4

409 38 3
                                    

Duk wani hiran su da Amina sun gama shi, shirin bacci su kayi don har sun kashe wuta. Amina kam har ta tofa addu'a sai ga Mami ta shigo ta kunna musu wutan.

"Har kun kwanta ne?" Ta tmby su, a tare su ka amsa mata. Tace "okay it brief, Nabeelarh Abban Ku zai je Bauchi gobe, Umma ba ta dan ji dadi zai je dubo ta. Yace in tmby ki zaki bishi ne ko kuma sai nan gaba?"

"Mami me ke damun Umman?"

"Kawai ba ta jin dadi ne kwana biyu kinsan an fara tsufa. Za kije in?"

Shiru tayi tana tunani, to kadunan ma ba wani dadi ya ke mata ba ko bakomai a can Umma za ta na sata nishadi "zanje mami" da sauri Amina tace "mami nima ina son zuwa" hararan ta mami tayi ta kashe wutan dakin "ke da ke zuwa school, lafiyan ki kuwa?" Dif Aminan tayi.

Tunda Asuba ta tashi, ta san tafiyan Abbah da Safe yake yi ko da kuwa Zaria za shi balle bauchi. Su Aiman da Siyama kaman su yi kuka da zasu wuce School, lallaban su dai tayi su ka wuce. Aiman da Siyama su Hampos su ke, Amina ce dai ke Universal sai Sadeeq da ke Darul Iman, makarantan da Nabeelarh ta gama.

Wuraren takwas da yan mintuna Abbah ya fito su ka kama hanya. Ita dai har wani irin ta keji ba ta ji dadin barin yan kannen ta da mami ba, yaushe rabon da ta zauna gida ta dade sai daiyanzu kuma da dama ya samu za ta kwashi kafa tayi bauchi? Anya ba za ta biyo Abbah su dawo ba kuwa? Ita kadai abinda ta ke ta kullawa tana kuncewa. "Daughter lafiya na jiki shiru kuwa?" Abbah ya tmby ganin yanda jikin ta yayi sanyi.

Murmushi ta kakalo ta ce "Lah bakomai Abbah"

"Applied Chemistry kika yi applying ko?" Da eh ta amsa mishi yace "Daughter za ki iya KASU kuwa? Ko dai in kaiki private University, ga baze, Nile a Abuja ga Alqalam katsina ko Alhikmah Ilorin" dan jim ta yi tana tunanin ina ne mafita. Can kuma sai tace "Abbah ko ina ka kaini zan iya karatu In sha Allah" murmushi yayi sanin halin yar tashi akwai kawaici ko da ko akan abinda ta ke so ne "ba za ayi haka ba Daughter, ki dai yi tunanin duk inda kika ga ya miki sai ki fada min, in ma Kasu in ne duk ai ba matsala"

Karfe biyun rana su ka isa garin bauchi. Old GRA a nan gidan Umman. Da fara'an ta, ta karasa ciki tana Kiran "Ina kike fito na iso" daga daki taji Umman tayi gyaran murya.

"Hajiya Umma Sallau kenan" ta fada da dan dariyan ta, sannan ita ma tayi saurin shiga bayi. Abbah Kam suna shigowa ya nufi Masallaci, dake shima ya tarar ana Sallan. Har ta idar da Sallan ta, ta gama azkar Umma ba ta gama Nafilfilun da take yi ba. Dan tabe baki tayi, a hanyan kitchen ta hadu da baba saude, Mai aikin Umman. "Baba Sannu da aiki, Allah ni dai Yunwa nake ji"

Dariya baban tayi tana fadin "Maraba da Uwar dakina, Hajiya Nabee ashe har dake ake tafe" turo baki Nabila tayi tana hade rai.

"Ni fa nace miki ban son sunan, babah mana"

"Afuwan Uwar dakina, je ki abinki yanzu zan kawo abincin" da dan gudun ta Nabeelarh ta fita zuwa falon gidan. Girgiza Kai babahn tayi, tana mamakin har yanzun akwai sauran yarinta gun Uwar dakin nata, duba da yanda ta ke kwasan gudu hankalin ta kwance, ba tare da wani damuwa ba.

Sai lokacin Umma ta idar da Sallah ta fito falon "ke Kuma me ya kawo ki? Nace ki zo ne?" Nabeelarh ba ta amsa ta ba ma Sai ma saurin rungume ta da tayi.

"Ni dai nayi kewan ki Ummah, shiyasa nazo" dariya Umman tayi tana fadin "in dai kika karya ni, to wlh Uban naki da ya kawo ki ban neme ki ba shi zai biya ni Kashi na. Kuma ba asibitin da aka isa a kaini"

Share zancen Nabeela tayi, don ba yau Umman ta saba fadin haka ba. "Ni dai zo ki bani abinci a baki, don wlh yunwa nake ji. Ni gidanmu ban saba da zama da yunwa ba gsky" dakuwa Umman tayi Mata.

"Kinsan ni kuwa ban gaji Yunwa ba. Kuma ni banda halin Uwar taku, da sai ta Kai karfe Tara na safe fa sannan wai zata tashi ta daura ma mutum abinda zai ci. Shiyasa ai na daina zuwa wannan gidan naku, banda ganawa mutum azaba ba abinda ake" Nabeelarh dai bata ce komai ba, tasan tana fadin wani abu Mami zata ja ma zagi. Ta rasa dalili, Sam Umma ba ta shiri da Mami. Duk kuwa abinda Mami zata Mata to bai birge ta. In kuwa aka ce yau Umma na hanyan zuwa Kaduna, to fa ranar tashin hankalin Mamin ya zo kenan. Duk dai cikin jikokin ta ba Wanda ta ke hantara, dan tsaf take zama ayi ta wasan jika da kaka da ita to Amma Uwar fa Sam ba ta daukan mata ba. Abun naci ma Nabeelarh tuwo a kwarya sosai, don ta dau alwashin watarana Sai ta tasa Umma ta gaya Mata mai mahaifiyar su ta mata haka da zafi.

Zuciya Da Gwanin TaWhere stories live. Discover now