6

327 30 4
                                    

Halima ta sa ta gaya ma Umman za suyi bako. Hararan ta Umma tayi tana fadin "Kai kaji min yarinyar nan, ni kakar kice da Zaki kawo min saurayin ki? Harda zuwa ba ko kunya wai Umma za a zo gaishe ki" hade rai Halima tayi.

"In kin kwantar da hankalin ki jikar taki ce zata kawo shi bani ba" murmushi Umman ta Fara "Au to kice bakon wannan ja'irar yarinyar ne. Amma ke tsaya me ya hada ki da yan nan garin kina garin gwamna fisabillahi. Ni fa ban son matsiyata gaskiya"

Dariya ma abun ya so ya basu. "To Umma ba ma dan nan garin in bane. Daga Kano zai zo, shiyasa aka gaya miki domin a shirya tarban shi" Halima ce ta sake bayanin, nan da nan kuwa fara'an Umman ya karu.

"Ah to Ma Sha Allah, ince dai iyayen naki basu sani ba? Don na fi so ni in Fara ganin shi, in tantance shi tukunna" Nabila dai tabe baki tayi. Tana jin Umman na kiran babah akan azo a hada ma bako kayan tarba.

"Ai Sai gobe zai zo" tana fadin haka, ta dau gyalen ta suka yi saurin yin waje. Wurin Friend inta da suka gama school tare, Rukayya. Suna fita suka ci karo da Yaya Khalipha, da sauri su ka juya cikin gidan a tare. Ai kuwa a hanya suka hadu da Anty za ta fita Unguwa. Nan fa su ka fara rokon ta akan tace tare zasu fita, saboda Kar ya hana su.

Ai kuwa Yana hango su ya mike yana gaida Antyn. "Anty Unguwa Zaki je ne? Muje in sauke ki mana" a tare suka kalli juna, Sai Kuma su kayi saurin basarwa. Hakanan su ka shiga motan ba da son ransu ba, gashi gidan da Anty zata kwata kwata ba hanyan inda suka dosa bane. Don wahala hakanan suka tsaya, ya sauke su sannan, bayan ya wuce suka lallaba zuwa inda zasu.

Ranar da Abakar in zai zo, tun da safe ba ta iya komawa bacci ba ma. Tsabagen tension da bata San na menene bane, ba wai ranar za ta Fara ganin shi ba. Sai dai tasan Kuma ba ta taba zama dashi a matsayin wanda wani alaka ta so ke tsakanin su ba. Gabadaya Sai ta ke jin kaman ba Sir in da ta sani bane zai zo wurin ta.

Ko bayan sun gama karyawa, Wanda abincin ma ba wani maida hankali tayi taci ba. Sai kaiwa da komowa take duk ta kasa natsuwa. Umma dai zuba Mata idanu tayi, Sai da ta ga abun ba na kare bane tace "Oh ni ya' su. Yaran bana Sam ba kunya, yanzu ke saurayin kike ma rawan jiki tsakanin ki da Allah? Ni Kam wannan wani irin tarbiyya ne wai ma'u ta baki?" Nabila ba ta tanka ta ba, fama ma ta ke da abinda ya dame ta ita. Halima kanta, dariya kawarta ta take bata.

"Ke relax mana Nabila, lafiyan ki kuwa? Sai kace in yazo cinye ki zai yi wai? Dan Allah kwantar da hankalin ki. Ba fa yau Zaki Fara ganin shi ba, all these nervousness" da kyar ta iya kakalo murmushi. "Ni ma bansan meya sameni ba Halima, i can't be calm" dariya Haliman ta kara yi "Ni ko zan so in ga wannan mai sa'an haka"

Karfe biyun rana ya iso, da ke a ranar zai wuce Jalingo. Nabila Kam kasa zuwa shigo dashi tayi, Sai Halima ce da wani kanin ta su kaje su ka shigo dashi har falon Umman.

Da fara'an shi ya dan durkusa kasa yana gaida Umman. Ta amsa tana kallon shi, da gangan Halima taki matsawa domin ta ga reaction in Umman kawai.

"Mun same ku lfy kaka?"

"Ina fa lfy dan bature? Ina nan ina fama da ciwon baya da kafa, ga ba daman mutum yayi magana yanzu sa ce wai tsufa ne. Na ga dai su inma zasu tsufan, ko ba haka ba dan bature?" Murmushi yayi sosai "Hakane Kam Umna"

"To Kai ko dan bature, tsakanin ka da Allah ina jika ta, ta samo ka ne wai? Anya ma ba niyyan dauke ta kake dashi ba? Gama yanzu naji ance garkuwa da mutane shine sana'an da ke ta..." Dariyan Halima ne ya katse Mata maganan ta. Duk su ka juya suna kallon ta.

"Wlh ba ni bace abun dariya, Kakar ki Innah ita ce abun dariya Amma bani ba" saurin wucewa Halima tayi, don tasan don Ummah ta sille ta gaban shi, ba wani abu bane.

A daki ta same ta tayi jugum tana kallon kayan da ta fiddo zata sa. "Nabila miye haka? Ya fa iso fa" da sauri ta mike tsaye. Simple Abaya ce daman ta fiddo zata saka. Kallon Haliman tayi tace "To yanzu fita zan yi kuma gaban Ummah?"

Zuciya Da Gwanin TaDonde viven las historias. Descúbrelo ahora