kaffaɗarsa RASHID ya doka ya ce, "is okay.! ya faɗa yana zame jikinsa daga jikin SHAHEED machine suka haye haka sauran suma duk sukayiwa SHAHEED bankwana, yana kallon su suka haye machine na suka fice daga jejin da gudu, saman irin machine ɗin nan mai kibiyu, jejin ya rage daga SHAHEED sai ILHAM zaunawa sukayi suna jiran motar kaya kuma dama sai can dare zata zo.
       
                  Misalin ƙarfe 11:00pm na dare SHAHEED ya goya ILHAM dake bacci ya fito daga jejin fuskarsa rufe da irin abun nan na buzaye, wata motar kayace ta tsaya tifa, SHAHEED ya ƙarasa wajen suka gaisa da driver motar sannan ya zagaya ya shiga bayan motar can cikin kaya tare da kwantar da ILHAM saman jikinsa ya rufeta da zani, sannan ya jawo buhunhuna dake cikin motar suka masu rumfa yarda ba mai iya ganewa suna wajen.
             Bayan driver motar ya tabbatar da ba mai gane akwai mutane bayan motar ya ƙara loda masu kaya atishawa ILHAM ta saki saboda kura, ta ƙara shigewa SHAHEED  sukayi lamo dan ita tuni tayi bacci shine dai da zuciyarsa ke lugude ya kasa samun nutsuwa saboda tsananin tashin hankali,  dakarfin gaske zuciyarsa ke bugawa gami da tsintsinkewa, yayinda da kansa ke mugun sara masa, saboda tashin hankali sosai yake cikin ruɗani da zulumi yayinda nadama ke rufesa kowace daƙiƙa, har motar su ta tashi kasancewar driver ƙwarare ne wajen tuƙi, ta jeji suka dinga bi suna tafiya, kasancewar daga katsina zuwa ƙafur tafiya ce mai nisa, sun jima suna tafiya kafun su iso ƙafur sun kwashe kusan 3hours suna tafiya sannan suka iso cikin dare sosai misalin ƙarfe 2:00pm na dare, a wani jeji motar ta tsaya wanda babu gida gaba babu gida baya, sai gonanaki na fulani driver motar ne ya ƙaraso ahankali yana cewa, "SHAHEED mun iso" tuture kayan SHAHEED yayi ya fito ɗauke da ILHAM yana kallon gonanaki dake wajen inda daga gefen gonakin a rubuta MASU GINDAI village dake cikin ƙaramar hukumar ƙafur, ƙauyen fulani kenan aljihunsa SHAHEED ya zura hannu ya zaro bandil ɗaya wadda PETER ya basa ya miƙawa driver motar fuska washe ya amsa yana cewa, "Allah ya saka da alkhairi SHAHEED Allah kuma ya ƙara rufa asirri.! ba tare da SHAHEED ya tankasa ba yayi gaba....

*Follow me on facebook page n group*:  *salma mas'ud nadabo*

*Follow me on IG*:  *Salmerh 777*

*VOTE*
*COMMENT*
*SHARE*

~Taku har kullum salma mas'ud nadabo~

WATA ƘADDARAWhere stories live. Discover now