Kan dan dakalin da ke kofan apartment in su ya ke a zaune yana kallon yanayin garin da ya fara hada hadari. Tun jiya bayan tafiyan ta bai iya kara fita daga side in nasu ba. Daman ya san makarantar will never be the same sabida rashin ta a ciki. Duk yanda zuciya shi ke kwaidata mishi son kasancewa da Nabila, wani lokaci ya kanji cewa anya ba ta mishi karanta ba kuwa?
A haka abokin shi mansur ya zo ya iske shi a wurin. Kaman ba zai mishi magana ba da farkon sai can kuma yace "anya mutumina ba zamu shirya mu bi hanya Kaduna ba kuwa?" Murmushin dole yayi ba tare da ya shirya ma hakan ba. Mansur ya kara cewa "ina ga mafitan kawai kenan" tabe baki Abubakar yayi yace "to wai na ce maka ina son ganin ta ne?" Yanda yayi maganan cike da nuna basarwa ya sa mansur darawa "kai ma ka san ka gaya ma wani amma ba dai mansur ba da kuke kwana daki daya" Abubakar bai kara cewa komai ba sai ma mikewa da yayi ya shiga daki bai dade ba ya fito da gift bag in da ta bashi jiyan kafin ta fice. Nan gefen mansur ya koma ya zauna, shi dai mansur kallon shi kawai ya ke. Hannu ya sa a cikin bag in ya fiddo wani album. Hard copy in hotuna guda uku ya ciro daga cikin folder, sai da ya gama karewa kyakyawan fuskan da ke cikin hoton kallo sosai sannan ya nuna ma mansur "I have this to talk to in ina son ganin ta" abin ma dariya ya bawa mansur, like who does that a wannan zamanin. Sai da yaga Abubakar ya bata rai sannan ya sausauta dariyan nashi "Ai dole in yi dariya Mutumina, wa ke wani amsan hotunan mace a wannan zamanin? If you want to see her call her video call or better ma kaje gidan su, in dai soyayyan gsky kake mata fa amma"
Dan Jim Abubakar in yayi kafin yace "ba ma sai na fada maka irin son da nake mata ba mansur, you know everything. Matsalan dai in ganin kaman tayi karama."
Tsaki Mansur ya ja cike da takaici, kalaman abokin nashi kadai ya isa tabbatar mishi shi din bako ne a wannan fagen. "Kaga malam if you like her go get her, mace ba ta wani karanta kawai kai dai ka nemi soyayyan ta, ta yanda za ta amince da kai ko da a gidan su an hana ta sauraran maza ne sai ta shiga jami'a to fa in har tana son ka ka gama. Ai laggon mace kenan ka dana mata dafin soyayyan ka"
Sauraron mansur in ya ke har ya gama sannan ya ce mishi "kai kake ganin ban san halin mata ba, I know everything wannan in dai kawai ina ganin tayi karama ne da irin karatun da nake bukatan koya mata"
Da sauri mansur yace "then teach her everything, irin su ma sun fi saurin dauka" tafa hannu su kayi suna dariya, mansur ya sake cewa "just call her now"
"Ni fa ban ma da numbanta" sakin baki mansur yayi yana kallon shi "tab! Maganan babba ne, to kai ta ya akayi kayi gangancin nan? Amma we have many ways of getting her number" da sauri Abubakar yace "no need, I give her a letter daren grad insu, if she feel the need za ta kirana, na rubuta mata numbana"
A bangaren Nabila kam, bayan ta koma daga rakiyan Anty salma dakin da ta ke sharing ita da Amina ta nufa da tunanin coper Abubakar wanda ya ki barin ta sam ta sarara. Tun dazu ta ke tunanin abinda ya bata ana washegari graduation, wanda ta dau mishi alkawarin lallai lallai sai ta isa gida za ta bude.
Gift bag ne na musamman, gabadaya ta zazzage jakan kan gado tana son ganin mai ya kunsa. Karamin kwalin da ya fara jan attention inta ta fara dauka, silver ring da bracelet ta gani masu dankaren kyau, ita kadai tayi dariya tana fadin "Allah sarki sir nagode" a fili. Unwrapping in sauran tayi. Books hard copy ne guda hudu, biyun novel na Collen hoover da Danielle steel, if she can remember ya bata lbrn books in tace za su yi dadi, wato shine yaje ya siyo mata. Biyun kuwa motivational book ne da poem collection. Dan note in da ta gani a gefe books in ta dauko tana dubawa. Handwritten in shi ne
“i hope you can read this books to avoid doing nothing at home before you start seeking for admission.
Abubakar Sadiq Mambila"Ba ta san sanda ta rungumo littatafan tana kara kallon handwriting in shi ba, a zuciyan ta tana raya sir bai mata adalci ba da ya amshi hotunan ta shi kuma ya ki bata nashi duk da ta bukaci hakan.
YOU ARE READING
Zuciya Da Gwanin Ta
RomanceBurin zuciya a ko yaushe shine ta samu gwanin ta. Ko da kuwa hakan zai zama illa a gare ta. To amma in hakan ne kadai ya rage zabi, ya abin kan kasancewa? Ku biyo ni... Ku fito kuji labari zazzafa Kan zuciya da gwanin ta Tsokar da babu irin ta mai s...