Daga nan ta ajiye wayan, Sai da suka shiga garin Abuja sannan ta tuno Anty Salma fa ba ta San ta shigo gari ba.
Tana kunna data taga yayi, da sauri tayi logging into snap chat. Selfie ta ma kanta bayan ta kashe flash, Sai ta sticker in location, yayi indicating Abuja. Da sauri tayi saving, ta shiga WhatsApp ta tura ma Anty Salman. Da sauri ta kashe data in ta, tayi gefe da wayan.
After some minutes taji wayan ta na buzzing. Ta riga da tasan Anty Salma ce, don haka ba ta dauka ba. Bayan ya katse, ta kara kunna data. Dan daga wayan tayi, dake Mamma hankalin ta na kan tab in hannun ta, tana ta wani aikin ta can. A sace Nabila, tayi snapping insu a tare. Da ke har sound in camera in ta cire. Tura ma Anty Salman tayi, a kasa tayi captioning "Can't pick, with her"
Emojis in dariya kala kala Anty Salman ta Mata sending back. Akwai shakuwa sosai a tsakanin su, dake lokacin da ta ke zuwa hutun dolen, they are always together duk da tazaran shekarun da ke tsakanin su. Tare su ke amsan hukuncin Momma, so sun saba yan gulmace gulmacen su ta waya ko da kuwa a gaban tane. Sau daya ta taba Kama su, one thing about Mamma, ba wai dukan ka za tayi ba ko tasa ka wani punishment. Aa silently kake amsan hukuncin ka. Ko da ta duba wayan ta ga maganan ta su ke a lokacin, ba tace musu komai ba ta basu wayoyin su back. Sai dai the next thing, su kaga connection in gidan ya dauke baki daya. Ba ma WiFi kadai ta kashe ba, hatta service in gidan tafiya yayi.
Tv baki daya ba subscription, abun da ba a taba yi a gidan ba. Drivers in gidan duk a lokaci daya suka tafi hutu, meaning they are officially grounded kenan. The next one kuwa, tashi suka yi baki daya cleaners da cooks in gidan suma basa nan. Dole suke tashi su gyara gidan nan, duk kuwa da mahaukacin girman shi. Sannan su Fara fafutukan daura abinci, kuma ba iri daya ba, don bai daga ciki tsarin gidan. So Sai ya zamto, system da wayan da suke tunanin za suyi kallon basu da lokacin shi. Daga karshe da kansu suka saduda, su kaje har dakin ta suka durkusa suna bata Hakuri, ko kallon banza basu samu ba. Dole Sai da suka danganta da Alhaji, baban su Salman tukunna. Ce musu tayi, tunda ta zame musu abun dariya, Sai suyi ta gani. Duk dai da hakan bai sa sun saduda ba, Sai dai taka tsantsan da suke yi sosai.
Ukhti 😍: "How did you follow her?" Haka tayi ma Anty Salman saving, wato Yar uwarta.
"The usual by force"
Ukhti 😍"I will find a way to sneak you here, at least kafin na koma"
"Please do" ta tura Mata hade da emojis in kuka kala kala da na ban tausayi. Da gaske Anty Salman ta tausaya Mata, don tasan wahalan zaman gidan su. Ba duka ba zagi, ba aikin Wahala, a kawo maka kaci. Kasa kaya ka cire a wanke maka. Ga free WiFi ba ka da matsalan data Sam. Amma duk da haka zaman kadaicin da wahala. Ga ita Mamma ba sakan ma fuska za tayi ba, balle kaji dadin gidan. Komai kake zai fita ranka, in kallon ne har Sai ka ture. Sai dai Kam ba yawan fita, ko kawayen ka da wuya ake barin ka zuwa gunsu. Ita har bata ga amfani dribobin gidan su ba. Sau da dama ta Sha sneaking ta fita, ba ma tasan inda zata je in ba. Amma kawai tana needing fresh air.
Saboda haka lokacin auren ta, ko kwalla ba tayi ba wai don zata bar gida. In akwai inda ba ta fatan ta ganta a wurin, to gidan su ne. Saurayin ma daya tukun, a University ta hadu dashi can California, Amma ta kawo shi gidan su in tazo hutu tsoro take ji. Sai da ya matsa mata da zancen yana so ya turo sannan fa, daga karshe ma dole ta samu mahaifin ta don kasa tunkarar Mamma da zancen tayi. Shine ya Kira shi yazo gidan, ya same shi, suka gaisa da Mamma. Da farko cewa ma tayi ita Kam bai Mata ba, Sai da aka kai ruwa rana don dai ita ma salman cewa tayi shi kadai take so. Daga baya Kuma da kanta ta sauko ta bari akayi auren. Har aka gama bikin ta, one thing she is proud of, shine yanda Mamma ba ta ji kunyan ta ba, ta zauna ta fahimtar da ita zaman aure. Ba abinda ya rage ba ta fada ko tama yar tata ba. Wannan fannin Kam, har gobe tana tinkaho dashi sosai.
Ana parking a gidan Nabila ta san, ta riga da ta shigo Kuma ai. Haka taja trolley inta, ta wuce dakin da take sauka. Ranta duk a jagule, tana tunanin irin zaman kadaicin da ke jiran ta. Ta gama wanka tana Shirin fita cin abinci kenan call in Sadeeq ya shigo wayan ta.

YOU ARE READING
Zuciya Da Gwanin Ta
RomanceBurin zuciya a ko yaushe shine ta samu gwanin ta. Ko da kuwa hakan zai zama illa a gare ta. To amma in hakan ne kadai ya rage zabi, ya abin kan kasancewa? Ku biyo ni... Ku fito kuji labari zazzafa Kan zuciya da gwanin ta Tsokar da babu irin ta mai s...